Farashin dala ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin canjin kuɗaɗe a Najeriya inda a safiyar ranar Alhamis aka sayar da dala kan naira 921 a kasuwar musayar kuɗin ƙasashen waje da ke Abuja babban birnin Najeriya, kamar yadda Aminu Abubakar, ɗan kasuwa kuma mai canji ya shaida wa BBC hausa.
Wannan lamarin na nuna yadda kuɗin naira ke ci gaba da rasa daraja.
Ya ce a ranar Laraba an sayar da dala naira 918, maimakon naira 921 da aka sayar ranar Alhamis.
Ya kara da cewa daga Litinin zuwa ranar Alhamis an samu karin sama da naira 30 akan farashin dala.
A Legas kuma, Malam Liman Muhammad Inje, mai canji a kasuwar canjin kuɗaɗe ya shaida wa BBC cewa an sayar da dala a kan naira 917 zuwa 920 a ranar Laraba.
A Kano kuma Umar Suleiman, mai canjin dala ya ce dala ta tashi a kan naira 910 zuwa 920 a ranar Laraba.
Masu canjin, sun alakanta faɗuwar darajar naira kan matakin da gwamnati ta ɗauka na bai wa bankunan kasuwanci damar sayar da dala a kan farashin da kasuwa ta ƙayyade.
A ranar 14 ga watan Yunin 2023 ne, Babban Bankin kasar ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ƙasar ta dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje zuwa guda ɗaya.
A baya dai, Najeriya na amfani da tsarin canjin kuɗaɗen waje na hukuma da kuma na bayan fage, lamarin da ya sa ake samun farashin dalar Amurka iri biyu.
Kafin wannan mataki bankuna na canjin dalar ne a kan farashin da Babban Bankin Ƙasar (CBN) ya ƙayyade wadda a hukumance a lokacin darajar naira ta karye daga naira 477 zuwa 750 a kan duk dalar Amurka ɗaya.
Dalilan da suka janyo karyewar naira
Masu canjin a tattaunar su da BBC Hausa sun bayyana ra'ayinsu kan wasu dalilan da mai yiwuwa suke janyo faɗuwar darajar naira.
Aminu Abubakar, ɗan kasuwa kuma mai canji a Abuja ya ce dala yanzu an mayar da ita kamar kadara wanda hakan sake rage darajar nairar ne.
"Yanzu mutane da 'yan kasuwa da masu kuɗi har da gwamnati ma suna ajiye kuɗi da dala a banki ko a gida saboda darajar naira kullum kara faduwa take yi sai idan farashinta ya ƙaru, su fito da su domin su sayar."
"Idan aka auna kamar watanni biyu da suka wuce, dalar nan ba ta kai naira 800 ba, toh yanzu mutumin da ya saye ta a 800 a ajiya kuma ya zo ya siyar da ita a kan naira 921, ai ya samu riba da yawa."
"Matatun man fetur ɗinmu duk ba sa aiki, duk cinikin da za ayi da dala ne, kuma yanzu bankuna ba su da wadatacciyar dalar, kuma wannan na daga cikin abin da ya sa dalar ke tashi kuma darajar naira na faɗuwa."
Shi ma Umar Suleiman, mai canji a Kano ya ce da naira na da kariya amma yanzu gwamnati ta cire kariyar wanda hakan ya janyo karyewar naira.
"Dama a sayar da man fetur ne hanyar da Najeriya ke samun dala, kuma yanzu sayar da man fetur din ya ragu''.
"Kullum bukatar dala karuwa take a ƙasar saboda kusan komai ba ma yi da kanmu, shigo da su muke yi kuma da dala ake shigo da abubuwan, saboda haka ƙaruwar buƙatar dala tana kara durkushe darajar naira"
Me hakan ke nufi ga darajar naira?
Alhaji Ƙasimu Garba Kurfi wani masanin tattalin arziki ne Najeriya, ya kuma ce akwai yiyuwar farashin dalar zai sauka idan gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan da suka dace.
''Gaskiyar al'amari shi ne duk ƙasar da ta daidaita canjin kuɗinta zuwa sau ɗaya, to ya kamata kuma ace ta ranto kuɗi, domin magance yunwar da ake da ita ta dalar a ƙasar''.
Masanin tattalin arzikin ya ce amma Najeriya ba ta yi wannan ba, kafin daidaita hanyoyin canjin.
''Kafin wannan matakin CBN ta sani cewa ana buƙatar sama da dala biliyan uku, kuma har yanzu ba a samu wannan kuɗ ba'', in ji shi.
Alhaji Kurfi ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa farashin dala ya ci gaba da hauhawa a Najeriya.
Ya ƙara da cewa ƙasashen duniya da dama sun ɗauki irin wannna mataki, kuma sun samu nasara.
Ko farashin dala zai ci gaba da tashi ?
Masu canjin sun ce akwai yiwuwar farashin dala zai ci gaba da tashi idan har gwamnati ba ta kawo hanyar da zai kare naira ba.
Malam Liman ya ce da akwai kamfanonin canji da gwamati ke baiwa damar sayar da dala, a lokacin farashin dala ba wani hawa yake ba, amma tun da aka cire musu wannan damar, tun lokacin farashin dala ya yi tashin gwauron zabi.
Umar Sulaiman kuma ya ce ''idan har gwamnati bata wadata kasar da dalar ba, ba wai a ce wuri daya kawai ake iya samun ta ba, toh farashin ta ya dinga hawa kenan''.
Aminu Abubakar ya ce idan har ana son naira tayi daraja, gwamnati ya kamata ta mayar da hankalinta kan abubuwan da suke kawo buƙatar dalar musamman kamfaonin da masana'antun ƙasar domin tabbatar da abubuwa suna aiki yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta sa ido kan hada-hadar kuɗaɗe, kamar yadda ake tura kuɗaɗe masu yawa a sayi dala, idan akayi hakan kuma buƙatar dala ta ragu, darajar naira za ta tashi.