"Ban ce tsoro ko kadan ba, saboda na san abin da na yi kan hanya ya ke,'' inji matashiyar 'yar Afghanistan mai shekara 18 da babu alamar tsoro ko kadan tattare da ita, mai cike da burin ganin ta yi karatun jami'a, sai dai kash matakin gwamnatin Taliban ya sanya ta cikin matsananciyar damuwa saboda sun haramtawa mata zuwa jami'a.
Takaici da bakin cikin ganin mafarkinta na neman bin iska, da tasgaro da yi wa makomarta kafar ungulu, (mun sauya sunanta saboda dalilai na tsaro) ta dauki matakin yin zanga-zanga ita kadai a gaban jami'ar Kabul ta hanyar amfani da kalma daya daga Alkurani, wani lamari da ba safai ake gani ba.
Ranar 25 ga watan Disamba, Adela ta tsaya gaban babbar kofar shiga jami'ar dauke da allon da aka rubuta kalma daya ta harshen larabci- Iqra, ko kuma ''Karanta''. Musulmai sun yi imanin ita ce kalmar farko da Allah SWA ya fara saukar wa Annabi Muhammad SAW.
"Allah ya ba mu damar neman ilimi. Ya kamata mu ji tsoron Allah, ba 'yan Taliban ba da ke son kwace ma na 'yancinmu ba,'' a hirar ta da BBC.
Zanga-zanga kai daya
"Nasan su na yi wa masu zanga-zanga ba dadi. Su na lakada musu duka, su haure su, su na amfani da makamai, su na amfani da feshin ruwa, sukan azabtar da su da wutar lantarki.
Amma duk da haka na tsaya a gabansu,'' in ji Adela a lokacin hira da sashen BBC Afghanistan.
"Da farko ba su dauki abin nawa da muhimmanci ba. Daya baya wani dauke da bindiga ya ce na bar wurin."
A zahiri, Adela ta ki barin wurin, ta yi tsayin daka, amma a hankali kwalin da ta ke dauke da shi da kalmar da ke jiki ta fara daukar hankalin mutanen da ke kusa da ita.
A daidai lokacin ta yi amfani da damar ta fara jan hankalin mutane ciki har da 'yan Taliban.
''Za ka iya karanta abin da aka rubuta?'' ta tambayi daya daga ciki.
Amma ya ka sa cewa komai, dan haka sai Adela ta ci gaba da magana; ''Yanzu ba za ka iya karanta kalmar Allah ba?''
"Ran shi ya yi mugun baci, daga nan ya fara yi min barazana."
An kwace allon, an kuma tilasta ma ta barin wurin bayan mintina 15 da fara boren na ta.
A lokacin da ta ke zanga-zangar, yayarta na zaune cikin wata tasi ta na daukar hotuna da bidiyon abin da kanwarta ke yi.
"Direban tasi din ya fara jin tsoron 'yan Taliban. Ya na ta rokon yayata ta daina daukar hotuna da bidiyon. Saboda a tsorace ya ke matuka, ya kuma ce ta fice daga motarsa."
Karuwar matsawa mata da yi musu iyaka
Janyewar dakarun kasashen waje da Amirka ke jagoranta, ba zato ba tsammani daga Afghanistan, ya bai wa Taliban damar karbe iko da kasar a watan Agusta 2021."
Ran shi ya yi mugun baci, daga nan ya fara yi min barazana."
An kwace allon, an kuma tilasta ma ta barin wurin bayan mintina 15 da fara boren na ta.
A lokacin da ta ke zanga-zangar, yayarta na zaune cikin wata tasi ta na daukar hotuna da bidiyon abin da kanwarta ke yi.
"Direban tasi din ya fara jin tsoron 'yan Taliban. Ya na ta rokon yayata ta daina daukar hotuna da bidiyon. Saboda a tsorace ya ke matuka, ya kuma ce ta fice daga motarsa."
Da farko sun haramtawa 'yan mata komawa makarantar Sakandare bayan kammala dogon zama.
A watan satumba, sun hana dalibai mata daukar wasu daga cikin darussa, sun kuma fada musu za su iya zabar jami'ar da ke kusa da gundumar da suke zaune.
Ranar 20 ga watan Disamba, su ka haramtawa mana zuwa jami'a, lamarin da ya tunzura duniya da janyo allawadai, bayan kwanaki kadan suka kara daukar matakin hara mata zuwa wuraren aiki da kuma aiki da kungiyoyin agaji masu zaman kan su.
Mata musamman daliban jami'a sun yi ta zanga-zanga kan lamarin musamman wadanda suke da burin zurfafa ilimi.
Wasu daga ciki su na amfani da kalmomin ''mata, rayuwa, 'yanci.'' a lokacin zanga-zangar baya-bayan nan da ake yi a Iran.
Jami'ai a jami'ar Kabul, da hudu daga cikin tsangayoyin mata ne ke jagoranta, sun shaidawa BBC cewa an hana Farfesoshi mata shiga harabar jami'ar.
Kira ga mata>
"Lokacin da na yi zanga-zangar, wani matashi ya so daukar hoto da bidiyo da ni domin ya karfafa min gwiwa. Amma 'yan Taliban suka lakada masa duka,'' in ji Adela.
Wani farfesa ya yaga takardun shaidar difiloma da ya yi, an kuma yada kai tsaye a Talbijin domin nuna adawarsa, kuma wani makusancinsa ya shaidawa BBC sama da malaman jami'a 50 ne suka ajiye aiki a wani bangare na tasu zanga-zangar.
Wani malami da ya ajiye aikin koyarwar, ya shaidawa BBC ya janye hakan, bayan mambobin Taliban sun lakada masa dan karen duka.
Amma Adela ta amince, lamari ne mai matukar wuya mazan Afghanistan su shiga wannan gwagwarmayar.
"Tsirarun mazan Afghanistan ne suka tsaya mana. A Iran maza sun fito domin gwagwarmaya akan hakkin 'yar uwarsu, da nemawa mata hakki da 'yancinsu. Idan muka kada kai, mukai tsayin daka domin kwato hakki da 'yancin mu na samun nagartaccen ilimi, to 100 bisa 100 nasarar ta mu ce baki daya."
Ba gudu ba bu ja da baya
Sai dai shugabannin Taliban ko a jikinsu.Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ambato ministan Ilimi Nida Muhammad Nadim na cewa babu mai sauya matakin, ba gudu ba ja da baya, ''ko da za su yi mana luguden makaman roka ne.''
Ita ma Adela ba ta karaya ba
"Idan ba zan iya tashi sama ba, ai zan iya fyalla gudu. Idan ba zan iya gudu ba, babu abin da zai hanani tafiya cikin tsanaki.
Idan ba zan iya duka ba, tabbas zan ja ciki. Abu guda daya na sa ni, ba zan taba karaya ba, ba zan daina gwagwarmaya ba, sai inda karfi na ya kare.''
Kawayenta sun ba ta karin gwiwa, inda su ke cewa- "ke gwarzuwa ce, kin amince matan Afghanistan za su iya komai a rayua, za kuma su iya kwatarwa kan su 'yanci, da samun ingantacciyar rayuwa.
"Ba ma fatan komawa rayuwar kuncin da mukai a baya, shekaru 20 da suka gaba ta. Mun fi lokacin baya karin gwiwa, mu ba ragwaye ne ba, mu na da ilimi kuma mun san 'yancinmu.''