Al'umma da ƴan siyasa da ƙungiyoyin addinin musulunci a Najeriya suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan harin da sojoji suka kai "bisa kuskure" a Tudun Biri, wani ƙauye a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a arewacin ƙasar.
Harin dai ya yi sanadin asarar rayuka da dama tare da jikkatar wasu da ke samun kulawa a asibiti.
Hukumomi sun bayyana cewa mutane 85 ne harin ya kashe, sai dai ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma al'ummar ƙauyen na cewa adadin ya zarce haka.
Ga wasu daga cikin manyan mutanen da suka yi tsokaci game da lamarin:
A binciki lamarin - Tinubu
Tuni shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya kuma jajanta wa al'ummar ƙauyen na Tudun Biri, inda ya yi alƙawarin ganin an yi cikakken bincike.
Muna fatan hukumomi su yi bincike – Khalifa Muhammadu Sanusi II
Yayin da yake miƙa saƙon ta'aziyya da kuma jaje, Khalifan ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II ya ce a shekarun baya an samu afkuwar irin haka a jihar Nassarawa amma har yanzu ba a ga rahoton binciken da hukumomi suka yi ba.Muhammadu Sanusi ya ce ya kamata hukumomi su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ba a samu afkuwar irin haka a gaba ba.
Ya kuma yi kira ga mutane su kwantar da hankalinsu sannan su bai wa hukumomi haɗin kai a binciken da suke yi.
Masifu za su yi ta ƙaruwa a arewa saboda rashin jagoranci – Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma ɗaya daga cikin dattawan arewacin Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce matukar dattawan arewa ba su hada kai domin magance matsalar tsaro a yankin baki daya ba, to da wuya a daina ganin masifu na auka wa al'umma.Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya bayyana wa BBC hakan yayin da yake magana game da iftila'in bam da ya fada kan al'ummar Tudun Biri a jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin asarar rayuka.
Ya ce matukar dattawan arewa ba su hada kai don magance matsalar tsaro a yankin baki daya ba, to za a riƙa fuskantar irin waɗannan matsaloli.
Ya kamata a bijiro da dabarun kauce wa sake afkuwar harin – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya bayyana takaici bayan harin da ya faru a jihar ta Kaduna.A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya buƙaci mahukunta su ƙaddamar da bincike domin kare afkuwar makamancin ibtila'in a gaba.
Ya ce batun kai hari bisa kuskure wani lamari ne da da ke ɗaukar wani yanayi na damuwa a ƙasar.
A biya mutanen da harin ya shafa diyya – Sheikh Ɗahiru Bauchi
A hirarsa da BBC, Sheikh Ɗahiru Uthman Bauchi, wanda shi ne shugaban ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, ya ce akwai mamaki a ce an kai irin wannan hari bisa kuskure.Ya ce akwai buƙatar mahukunta su fito su yi bayani kan yadda lamarin ya faru tare da biyan diyya ga rayukan da aka rasa.
"Muna neman su sanar da mu yadda aka yi aka ƙona mana masu yin mauludi da jiragen sama," in ji Sheikh Ɗahiru Bauchi.
Wanda ya yi kisan kai da kuskure ne yake biyan diyya – Sheikh Bala Lau
Shugaban ƙungiyar Izala a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce abin da ya faru ga masu bikin mauludi abin baƙin ciki ne.A cewarsa, "muna kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya, ɗaukan matakai da ake yi don kawo ƙarshen ta'addanci abu ne mai muhimmanci, amma kare rayuka na da muhimmanci, kar garin neman gyara a fada cikin wata ɓarna."
Shi ma ya nemi a biya diyya saboda "wanda ya yi kisan kai da kuskure ne yake biyan diyya, wanda ya yi kisa da gangan, shi ba maganar diyya - a kan kama shi a yi masa hukunci."
Sai dai ya ce batu ne da ya shafi gwamnati - duk abin da ya faru, bayan binciken ta, ya kamata gwamnati ta biya diyya ga waɗanda aka rasa su," in ji Sheikh Bala Lau.
Ya kamata a tabbatar da adalci - Kwankwaso
A nashi saƙon ta'aziyyar a shafinsa na X, ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce irin wannan hari na kuskure abu ne mai ban tsoro da ke janyo illa ga mutanen da ba su ji ba su gani ba da ya kamata a ce hukumomin tsaro sun tabbatar wa tsaro.Ya ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su bi diddigi domin tabbatar da adalci a kuma kare afkuwar irin haka a gaba.