BBC Hausa of Friday, 13 January 2023

Source: BBC

Matsalar kuɗi da Najeriya ke fuskanta da kuma sauyin fasalin kuɗi

Hoton alama Hoton alama

A cikin jerin wasikunmu daga ‘yan jaridar Afirka, Mannir Dan Ali, tsohon babban editan jaridar Daily Trust ta Najeriya, ya yi nazari kan matsalar kuɗi da Najeriya ke fuskanta wadda ta kasance ƙasar da ta fi yawan al’umma a Afirka ke fama makonni kalilan kafin gudanar da zaɓe.

Takardar kuɗi dai tana da muhimmancin gaske a Najeriya - ba kowa ne ke amfani da na'urar cirar kuɗi ba wato ATM. Mutane kalilan ne suke ajiye kuɗaɗensu a banki - inda ake yawan faɗa cewa mutane da dama na ajiye kuɗinsu a karkashin gadajensu.

A cewar babban bankin Najeriya, ƙasa da kashi 20 na kuɗaɗen da ake amfani da su a ƙasar ne kaɗai ke hannun bankuna.

Gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa daga cikin naira tiriliyan 3.2 da ke yawo, kusan tiriliyan 2.7 na a wajen bankunan kasuwanci.

Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa a watan Oktoba ya bayar da sanarwar cewa zai sauya fasalin manyan takardun kuɗin ƙasar.

Babban abin da aka sauya wa shi ne launi na takardun kuɗin. Naira 1,000 ya canza daga launin ruwan kasa zuwa shudi; 500 daga tsanwa zuwa kore da 200 daga launin ruwan kasa da shuɗi zuwa ruwan hoda.

Sabbin kuɗin sun zama tamkar zinare

Matsalar da ke tattare da ƙasar da ba kasafai abubuwa ke tafiya yadda aka tsara ba, zai yi wuya a ce sauyin kuɗi da gwamnati ta yi zai iya kammala cikin mako shida – inda a karshen watan Janairu, tsoffin takardun kuɗin ba za su sake aiki ba.

A daidai lokacin da ake jira kafin su daina aiki, sabbin takardun kuɗin sun kasance kamar zinare, inda ake shan wuya kafin samun su.

Na samu damar rike sabbin takardun kuɗin guda goma a makon da ya gabata bayan zuwa wani banki a Abuja, babban birnin ƙasar.

Na yi kokarin cire sabbin kuɗi daga wata na’urar cirar kuɗi, sai dai har yanzu tsoffin kuɗi ne na’urar ke fitarwa.

Ma’aikacin bankin da ya bani kuɗin wanda ba su fi dala 20 ba, ya ce iya abin da kowa zai iya samu kenan.

Ya tambaye ni da na saka bayanai na a cikin wata takarda da ke kusa da shi – wata hanya ta tabbatar da cewa kwastomomin banki na asali, na samun sabbin kuɗin, ba wai waɗanda ke karkata su zuwa ga ‘yan canji ba, waɗanda ke cazar wani abu kafin su bayar da sabon kuɗin.

Har masu arziki da kuma ke da karfin iko ma na fuskantar matsaloli wajen samun sabbin kuɗaɗen.

A ranar da aka fara amfani da sabbin kuɗaɗen, kwanaki kaɗan kafin bikin kirsimeti na ji wani babban mamban jam’iyya mai mulki, na ƙorafin cewa duk da ya samu zuwa bankin da yake mu’amala da su, manajan bankin, ya ce kuɗi kalilan kaɗai zai iya ba shi, saboda an takaita ma bankunan iya sabbin kuɗi da za su iya bayar wa.

Waɗannan abubuwa, su ke ƙara nuna matsaloli da ake fuskanta wajen kammala sauyin komawa amfani da sabbin kuɗi.

Idan har a biranen Abuja da Lagos da Fatakwal da kuma Kano mutane ba su kai samun rike sabbin kuɗin ba, ana tunanin zai yi wahala su yawaita a faɗin ƙasar nan da ƙarshen wata.

Sauyin sam bai shafi ayyukan masu garkuwa ba

Idan ana son cimma buri na ganin sun samu yawaita, to akwai bukatar gaggawa na ganin an tallata batun.

Kafafen sada zumunta sun cika da labarai da ke yawo na cewa wasu mata ‘yan kasuwa na kin karɓar sabbin kuɗaɗen, waɗanda suke ganin basu kai ingancin tsoffin ba – bugu da ƙari ga fargabar faɗawa hannun mazambata.

Sannan duk da sauya launin kuɗin, ana ganin da wuya hakan ya kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, wanda ake fuskanta a sassan ƙasar da dama.

Akwai ma bayanai da ake samu cewa masu garkuwan na tambayar a biya su da sabbin kuɗaɗen, duk da cewa ba su san mutane ma basu kai ga rike su ba.  

'Yan Najeriya da dama na cikin barazanar rasa kuɗaɗensu da suka ajiye.

Yawancin garuruwa a ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Najeriya ba su da rassa na bankuna, inda ko da a wannan lokaci na hada-hadar kuɗi ta latironi, ba su kai ga yawaita ba a yankunan ƙarkara.

Ya kamata a ce an samar da su a yankunan ƙarkara, inda ake da daɗaɗɗiyar dabi’a ta ajiye kuɗi a karkashin katifu ko ma gadajen mutane.

Mista Emefiele, ya dora laifin hakan kan matsalar kuɗi da ake fuskanta a ƙasar.

Sai dai a zahirin gaskiya, ba talakan Najeriya ne ya kamata a ɗorawa laifin ajiye kuɗi a a gida ba.

Masu sharhi sun ce hakan zai zama batu kafin zaɓe musamman ma lokacin da ake zargin ‘yan siyasa da amfani da kuɗi wajen sayen kuri’a.

A lokacin zaɓen 2019, kafofin sada zumunta sun cika da hotuna da kuma bidiyon wata babbar mota cike makil da kuɗi tana shiga gidan wani babban dan siyasa kuma mai fada a ji.

Sai dai muƙarrabansa sun musanta batun cewa za a yi amfani da kuɗin wajen sayen kuri’a.

Amma al’adar bai wa masu zaɓe kuɗi domin zaɓar wani ɗan takara na daban, ba sabon abu bane a Najeriya.

Za a iya cewa gwamnati na sane da batun sauya fasalin kuɗi, domin daidaita harkokin siyasa kafin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sai dai ana ƙara nuna damuwa kan lokaci da aka yi wannan sauyi.

Majalisar dattawa ta buƙaci a tsawaita lokacin sauya fasalin kuɗin, amma alamu na nuna cewa CBN na kan baƙarsa.

Don ƙara tsananta abubuwa ma, a halin da ake ciki, gwamnan babban bankin ƙasar ya yi ɓatan dabo, inda ya fita ƙasar waje na tsawon makonni.

Yana kuma fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka haɗa da rashin iya gudanar da aiki, wanda wasu ke ganin na da nasaba da siyasa.

Ana dai ganin da wuya a iya kammala sauyin zuwa amfani da sabbin takardun kuɗin kafin na da 31 ga watan Janairu.

Wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari zai kawo karshe a wata Mayu, inda zai miƙa wa magajinsa bayan mulki na shekaru takwas a matsayin zaɓaɓɓen shugaba.

Ga wasu mutane, suna kuma sake tuna lokacin da aka sauya takadun kuɗi a shekarun 1980, lokacin da Buhari ke mulkin soja. Lokaci ne kuma da ‘yan kasuwa da dama masu zaman kansu suka durkushe da kuma rasa arzikinsu.