BBC Hausa of Friday, 8 December 2023

Source: BBC

Matatar man Dangote ta karɓi ɗanyen mai a karon farko

Kamfanin mai na Dangote a Legas Kamfanin mai na Dangote a Legas

A ranar Juma'a ne matatar Dangote ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran abubuwan amfani.

Sabuwar matatar ta Dangote za ta zama mafi girma a Afirka idan ta fara aiki.

A cikin wata sanarwar da ta fito daga matatar, an ambato shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote na cewa "wannan mataki ne mai muhimmanci."

Sanarwar ta ce matatar man fetur ta Dangote ta sayi gangar ɗanyen mai miliyan ɗaya daga wasu manyan kamfanonin haƙo ɗanyen mai.

Ta ci gaba da cewa wani jirgin dakon kaya ɗauke da ɗanyen man ya isa wurin sauke mai na Dangote, inda ya juye shi a cikin manyan rumbunan zuba ɗanyen mai na matatar.

Kuma wannan, a cewar sanarwar shi ne kashin farko a cikin ɗanyen mai ganga miliyan shida da matatar ta saye daga manyan kamfanonin haƙo ɗanyen mai.

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC ne ake sa ran sai samar da ɗanyen fetur na gaba ga matatar, a cikin mako biyu zuwa uku masu zuwa, yayin da kamfanin ExxonMobil shi ma sai samar da wani ɓangare na ɗanyen man.

A watan Nuwamba ne kamfanin mai na NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniya ta samar da ɗanyen man fetur ga matatar.

Wannan dai wani lokaci ne da aka daɗe ana jira a ƙasar ta Najeriya, ganin cewa ana sa ran matatar za ta sauya harkokin man fetur a ƙasar.

Duk da cewa Najeriya ce kan gaba wajen fitar da ɗanyen mai a Afirka, amma ba ta iya tace shi domin samar da man fetur domin amfani a ƙasar, wadda ita ce kan gaba wajen yawan jama'a da ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka.

Bayani kan matatar mai ta Dangote

Idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya har ma a samu rara da za a fitar zuwa wasu ƙasashe a kullum.

An tsara ta yadda za ta iya sarrafa nau’uka daban-daban na ɗanyen mai daga ƙasashen Afirka da na ƙasashen Gabas ta tsakiya da yankin Amurka.

Matatar tana da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.

A watan Mayun 2023 ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar matatar man mallakin mutum mafi arziƙi a Afirka, Aliko Ɗangote.

An ƙaddamar da matatar ce kimanin shekaru 67 bayan da Najeriya ta fara samar da ɗanyen man fetur a 1957.

Tun bayan da aikin samar da tatar man ya kankama al’ummar Najeriya sun zaku su ga fara aikinta, kasancewar suna kyautata zaton cewa za ta kawo sauki ga samuwar man fetur a fadin kasar.

Mene ne zai sauya?

Dakta Ahmed Adamu, masani ne kan man fetur a Najeriya, ya ce matatar man fetur ta Ɗangote za ta amfani Najeriya ne idan aka ɗauki wasu muhimman matakai biyu:

Samar da isasshen danyen mai: Dakta Ahmed Adamu ya ce matuƙar ana son matatar ta yi aiki yadda ya kamata ta yadda za ta samar da sauƙi, to dole ne sai an samar mata da isasshen ɗanyen mai.

A cewar sa yanzu haka Najeriya ba ta samar da isasshen ɗanyen mai da zai wadaci matatar sanadiyyar matsaloli na fasa bututai da kuma satar ɗanyen mai.

Ya ƙara da cewa matuƙar babu isasshen ɗanyen man fetur ɗin hakan zai tilasta wa matatar nemo ɗanyen mai a wasu ƙasashen, wanda hakan zai ƙara tsadar ɗanyen man da take buƙata.

Cire tallafin man fetur: Dakta Adamu ya ce ya kamata a cire tallafin man fetur ta yadda za a sakar wa matatar mara wajen sayar da man fetur a Najeriya kamar yadda ake sayarwa a sauran ƙasashe ba tare da tarnaƙi ba.

Ya ce kasancewar matatar kamfani ne mai zaman kansa ya kamata a bar shi ya yanke hukunci a kan farashin da yake son sayar da tataccen man fetur ɗin.

A cikin bayanin nasa, dakta Ahmed ya ce samar da matatar man fetur a Najeriya zai rage wa ƙasar wahalar da take sha wajen samun kuɗaɗen shiga na ƙasashen ƙetare kamar dalar Amurka.