Al'ummar Nijar sun yi maraba da ɗage haramcin da gwamnatin ƙasar ta yi a baya-bayan nan kan safarar mutane - musamman mutanen Agadez, yankin da baƙin haure ke bi domin tsallakawa zuwa ƙasashen arewacin Afirka da kuma Turai.
"An soke dokar ne a ranar Juma'a, kuma zuwa Lahadi, na ga motoci ƙirar 4x4 a Agadez suna shirin ci gaba da balaguronsu," kamar yadda Chehou Azizou ya shaida wa BBC. Shi ne wanda ya kafa ƙungiyar Alarme Phone Sahara, da ke aikin taimakawa wajen dawo da baƙin haure da suka makale a sahara.
A 2015 aka samar da dokar - da ke da goyon bayan Tarayyar Turai - a lokacin da aka fi samun yawaitar ƴancirani da ke kwarara Turai.
A lokacin, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa aƙalla ƴancirani 4,000 ke ratsawa ta Agadez ba tare da takardu ba.
Amma mutanen birnin na ganin dokar ta fi shafarsu - yayin da ƴancirani ke tafiya mai tsawo cikin Nijar su shigo Agadez, amma mazauna birnin ne dokar ta fi yi wa illa.
"Wannan dokar ta jefa mu cikin mawuyacin hali. Idan ɗancirani ya shigo Agadez, ba zan iya ɗaukar shi ba a mota domin za a hukunta ni, kamar yadda wani kansila Agali Zodi ya shaida wa BBC.
"Mutanen da ke dafa abinci ga ƴancirani ana hukunta su, haka ma direbobin bas na ciki da wajen birnin. mutanen da suka ba ƴancirani masauki ana hukunta su.
"Mutanen Agadez sun ji daɗin soke wannan doka."
Wani ɓangare na dokar na cewa, dalilinta shi ne tabbatar da tsaron ƴancirani da kuma rage yawan mace-mace a sahara.
"Lokacin da Tarayyar Turai da tsohuwar gwamnati ta ce dalilin dokar shi ne kare ƴancirani, ya ba mu dariya sosai," in j i Mista Azizou.
"Domin ɗaukar tsauraran matakai kan hanyar da ƴancirani ke bi, sun san yadda za su kaucewa mahukunta wanda ke haddasa yawan mace-mace da ɓatan mutane a sahara. Dubban mutane sun salwanta sakamakon wannan dokar."
Mai bincike kuma mai sharhi a Berlin Alia Fakhry ta yadda da hakan.
"Masu safara da ƴancirani na bin hanyoyi mafi hatsari ta sahara domin kaucewa jami'an tsaro," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Nijar na cikin wani lokaci na sauyi. Sojoji sun hamɓarar da Mohamed Bazoum a watan Yuli.
Sojoji da suka ƙwaci mulki sun zarge shi da zama mai kare muradun manyan ƙasashen yammaci da suka haɗa da Faransa da Tarayyar Turai fiye da buƙatun Nijar.
Tun juyin mulki, sun kori sojojin Faransa daga ƙasar tare da fito da wasu tsare-tsare da suka kira na dawo da martabar Nijar.
Amma Tarayyar Turai ta ce soke dokar safarar ƴanciranin a watan Nuwamba zai haifar da yawaitar mace-mace da ƙaruwar ƙwararar ƴancirani.
Ms Fakhry ta ce ya yi wuri a gane tasirin hakan. Kafin samar da dokar a 2015. Kuma yanzu a cewara sojoji na son dawo da tsaron kan iyakoki tare da bayar da kariya wanda zai taƙaita yawan mace-macen.
Ta kuma ce, mutanen da ke yada zango a Nijar ba ƙasashen Turai ba ne kawai suke harin zuwa, galibinsu suna son tsallakawa ne ƙasashen arewacin Afirka.
Alagie Sanneh, ɗan ƙasar Gambia da ke zaune a Agadez, ba shi da ra'ayi kan matakin soke dokar safarar ƴanciranin.
Ya san hatsarin da ke tattare da ratsa sahara tun a 2014 kafin kafa dokar.
Ya dawo Agadez bayan ya ratsa Bahar Rum har ya samu shiga Austria, kafin aka dawo da shi Gambia.
"Na san hatsarin hanyar sahara, na yi tafiya ta tsawon kwana huɗu zuwa shiga a sahara kan hanyar shiga Libya. Akwai hatsari domin direbobin da ke ɗauke da ƴancirani gudun tsiya suke ba ruwansu. Wasu motocin kan yi hatsari, su kashe kowa da ke ciki."
"A wannan saharar za ka iya rasa ranka a kowane lokaci."
Yanzu yana birnin da nufin haɗa dala 600 da ke yake buƙata ya tsallaka Tunisia.
Ko dokar na nan ko ba ta aiki, mutane da dama kamar Mista Sanneh sun ce ba za su haƙura ba da burin samun rayuwa mai inganci.
"Ina son yin aure wata rana na samu ƴaƴa. Kuma ina son su yi alfahari da ni, dalilin da ya sa na yi gudun hijira. Kodayake an koro ni, amma na kasa zama a gida."
Ya ce bai yi karatu ba kuma ya yi aiki a matsayin direba.
"A gida nakan shafe wata biyu zuwa uku, wani lokaci tsawon shekara babu aiki."
"Da wahala, dalilin da ya sa nake son zuwa Turai. Da takaici. Ba na son ƴaƴana su sha wahala kamar yadda na sha, ina son su samu rayuwa mai inganci."