BBC Hausa of Sunday, 18 June 2023

Source: BBC

Mece ce cutar Anthrax kuma ta yaya ake kamuwa da ita?

Hoton alama Hoton alama

A ranar Laraba ne likitoci a jihar Kaduna da ke Najeriya suka fitar da wata sanarwa, wadda a cikinta suke gargaɗin mutane kan cutar Anthrax.

Tuni hukumomi a wasu ƙasashe maƙwabtan Najeriya suka ayyana ɓarkewar cutar, kamar Ghana.

Duk da cewa ba a samu ɓullar cutar a Najeriya ba, amma masana na ganin cewa akwai haɗari sosai domin cutar na iya yaɗuwa cikin hanzari.

Haka nan wani ƙarin haɗarin shi ne yadda ake tunkarar lokacin babbar sallah, inda mutane ke ta'ammali da dabbobi waɗanda ake amfani da su domin layya.

A Najeriya ma hukumomi sun gargaɗi mutane kan cin naman dabbobi barkatai.

Mece ce cutar Anthrax?

Anthrax wata cuta ce mai tsanani wadda ƙwayoyin cuta na ‘bacteria’ ke haifarwa.

Yawanci ana samun ƙwayoyin cutar ne a cikin ƙasa, kuma cutar ta fi kama dabbobin gida da kuma na daji.

Alamomin cutar Anthrax

Alamomin cutar Anthrax ya danganta da yadda ta shiga jikin mutum.

Alamomin za su iya bayyana daga kwana ɗaya bayan kamuwa da cutar zuwa sama da wata guda.

Sai dai ko ta yaya mutum ya kamu da cutar akwai haɗarin cewa za ta haifar da mummunar rashin lafiya ko ma mutuwa matuƙar ba a yi maganin ta da wuri ba.

Wasu daga cikin alamomin cutar sun haɗa da:

  • Mura


  • Zazzaɓi da zafin jiki


  • Ciwon ƙirji


  • Numfashi sama-sama


  • Jiri


  • Amai da ciwon ciki


  • Ciwon kai


  • Raunin jiki


  • Ciwon jiki


  • Yadda mutane ke kamuwa da Anthrax

    Mutane na kamuwa da ita ne a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.

    Cutar kan fara aiki ne da zarar ta shiga jikin ɗan’adam.

    Daga nan sai ƙwayar cutar ta hayayyafa cikin sauri sannan ta yaɗu zuwa cikin jiki, daga nan ne takan fitar da sanadarai masu guba wadanda ke cutar da ɗan'adam ta hanyar haifar da rashin lafiya mai tsanani.

    Ƙwayar cutar kan shiga jikin ɗan’adam ne idan suka shaƙe ta, ko mutum ya ci abinci ko ya sha ruwa wanda ke ɗauke da ƙwayoyin cutar.

    Haka nan ƙwayar cutar kan iya shiga jikin ɗan’adam ta wata kafa, kamar idan mutum ya yanki ko kuma ya ƙurje fatarsa.

    Ta yaya dabbobi ke kamuwa da cutar Anthrax?

    Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwa wanda ke ɗauke da ita.

    Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.

    Hanyoyin kariya

    Dr Dahiru Murtala wani likita ne a Najeriya, ya ce babbar hanyar da za a guje wa kamuwa da cutar ita ce ta hanyar guje wa cuɗanya da fatun dabbobi.

    Haka nan yana da kyau waɗanda sana'arsu ce cuɗanya da dabbobi su rinƙa amfani da ababen kariya, kamar safar hannu da takunkumin fuska na kariya.

    Sannan ya ce da mutum ya nemi agajin masana lafiya da zarar ya yi zargin cewa ya kamu da cutar ta hanyar zuwa asibiti.

    A Ghana dai tuni hukumomi suka haramta yankawa da cin nama na tsawon wata guda a yankin Gabas mai nisa na yankin arewacin ƙasa sanadiyyar ɓarkewar cutar ta Anthrax.

    Haka nan an haramta zirga-zirga da dabbobi kamar shanu da tumaki domin daƙile yaɗuwar cutar.

    Bayanai sun ce mutum ɗaya ne ya mutu sanadiyyar cutar a yankin, haka nan aƙalla dabbobi 30 ma sun mutu duk sanadiyyar kamuwa da cutar.

    Akwai barazanar cewa cutar za ta iya yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar.