BBC Hausa of Wednesday, 18 January 2023

Source: BBC

Man City ta ci gaba da rike matakin farko a samun kudin shiga a tamaula

Hoton alama Hoton alama

Manchester City ta ci gaba da zama a matakin ta daya a duniya a samun kudin shiga a harkar tamaula a 2021-22 in ji Deloittee.

Kamfanin mai kididdigar hada-hadar kudi ya ce rabin wadanda ke cikin 'yan 20 din farko masu buga Premier League.

A rahoton ya ce Manchester City ta samu kudin shiga da ya kai fam miliyan 619.1 a 2021-22 har da kudin tallace-tallace da ya kai fam miliyan 330.

Liverpool tana mataki na uku karon farko da ta taka wannan gurbin tun bayan shekara 26 da aka fara binciken, wadda ta samu fam miliyan 594.3.

A baya Liverpool tana mataki na bakwai, sai dai kokarin da ta yi na kai wa wasan karshe a Champions League a bara, ya sa ta hau kan Manchester United a karon farko.

Leeds ta shiga cikin 'yan 20 din farko a karon farko tun bayan 2002-03, wadda take ta 18, ita kuwa Newcastle tana mataki na 20.

Rahoton ya yi kididdiga kan kudin shiga da kungiya ke samu a fannin tallace-tallace da ladan wasa da sauran batutuwan samun kudin shiga.

Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu, sai dai abokiyar hamayyarta Barcelona ta yi kasa daga mataki na hudu zuwa na bakwai, bayan rashin kaso 13 cikin 100 daga kudin haska wasanninta.