BBC Hausa of Friday, 11 August 2023

Source: BBC

Manyan hafsoshin sojin Ecowas za su gana don tsara shirin tunkarar Nijar

Hoton alama Hoton alama

Manyan hafsoshin sojin Afirka ta Yamma za su gudanar da taron ranar Asabar a Ghana don tsara shirye-shirye a kan yiwuwar amfani da ƙarfin soja a kan Nijar.

Matakin na zuwa ne bayan ƙungiyar ƙasashen wato Ecowas ta ba da umarnin a tanadi dakarun ta-kwana da nufin dawo da Nijar kan turbar dimokraɗiyya.

Manyan hafsoshin sojin na ƙasashen Ecowas za su gudanar da taron ne cikin birnin Accra, ko da yake babu cikakkun bayanai game da ajandar taron.

Ƙasashen Afirka ta Yamma dai tuni suka ci gaba da duba yiwuwar ɗaukar matakan soji a kan Nijar bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum ya kasance juyin mulki bakwai da aka samu a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekara uku, abin da kuma ya ƙara jefa yankin cikin tunzuri, baya ga hare-haren masu iƙirarin jihadi da yake fama da su tsawon lokaci.

Kungiyar Tarayyar Afrika a ranar Juma'a ta nuna damuwa kan rahotannin halin da Shugaba Bazoum wanda ke tsare, yake ciki, inda ta ce ba za ta lamunci ci gaba da tsarewar da sojojin da suka yi juyin mulki ke yi masa ba.

"Ci gaba da tsare zaɓaɓɓen shugaban ƙasa wanda aka zaɓa ta hanyar doka, abu ne da ba za mu amince da shi ba," cewar wata sanarwa da shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat ya fitar.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis, Shugaba Alassane Ouattara ya ce "Tsare Bazoum tamkar ta'addanci ne, kuma na yi alƙawarin bayar da gudunmawar dakaru".

Kungiyar Kare Hakkin Ɗan'adam ta Human Rights Watch, ta ce ta zanta da Shugaba Bazoum a wannan mako, kuma yana ci gaba da kasancewa a tsare tare da matarsa da kuma ɗansa, ya ce kuma lafiyar iyalinsa tana cikin garari.

"Ɗana ba shi da lafiya, yana fama da ciwon zuciya, kuma yana buƙatar ganin likita," Kamar yadda ƙungiyar ta ruwaito Bazoum yana cewa. "Sun ƙi barinsa ya samu ganin likita ko magani."

Ya kuma faɗa wa ƙungiyar cewa rabon sa da wutar lantarki tun ranar 2 ga watan Agusta, kuma an ƙi bari ya ga iyalansa da abokansa waɗansa ke son kawo masa taimako.

Duk da yake Nijar, na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya, da ba ta kusa da teku, kuma girmanta ya kai misalin faɗin Faransa biyu, ita ce ƙasa ta bakwai a duniya da ke samar da makamashin uranium, wani muhimmin sinadari da ake amfani da shi wajen sarrafa makamashin nukiliya da kuma haɗa magungunan cutar daji ko kansa.

Kafin juyin mulkin, Nijar ta kasance abokiyar ƙawance ga Ƙasashen Yamma, amma yanzu ta juya wa uwargijiyarta Faransa baya inda take yunƙurin ƙulla alaƙa da Rasha.

Akwai dakarun Amurka da Faransa da Jamus da kuma na Italiya a Nijar, a matsayin wani ɓangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi da ya bazu a faɗin yanki Sahel.

Amurka da Faransa suna goyon bayan Ecowas

Faransa da Amurka dai sun bayyana goyon bayansu ga dukkan shawarwari da taron Ecowas na ranar Alhamis ya cimma, wanda ya amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar harkokin wajen Faransa, ta ƙara nanata adawa da juyin mulki a Nijar da kuma tsare Shugaba Bazoum.

Ita ma Amurka ta bakin Sakataren Wajenta, Anthony Blinken, ta ce "Gwamnatin Washington na goyon bayan duk wani mataki da Ecowas za ta ɗauka don ganin an dawo da tsarin dimokraɗiyya Nijar".

Ta kuma ce za ta ɗora alhakin duk abin da ya faru ga lafiyar Bazoum da kuma iyalansa a kan sojojin.

'Mun damu da yanayin lafiyar Bazoum"

Tarayyar Turai ta ce halin da ake tsare da Bazoum Mohamed na ci gaba da taɓarɓarewa, kuma ta yi kira saki hamɓararren shugaban cikin gaggawa.

Wata sanarwa da EU ta fitar ta hannun jami'inta kan manufofin hulɗa da ƙasashen waje, Josep Borrell, ta ce ita da Majalisar Ɗinkin Duniya sun damu matuƙa a kan halin da Bazoum ke ciki bayan tattaunawa da shi ta wayar tarho ranar Laraba.

"Mun damu game da halin lafiyar Bazoum da kuma ta iyalansa. Ba mu da tabbaci a kan irin tsaron da aka ba su," in ji EU.

Hamɓararren shugaban ƙasar dai na tsare a gidansa da ke fadar shugaban ƙasa cikin Yamai, babban birnin Nijar tun bayan kifar da shi daga kan mulki.