Daga Megan Carnegie
Matasan zamani da ake yi wa laƙabi Gen Z da na sane da maganar kuɗi tun daga ranar farko da suka saka ƙafa a wurin aiki - kuma da yawa daga cikinsu ba su gamsu da albashinsu ba.
Alƙaluma sun nuna cewa 'yan zamani Gen Z na samun cigaba a wuraren aiki, kuma kuɗi ne ya fi ƙarfafa musu gwiwa fiye da mutanen kowane zamani da aka yi a baya.
Maganar rage mayar da hankali kan kuɗi ba sabon abu ba ne a yanzu - alƙaluma daga wani bincike da shafin Monster ya yi a 2016 sun nuna cewa kashi 70 cikin 100 na 'yan Gen Z a Amurka sun bayyana kuɗi a matsayin abin da ya fi ƙarfafa musu gwiwa tare da kuma inshorar l,afiya.
Sai dai ƙwararru sun ce shekaru da yawa bayan haka, matsin tattalin arziki ya sa waɗannan matasa ƙarin maitar kuɗi. A shekarar da ta gabata, bayanai sun bayyana cewa hasashen albashin da za su samu ya ƙaru sosai - da yawa na neman dubban ɗaruruwa tun daga farkon shekarun fara aiki.
Wannan ba ƙramin abu ba ne idan aka lura cewa 'yan zamanin Gen Z sun tsinci kan su a wani yanayi na musamman.
Sun girma suna ganin iyayensu 'yan Gen X na fama da matsalar kuɗi cikin tsananin tattalin arziki; yanzu kuma da ake fama da wasu matsalolin na tattali, sun tsunduma cikin nasu matsalolin na rashin tabbas.
Sakamakon haka ne suke neman ƙarin kuɗaɗe daga iyayen gidansu a yanzu fiye da kowane lokaci, kuma tun daga farkon fara aiki, inda masana suka ce matasan a shirye suke su bar aiki don samun wanda ya fi shi albashi nan take.
Wasu na kallon 'yan Gen Z a matsayin "mayun albashi". Wasu lokutan, a cewar ƙwararru, abu ne mawuyaci dattijai su iya gane dalilin da ya sa matasan ke saka maitar kuɗi a gaba.
"A shekarun Gen Z, tsofaffi kan yi aikin awa 40 duk mako, kuma su tara kuɗin da za su sayi gida har ma su fita yawon sharholiya a ƙarshen mako," a cewar Corey Seemiller, wani malamin makaranta kuma bincike wanda ya gabatar da maƙala a TEDx kan Gen Z.
"Gen Z na aikin awa 50 a mako, da kuma awa 20 a harkokinsu na gefe, duk da haka da kyar suke samun kuɗin da za su biya haya."
Amma akwai wasu abubuwa daban baya ga maitar kuɗi kawai. Bugu da ƙari, maitar kuɗin da suke yi ka iya amfanar kowa da kowa.
Tangal-tangal da kuma rashin tabbas
Akasari ana bayyana Gen Z a matsayin matasan da aka haifa a tsakanin 1997 zuwa 2012. Su ne suka taso a cikin matsalolin tattalin arziki daban-daban. Wasu daga cikinsu ma rashin tabbas kawai suka sani.
"An raine su har zuwa lokacin da iyayensu ke kokawa kan ƙarancin kuɗin gudanar da ayyuka da kuma abubuwan da suka faru saboda hakan," in ji Seemiller.
Akasarin matasan sun shiga aiki ne a karon farko ko kuma suna farkon farawa lokacin da annobar korona ta dosa. Baya ga hayaniyar aikin da ke hana su shiga matakin albashi na gaba, sai kuma ga korar ma'aikata - wasu alƙaluma na cewa fiye da yadda ƙarnin da ke biye da su.
"Waɗannan abubuwa ne suka mamaye tunaninsu, sai kuma ga fargabar rashin kuɗi," kamar yadda Seemiller ya bayyana.
Da yawa daga cikin 'yan Gen Z na fuskantar hauhawar farashi a faɗin duniya, kuma yayin da kuɗin da ake kashewa wajen ilimi da yawansu na karɓar bashin kuɗin makaranta.
Alƙaluma daga Bank of America na 2022 sun nuna 'yan Gen Z masu yawa sun ba da rahoton gaza samun kuɗin da za su biya bashin da suka karɓa a wannan zangon.
A takaice, suna matukar fargaba kan kudadensu fiye da sauran al'ummomin da suka gabata. Wani bincike na Cigna na ma'aikatan duniya 12,000 ya nuna cewa kashi 39 na matasa sun ambaci rashin tsaro a matsayin babban abin damuwa, idan aka kwatanta da kashi 34 na wadanda suka gabata da kuma kashi 29 na masu shekaru 50 zuwa 64. Matasan ma'aikata sun damu musamman game da hauhawar farashin rayuwa da kuma yadda hakan zai shafi rayuwarsu nan gaba.
"Duk daga bayanan da aka samu, a bayyane yake cewa ma'aikatan matasa suna son a biya su yadda ya kamata kuma a yi la'akari da su ta dalilin darajar da suke kawowa wurin aiki, amma kuma suna neman kwanciyar hankali." in ji Sam Chen, wanda ya kafa Gen Z kuma Shugaban wani kamfanin Amurka wdda ke hada mutane da aikin da ya dace da su, mai suna Fetti. Tabbas, wani bincike na 2022 daga dandalin neman aiki mai suna Handshake, ya nuna cewa kashi 74 mutane 1,400 da suka kammala karatun digiri a Amurka a shekarar 2023 da aka bincika sun ce suna ba da fifiko ga kwanciyar hankali da albashi daga masu daukan aiki, abubuwan da suka fi girma ciki har da sunan masu daukan aiki (41%), da fannin aiki mafi bunkasa (39% ) da kuma fa'idojin aikin (66%).
A taikaice dai, in ji Seemiller, matasan na neman albashi mai tsoka domin su sami natuswa a rayuwarsu. "Suna so su iya rayuwa a kan albashin su kuma ba tare da biyan kudin abubuwan gudanar da rayuwa ba," in ji ta. "Nazarin da na yi ya nuna cewa kasancewa mai farin ciki da kwanciyan hankali, da kuma samun rayuwa a natse, tare da samun kudin za su iya gudanar da rayuwans shi ne abu mafi muhimmanci ga matasa wurin samun aiki-ba wai su zama masu kudi su yi yawon duniya ba"
Don haka, ba lallai ba ne cewa matasa su kasance masu kwadayi ko son kudi ba; Akasari, in ji masana, kawai suna son su iya biyan bukatunsu ne. Ma'aikata a wuraren da ke da tsadar rayuwa - musamman manyan biranen - suna bukatan albashi mai tsoka; misali, a wasu kididdigan da aka yi, matsakaicin albashin matakin shiga ga ma'aikatan Amurka a karshen 2022 shine $55,260 (£ 44,627), duk da haka mutumin da ke zaune a San Francisco zai bukaci samun sama da $74,280 (£ 59,978) - bayan haraji - domin biyan bukatunsa.
Duk da yake, ba shakka, tsadar rayuwa ta shafi kowa, matasa ba su da nisa a tazaran rayuwa , don haka ba su da kwanciyan. Millennials, alal misali, sun dade a cikin rukunin ma'aikata, kuma sun samun kudi, wasu daga cikinsu sun iya siyan gidaje kafin farashin ya tashi game hauhawar farashin da Covid-19 ya haddasa.
Seemiller ya ce "ba za a iya kwatanta rayuwar matasan yanzu da na wadanda su ka gabata ba, dangane da kwanciyar hankali na kudi, idan aka kwatanta da lokacin da suke shiga aikin," in ji Seemiller. "Sauran rukunnen jama'a, ban da watakila wadanda suka shiga aiki a lokacin koma bayan tattalin arziki, ba su fuskanci wannan yanayin ba lokacin da suke matasa."
Sharuddan da suka dace don karin albashi?
Ko matasa za su sami albashi mai tsokan da suke bukatan? A wani bangaren alamun na da kyau.
Yadda fagen aiki ya ke a yanzu yana nuni da yanayi mai kyau ga matasa ma'aikata. Duk da cewa daukar ma'aikata ya dan yi tun lokacin barkewar cutar corona, kasuwar masu neman aikin har yanzu tana ci cikin kasashe da yawa, wanda ke nufin har yanzu ma'aikata suna da ikon shigar bukatu kan masu daukn ma'aikata.
Masana sun ce hakan na nufin cewa matasa sun fi kwarin gwiwan neman karin albashi; suna amfani da damar da su ka samu ta dalilin gasa mai tsanani wurin nemn hazaka, wasu nazarin sun nuna cewa suna farin cikin samun biyan bukatunsu. Bayanan Handshake sun nuna cewa fiye da kashi 80 na masu amsa binciken sun yi imanin za su iya samun aikin da zai biya su albashi mai kauri - ya kuma cika masu burinsu na rayuwa..
Amma akwai abin dubawa. Bayanai daga dandali na daukar ma'aikata mai suna Sonovate, wanda ya binciki kanana da matsakaitan 'yan kasuwa 500 na Burtaniya wadanda suka kara albashi don rike ma'aikatansu masu hazaka, ya nuna cewa 54 ko shakka babu za su iya ci gaba da wannan matakin kara albashi har na wani tsawon lokaci. A takaice dai, mafi yawan matasa na iya samun kansu cikin halin rashin jin dadin aabin da wadanda suka dauke sus aiki za su yi masu nan gaba.
Matasa ma su aiki na son a biya su yadda ya kamata kuma a yi la'akari da irin hazakar da su ke da shi a wurin aiki, amma kuma suna neman kwanciyar hankali - Sam Chen
Zai iya zame ma matasa masu aiki dole su suaya wuraren aiki idan suna son karin albashi. Kuma wasu matasan na yin yunkurin samun nasu kudina hannunsu, musamman idan ba za su sami abin da suke bukata kai tsaye daga wadanda suke yiwa aiki ba. Yayin da ake fuskantar matsalr albashin da ba ya iya biyan bukatu saboda hauhawar farshin kayayyaki, suna neman sabbin hanyoyin samun kudin shiga fiye da wadanda suka gabata, a inda matasan za su iya neman wani aiki (30%) da kuma kara sa'o'in aikin su fiye da wadanda suka gabata a 17% da 13%, bi da bi, bisa ga rahoton Randstad na 2023 Workmonitor.
Seemiller ta ce tsofaffin al'ummomi na iya tsayawa don cin gajiyar wannan albashin. Kwarai, matasa na kokarin habaka yanayin samun kudin su, amma Seemiller kuma ta yi imanin cewa neman albashin su yana da alaka da bukatar da su ke da shi n adalci da sanin ya kamata.
"Su rukuni ne na mutane da ke fadin abubuwa yadda su ke, suna magana lokacin da suka ji aikin da suke yi ba a biya su yadda ya kamata ba," in ji ta. "ta yin haka, suna jawo hankali kan wasu al'amurra da kuma ingiza sauran al'umma sa sami kwarin gwiwan neman abin da ya dace, sassaucin aiki ko kuma sa'o'in aiki mafi dacewa."
Kamfanoni da dama sun riga sun fara jin wadannan canje-canjen. Bayanai na Beamery na watan Afrilun 2023 sun nuna kashi cewa 91% na shugabannin kasuwancin Burtaniya 700 da aka bincika sun yadda da cewa bukatun da kananan ma'aikata suka bayyana na iya yin tasiri ga daukacin al'umma.
Kamar yadda wasu tsoffin ma'aikata ke gunaguni game da manyan bukatun albashin matasa, albashin yana zama abu mafi mahimmanci ga al'umma baki daya. Gallup na bin abin da masu neman aiki a Amurka suka fi baiwa fifiko tun daga 2015, kuma albashi ya haura daga mataki na huɗu (41%) zuwa mataki na farko (64%)
Dangane da ko albashin zai ci gaba da zama abu mafi muhimmanci ga matasa , Seemiller tana gani zai yi wahala a yi tunanin za su sauko kasa ko kuma su tsaya a inda suke matukar su ka kai wani matakin albashi . "Alamomin mu suna nuna cewa su mutane ne wadanda su ka damu da farin ciki, da kwanciyar hankali kan albashi mai tsoka kadai'', A cewar ta "Ko ta yaya, sun maida hankali sosai kan daidaito kuma za su ci gaba da kasancewa kan gaba idan suka ga cewa ba su samun abin da ya dace."