Kylian Mbappe ba zai yi atisaye da tawagar 'yan wasan Paris St-Germain ba a lokacin da suka fara shiri a ranar Litinin na fara gasar Ligue 1.
Mbappe na takun-saka da PSG ne bayan ya ƙi yarda ya tsawaita kwantiraginsa a ƙungiyar, yayin da ake ganin ya fi son komawa Real Madrid.
Dan wasan da ya fi zira kwallo a raga a kulob din, ya ki amincewa ya tsawaita kwantiraginsa na shekara ɗaya da zai kare a bazara mai zuwa.
Don haka PSG na son sayar da shi a yanzu domin su samu kudi a kansa a maimakon barinsa ya tafi kyauta a ƙarshen kaka mai zuwa.
Sakamakon haka, aka cire Mbappe daga cikin tawagar PSG da ta yi balaguron tunkarar kakar wasa ta bana a nahiyar Asiya.
Daga baya ya ki ganawa da wakilan Al-Hilal, wadanda suka yi tayin da ya yi fice a duniya na kawo shi kungiyar ta Saudi Pro League.
PSG za ta fara kare kambunta na Faransa a gida ranar Asabar, inda za ta kara da Lorient.
Majiyoyin PSG sun ce yunkurinsu na baya-bayan nan na sasanta lamarin shi ne bai wa Mbappe tabbacin sayar da shi a kwantiraginsa na karshen kakar wasa ta bana. Amma ya yi watsi da wannan tayin.