BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Massimiliano Allegri ya sake karbar aikin kocin Juventus

Massimiliano Allegri Massimiliano Allegri

Wasu rahotanni daga kafar yada labarai a Italiya sun ce Juventus ta koci Andrea Pirlo ta kuma maye gurbinsa da Massimiliano Allegri.

Sky Italia ta ce Allegri zai sake karbar aikin horar da Juventus a karo na biyu, bayan shekara biyu rabonsa da kungiyar ya kuma amince da kwantiragi.

Hakan ya kawo karshen aikin Pirlo wanda ta dauka a farkon kakar bana, duk da cewar bai da kwarewar aikin horar da tamaula.

Juventus wadda ta lashe Serie A tara a jere ta kasa cin kofin bana, wanda Inter ta dauka, kuma da kyar ta yi ta hudu a teburin babbar gasar Italiya a kakar nana.

Juventus ta yi rigen daukar kocin, saboda tsoron kada wasu kungiyoyin su riga ta, Sky Italia ta yi rahoton cewar Inter Milan wadda ta raba gari da Antonio Conte za ta iya daukar kocin.

Haka kuma Real Madrid ma za ta iya zawarcin Allegri, bayan da Zinedine Zidane ya yi murabus.

Rahotannin sun ce ana sa ran cimma yarjejeniyar shekara uku ko kuma hudu tsakanin Juventus da kuma Allegri.

Reuters ta tuntubi Juventus don tabbatar da labarin.

Allegri ya lashe Serie A biyar a jere tsakanin 2014 zuwa 2019, ya kuma dauki Coppa Italiya hudu ya kuma kai wasan karshe a Champions League karo biyu.