Manchester United ta kai gurbin 'yan 16 da za su ci gaba da Europa League, bayan da ta yi nasara a kan Barcelona ranar Alhamis a Old Trafford.
United ta yi nasarar cin kungiyar Nou Camp 2-1 a wasa na biyu a gurbin kai wa matakin 'yan 16 a gasar zakarun Turai.
Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Robert Lewandowski a minti na 18 a bugun fenariti.
Kwallo na 25 da ya ci wa Barcelona kenan a wasa 30 a dukkan karawa a bana, karo na 12 a jere da yake zura kwallo 25 ko fiye da haka a kakar tamaula.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Fred ya farke, sannan Anthony ya kara na biyu.
Anthony ya canji Weghorst - United ta zura kwallo 19 daga dan wasan da ya yi canji a kakar nan a dukkan fafatawa, ba wadda ta kaita amfana da hakan a manyan gasar Turai biyar.
Manchester United wadda ta buga 2-2 a makon jiya a Nou Camp ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-3 gida da waje kenan.
Wasa na 15 da aka kara tsakanin kungiyoyin biyu kenan, inda United ta yi nasara a hudu da canjaras biyar Barcelona ta ci shida.
United wadda take takarar lashe kofi hudu a bana, za ta buga wasan karshe a Wembley da Newcastle United a Caraboa Cup ranar Lahadi.
Ranar Lahadi, Barcelona wadda take ta daya a teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid, za ta ziyarci Almeria a wasan mako na 23.