BBC Hausa of Monday, 1 January 2024

Source: BBC

Man City ta sayi Echeverri, Kungiyoyi na rububin Adesina

File foto File foto

Manchester City ta sayi matashin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar River Plate kuma na tawagar ’yan ƙasa da shekara 17 ta Argentina, Claudio Echeverri tsawon shekara shidan amma matashin mai shekara 17 zai ci gaba da zama a ƙungiyar tasa har zuwa Disamban 2024. (Fabrizio Romano)

Manchester United ta fasa tsawaita zaman Raphael Varane a ƙungiyar da wata 12, hakan na nufin a yanzu ɗan wasan na Faransa zai iya neman ƙungiyar da zai tafi a wata ƙasa daga 1 ga watan nan na Janairu, a matsayin maras wani kwantiragi a kansa. (Mail)

Leicester na son aron ɗan wasan gaba na gefe na Liverpool Fabio Carvalho, bayan dawo da ɗan Portugal ɗin mai shekara 21 daga zaman aron da yake yi a RB Leipzig. (Sky Sports)

A makonnin nan Liverpool ta tura jami'anta masu nemo mata ƴan wasa da su sa ido a kan Micheal Olise na Crystal Palace, mai shekara 22, haihuwar Ingila kuma tsohon ɗan tawagar ƴan ƙasa da shekara 21 ta Faransa. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya na Tottenham da Senegal Pape Matar Sarr, mai shekara 21, wanda ya fice daga fili saboda raunin jinya da ya ji a wasansu na Lahadi da Bournemouth na dab da kulla sabon kwantiragi mai tsawo a kungiyar ta Arewacin London. (Athletic)

Monaco ta kusa kammala cinikin ɗan bayan Jamus Thilo Kehrer daga West Ham. (Fabrizio Romano)

Juventus, da Nice da kuma wasu ƙungiyoyin Premier da dama na son ɗan wasan gaba na gefe na Atalanta, Ademola Adesina, na Ingila. (Mail)

West Ham na sha'awar sayen ɗan wasan gaba na Najeriya kuma ɗan Montpellier Akor Adams a watan Janairu, amma kuma ƙungiyar ta Faransa ba ta son barin shi ya tafi a tsakiyar kaka. (Football Insider)

Sheffield United na son aron mai tsaron raga a watan Janairu, inda take son Kasper Schmeichel na Anderlecht da kuma tawagar Denmark. (Sun)

Brentford ta yi tayin yuro miliyan 25 a kan matashin ɗan wasan Real Betis, Assane Diao mai shekara 18 na Sifaniya

Southampton na nazarin sayen ɗan wasan tsakiya na Burnley kuma ɗan Belgium Manuel Benson. (Daily Echo)

West Ham za ta kara wa ɗan bayanta Vladirmir Coufal shekara ɗaya, to amma kuma ɗan bayan na Czech yana son abin da ya fi haka ne. (Sun)

Eintracht Frankfurt ta kusa cimma yarjejeniyar aro da Wolves a kan Sasa Kalajdzic, ɗan Austria mai shekara 26. (Bild)