Kasuwancin fina-finan Hausa a arewacin Najeriya ya faro ne daga Silima, wanda a wancan lokacin akwai wuraren kallo na Silima a sassa daban-daban na arewa.
Masu shirya fina-finai idan sun gama shiryawa ba sa fara kai shi kasuwa, suna daukar fim su kewaya da shi sassa daban-daban na kasar har kasashe maƙwabta kamar su Jamhuriyar Nijar da Kamaru.
A wannan yanayin ake samun kudade ba kadan ba kafin a sanya shi a kasuwa.
Silima ta fara samun matsala ne lokacin da aka ƙaddamar da shari'ar Musulunci a wasu jihohin arewacin Najeriya, wannan dalili ne ya sa aka rufe gidajen kallo.
Daga wannan lokacin sai aka koma bugawa a cikin kaset, mutane da dama sun yi tunanin kasuwancin fina-finai na kaset ba zai taba mutuwa ba.
Amma ba a je ko ina ba sai aka samu ci gaban fasaha, a wannan lokacin aka koma bugawa a CD da DVD.
Malam Falalu Dorayi mai shiryawa da ba da umarni kuma jarumi ne a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ya shida wa BBC cewa a lokacin da aka fara buga fina-finan a CD kakar yawancin abokan kasuwancinsa ta yanke saka.
''Duk wani dan fim ya san lokacin da ake kasuwar CD da DVD a wannan lokacin ne kasuwar fim ta fi garawa, ma'ana aka fi samun kudi.
Domin a lokacin zai yi wahala ka shirya fim ya fito kasuwa ka fadi, sai dai ka ci riba ba kadan ba. Duk da cewa ko a zamanin da akai amfani da kaset an samu alkhairi ba kadan ba, amma ba za ka taɓa haɗawa da lokacin da zamanin CD ko DVD.''
Su ma wadannan ajujuwan na kallon fina-finan sun tasamma faduwa ne a tsakanin shekarun 2011, zuwa 2015, a wannan lokacin an shaida wa masu sana'ar saida fina-finai har da masu shirya kan cewa to fa zamani ya cimma harkar, don haka wata ƙaƙƙarfar guguwar fasaha tana nan tana tunkaro masana'antar fina-finan Hausa.
Falalu ya kara da cewa ''Mun sanar da mutane cewa Technology zai zo da wadannan abubuwan da kuke kallo za a zo wani lokacin da kallonsu zai zama tsohon ya yi. Maimakon mutane su kalla a gida sai dai a kalla ta wayar salula.
A baya za ka iya buga CD 200,000 ko sama da haka amma bayan kadawar guguwar komai ya sauya saboda wasu lokutan sai an dawo maka da su kwafi na fim din ka cewa ba su siyu ba, don haka sai dai ka yi gwanjonsu kan farashi mai rahusa.
Bayan wani lokaci ma komai ya tsaya cak babu wani abun da ake samu a harkar,'' in ji Falalu.
Falalu ya dora alhakin fara komawa kallon fina-finan Hausa a Youtube a kan zuwan ci gaban Fasahar zamani, ''musamman amfani da wayoyin komai da ruwanka wato Android, da Smart Tv wadda ake iya nade fina-finai a cikin dan katin nan na rumbun ajiya wato Flash Drive, sai a sanya maka fina-finai sama da 50 a lokaci daya.
Kuma da wuya yanzu ka shiga gidaje ka samu an kunna talabijin an zauna ana kallon fim tare da iyali. Wasu sun gwammace su kalla a wayar salula, ko ta kwamfiyuta da sauransu.''
Wannan sabuwar fasaha da hanyar kallon fina-finan Hausa ta Youtube sauki ce ga masu kallon da kuma masu kasuwanci a zaune.
Amma ga masu shirya fina-finai ko masana'antar, domin daga wannan lokacin ne aka shiga tashin hankalin rashin kasuwanci, da kuma lalacewar kudi a hannun mutane.
Saboda zuwan fasahar zamani ta janyo koma baya a masana'antar ta yadda mutane ke fadi tashin yadda za su tsira daga dan abin da ya rage hannunsu.
Me ya sa tashoshi kamar Arewa 24 ba sa nuna fina-finan Hausa sai tsiraru?
Falalu na da ra'ayin cewa labarin ya fi karfin tashar, saboda ana maganar kudi ne. Duk irin kudaden da aka zuba a tashar Arewa24 ba za ta iya ja da masana'antar Kanyywood ba, sannan ba za ta iya nuna dukkan fina-finan da ake yi ba.
Saboda duk fim din da tashar za ta haska wanda take bukata bisa radin kanta, akwai manyan kudade da za su biya kafin haskawa.
Su kuma suna fanshe kudadensu ne ta hanyar tallace-tallace da wasu shirye-shirye.
Falalu ya bada misali da shirin sa na Gidan Badamasi mai dogon zango, ''inda ba Arewa24 ce ta ke bukatar haska shirin ba, dole sai na biya kudin lokacin da za a dinga haskawa wato ''Airtime'', zan siya na ba su mu rattaba hannu kan yarjejeniya da lokacin haskawa da sauransu.
Amma idan su ne suka siya, to a nan za su nemo tallace-tallacen da za su sanya a ciki an an ne suke fanshe kudaden da suka sanya suka sayi fim har ma su ci riba.''
Shin komawa kallon fina-finan Hausa a Youtube ci gaba ne ko koma baya ga masana'antar Kannywood?
Falalu ya ce wannan ya rage kudaden shiga ga masana'antar Kannywood, amma ta wani bangaren ya taimaka mata.
Dalili kuwa shi ne; '' idan muka dauki rage kudaden shiga, a baya Kannywood ta na da damar juya miliyoyin nairori.
"Ana samun mai shirya fim guda daya da a duk shekara ya na shirya fina-finai uku zuwa hudu, kuma kowanne fim guda daya yana kawo masa manyan kudi daga miliyan 30 zuwa miliyan 25.
"Amma yanzu an kai lokacin da yawancin masu shirya fina-finai babu abin da suke yi sun nade hannu harkar ta fi karfinsu.
"Cikin manyan masu shirya fina-finai 20 da muke da su a masana'antar Kannywood zan iya ce miki babu guda wanda harkar ke gara musu halin yanzu, daga ni sai Aminu Saira ne kadai muka rage a cikin wannan harkar.''
Mutuwar kasuwar kaset da CD da DVD
Ta hanyar da kallon fina-finan Hausa a Youtube ya taimakawa Kannywood ita ce, ''A baya kannywood ta zauna ta yi shiru kanta ya buga, ba ta san me za ta yi ba saboda kasuwar kaset da DVD da CD duka sun mutu murus.
A lokacin a Youtube din fim guda daya ake nunawa na wasu 'yan makaranta da saurayin ke wulakanta budurwar da take son shi.
Shi ma wasu 'yan Kaduna ko Kano ne suka shirya shi, to a lokacin shi kadai ake iya gani ta fasahar Youtube kuam an mautkar kallon shi.
A lokacin su kuma tashar Arewa 24 su na dora wsan Dadin Kowa da Kwana Casa'in, mutane suka raja'a a kai ana kallo. Sai kuma aka zo Gidan Badamasi kafin daga bisani su dakatar da mu kan cewa za mu yi wata yarjejeniya ta bude wata tasha wato Vedio on Demand.''
Falalu ya ce a lokacin da Jarumi Lawal Ahmad ya fara dora fim dinsa Izzar So mai dogon zango a tashar Youtube babu abin da ba a fada ba wasu na cewa wahala kawai yake yi babu abin da zai samu.
''Amma a yanzu shi ne a sahun gaba na masu cin gajiyar sanya fina-finai a Youtube. Daga nan shirye-shirye kamar Bugun zuciya, da A Duniya da Na Ladidi da sauransu.
A yanzu kusan kowa ya juye komawa nuna fim dinsa a Youtube saboda an gano wata hanya ta samun kudi cikin sauki, a babu-babu a duk wata za ka iya samu kudi akalla naira miliyan 1 zuwa 700,000.
Duk da cewwa ba ita ce hanyar da 'yan fim suke bukata ba amma ko ba komai ta samawa mutane kudaden shiga da bude musu idon gano wata hanya ta daban ta samun kudi.
A ra'ayin Falalu Dorayi tashar Youtube wata sabuwar kasuwa ga 'yan Fim, matsalar da ke fuskanta shi ne har yanzu masana'antar ba ta san inda ta sa a gaba ba.
Yadda za a zauna tattauna da shugabanni a kuma samu inda aka sa a gaba.
Ko yaya masana da masu sharhi kan masana'antar Kannywood ke kallon haka?
Malam Ibrahim Sheme dan jarida ne, kuma mamallakin mujallar Fim wanda aka dade ana damawa da shi a masana'antar Kannywood.
Ya ce: ''Abu na farko da ya kamata a sani shi ne ba a yi YouTube ba domin hada-hadar kasuwancin fina-finai ba.
"Shi ya sa manyan kamfanonin shirya fina-finai na duniya kamar Amurka Hollywood da China da Indiya wato Nollywood ba sa sanya fina-finansu a YouTube, idan ka ga sun sanya to tsofaffi ne an kuma sanya ne saboda tarihi.
"Shi Youtube waje ne na talla ko isar da sakon mutum ko kungiya ko adana tsofaffin shirye-shirye.
Youtube ba kasuwa ba ce, duk mai sanyawa fim anan kamar yadda 'yan Kannywood ke sanyawa ya yi ne domin neman suna, ko a san da shi ko, abin nan da ake cewa motsi ya fi labewa, a ce har yanzu bai mutu ba ana yi da shi.
"Amma a gaskiya babu kudin kirki da ake samu abin nan ne na da babu gara babu dadi ana yi domin rufin asiri, a ganina komawa da wasu tsirarun 'yan Kannywood suka yin a sanya fina-finai a Youtube yana nuna masana'antar ta mutu amma ta koma ta yi wa mutane fatalwa ta hanyar Youtube.''
Ibrahim Sheme ya ce komawar da aka yi kallon fina-finan Hausa a YouTube ba ci gaba ba ne, abin na nuna cewa masana'antar ta mutu ne.
''Idan ka duba manyan kamfanonin da suke shirya fina-finan Hausa na da, kamar su Mandawari Enterprises, da Iyantama Multimedia da Ibrahimawa Production da Sarauniya Production da RK Studio da sauransu, wancan lokacin wadannan masu kamfanonin sun mallaki abin duniya.
"Za ka ga suna sayen gidaje da motoci da ƙadarori wasu ma har da ƙara aure. Idan aka ce an rubuta labari akwai misali Ali Nuhu a ciki akwai dan kasuwar da zai dauki miliyan biyu ya ba ki, wato ya kama fim din.
"Haka marubuta labaran fina-finan kamar su Ibrahim Birniwa a baya, a mako daya zai iya samun miliyan daya na rubutu, amma a yanzu ba za ta samu ba.''
Sheme ya ce mutuwar kamfanonin shirya fina-finai na baya daya daga cikin koma baya ne ga masana'antar Kannywood.
Tamkar a ce an wayi gari babu Warner Bros, World Disney, Colombia, United Artis na Amurka a ce yau an wayi gari babu su ba ki daya, ai ba za a ce ci gaba ne a masana'antar Hollywood ba koma baya aka samu.
Don haka a ganinsa babbar koma baya ce Kannywood ta koma YouTube, bayan shekarun da aka dauka na ganin an kafa ta ta tsaya da ƙafafunta.
Mecece makomar masana'antar Kannywood idan aka ci gaba da tafiya a haka?
Malam Sheme ya ci gaba da cewa idan aka ci gaba a haka ai masana'antar Kannywood danƙwafewa za ta yi, tilas masu shirya fina-finan Hausa su zage damtse domin nema hanyoyin da ya kamata su bi, "amma Youtube ba mafita ba ce.
"Misali shiri mai dogon Zango na IZZAR SO, Bakori TV da jarumi Lawal Ahmad ke shiryawa, dubban masu kallo na zuwa su kalla.
"Idan aka dauki waka babu wadda ta dauki hankali a bara kamar JARUMAR MATA wadda Hamisu Breaker ya yi, zuwa yanzu sama da mutane miliyan 5 sun kalleta a YouTube.
"Amma abin tambaya a nan shi ne nawa Lawal Ahmad da samu? Nawa Hamisu Breaker ya samu?
"Ba na tsammanin Breaker ya samu abin da ya kai 600,000 cikin miliyan biyar da aka kalla, don haka zama a haka ci baya ne babu inda zai kai masana'antar fina-finai ta Kannywood, sai dai janyo mata durkushewa,'' in ji Sheme.
Ibrahim ya ce duk da sanin gaibu sai Allah, amma a bisa hangen da ya yi, kan bin da ke wakana a yanzu masana'antar tsukewa za ta kara yi.
"Za ta kara karyewa, na farko yanayin tsarin tattalin arzikin duniya zai shafi kannywood, tun da an ce abin da ya ci Doma ba ya barin Awai.
''Idan ka duba alkaluman tattalin arziki ana nuna zai shafi masana'antu ko zai shafe su.
Mafita ga Kannywood
Idan har yan kannywood tana son tsira daga bala'in karayar tattalin arziki da ke tafe, dole su tashi tsaye su yi abin nan da ake kira idan kida ya sauya, rawa ma za ta sauya a ganin Sheme."Su sani fa kallon fim ya sauya fasali, hanyoyin kimiyyar sadarwa sun sauya.
"A da ana kallo a kaset, aka dawo CD aka dawo DVD yanzu an koma internet. Dole su rungumi kimiyyar zamani, kamar yadda Hollywood da Bollywood da ma Nollywood ta 'yan kudu suka shiga.
"Kuma sun mana nisa sun shiga Netflix da ke Amurka, su ma 'yan Kannywood ya kamata su yi tunanin ta yaya za su shiga.
Hatta Northflix da aka yi tamu ta arewa ya kamata su karfafa su, gidajen Silima kamar Film House da ke Kano, da Silver Bird su yi kokarin yadda za su dinga kutsawa ciki domin a dama da su.
"A daina sayar da fina-finai arha, masu saidawa wadannan Silimomin da arha a janyo su a jiki a hada karfi da karfe domin magance matsalar.''
A karshe, Sheme ya ce ya kamata gwamnati ta shiga lamarin yadda za ta bai wa masana'antar tallafi, da shiga tsakaninsu da gidajen talabijin da na Silima.
Ta magance satar basira, da tabbatar da ingancin fina-finan. A kuma janyo kungiyar MOPPAN a ba ta damar yin gyara da magance matsalolin da suka yi wa Kannywood dabaibayi.