BBC Hausa of Friday, 7 July 2023

Source: BBC

Man Utd ta kusa samun Onana, Chelsea ta nace wa Caicedo

Andre Onana Andre Onana

Manchester United na dab da kammala cinikin mai tsaron ragar Inter Milan Andre Onana, na Kamaru bayan bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya a tsakaninsu. (Fabrizio Romano)

Haka kuma United din tana shirin sayen dan wasan gaba na Atalanta Rasmus Hojlund, mai shekara 20, dan Denmark a kan fam miliyan 50. (Telegraph)

Chelsea kuwa sai ta fitar da sama da fam miliyan 100 idan har tana son sayen dan wasan tsakiya na Brighton da Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, a bazaran nan. (Telegraph)

Newcastle na shirin bayar da mamaki inda take son sayen tsohon dan bayan Italiya, Leonardo Bonucci, na Juventus, mai shekara 36, domin kara karfin bayanta da 'yan wasa kwararru a shirin da take yi na tunkarar gasar Zakarun Turai. (TEAMtalk)

A yau Juma'a ne za a gwada lafiyar dan bayan Ajax Jurrien Timber a Arsenal inda kungiyar ke da kwarin gwiwar kammala cinikin dan Holland din a kan fam miliyan 38 da rabi (Standard)

Dan wasan tsakiya na Tottenham Ivan Perisic ya gaya wa kociyan kungiyar Ange Postecoglou cewa yana son soke kwantiraginsa, domin ya koma Hajduk Split ta kasarsa Crotia. (Gianluca Di Marzio)

Ita kuwa Atletico Madrid ta tuntubi Spurs ne a kan dan wasanta na tsakiya Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 27, dan Denmark, wanda kuma ake dangantawa da Bayern Munich. (Mail)

Southampton ta yi amanna za ta samu fam miliyan 50 farashin da ta yi wa matashin dan wasanta na tsakiya Romeo Lavia, na Belgium mai shekara 19, wanda Chelsea, da Liverpool da Arsenal duka ke nemansa. (Sky Sports)

Fatan Crystal Palace na sake kulla yarjejeniya da tauraron dan wasanta Wilfried Zaha ya dusashe kasancewar dan wasan mai shekara 30 na duba tayin da ya samu daga Lazio, da Fenerbahce da kuma Al-Nassr ta Saudiyya. (Standard)

Fulham na dab da cimma yarjejeniya da Willian bayan da kwantiragin dan Brazil din ya kare a karshen makon da ya gabata, ya zamanto ba shi da wata kungiya. (The Athletic )

Dan gaban Chelsea da Amurka Christian Pulisic, mai shekara 24, wanda ke son tafiya daga Stanford Bridge na dab da komawa AC Milan a kan fam miliyan 20. (90 min)

Dan bayan Arsenal William Saliba, na Faransa mai shekara 22, ya kulla sabuwar yarjejeniya da zai ci gaba da zama a Emirates har zuwa 2027. (The Athletic )

West Ham na duba yuwuwar zawarcin dan wasan tsakiya na Juventus Denis Zakaria. Da farko kungiyar za ta karbi aronsa ne amma da zabin sayensa gaba daya a kan fam miliyan 15.4 (Guardian)

The Hammers are also interested in Fulham's Portuguese enforcer Joao Palhinha, 27, and Southampton and England's 28-year-old set piece specialist James Ward-Prowse. (Guardian)

Wolves are desperate to keep 26-year-old English centre-back Max Kilman after turning down a £30m bid from Serie A giants Napoli. (Telegraph)