BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Mene ne aikin Sarkin Ingila kuma su wane ne 'ya'yan sarautar?

Sarki Charles III Sarki Charles III

A ranar Asabar 6 ga watan Mayu, Sarki Charles III zai zama sarkin Ingila na 40 wanda za a naɗa a cocin masarautar Birtaniya na Westminister Abbey.

Ya zama sarki ne bayan rasuwar mahaifiyarsa, Elizabeth II, a watan Satumba.

Mene ne aikin Sarkin Ingila?

Sarki a Birtaniya shi ne shugaban ƙasa. Sai dai ikonsa na wakilci ne kuma na je-ka-na-yi-ka, sannan ba shi da ɓangare a siyasance.

Yakan karɓi sakonnin bayanai daga fadar gwamnati a kullum, ciki har da bayanan da ake buƙata kafin duk wata ganawa ko kuma takardu da ke neman sanya hannunsa.

A al’adance firaminista kan gana da Sarki duk ranar Asabar a fadar Buckingham domin yi masa bayani a kan ayyukan gwamnati.

Irin ganawa ta sirri ce, kuma ba a fitar da wani bayani a hukumance kan abubuwan da ake tattaunawa.

Sarkin yana kuma da wasu ayyukan na gwamnati da yake gudanarwa, waɗanda suka haɗar da:

  • Kafa sabuwar gwamnati - bisa al’ada, shugaban jam’iyyar da ta lashe zaɓe yakan je fadar Buckingham, domin neman izinin kafa gwamnati. Sarkin ne kuma ke rushe gwamnatin da ke mulki kafin a yi zaɓe.


  • Ƙaddamar da gwamnati da kuma jawabin sarki: a al'adance sarki kan buɗe zaman majalisa na shekara da jawabi, wanda yakan yi daga karagar da ke majalisar dattijai inda yake bayyana abubuwan da gwamnati ke shirin aiwatarwa.


  • Amincewar sarauta: idan majalisa ta fitar da sabon ƙuduri dole sai sarki ya amince da ita kafin ta zama doka. A 1708 ne karo na ƙarshe da masarauta ta ƙi amincewa da wani ƙudurin da ya fito daga majalisa.


  • Bugu da ƙari sarki yakan jagoranci bikin shekara-shekara na tunawa da dakarun da suka kwanta-dama wanda akan yi a ginin Cenotaph da ke birnin Landan.

    Daga cikin aikin sarkin kuma, shi ne karɓar baƙuncin shugabannin ƙasashen duniya da kan kai ziyara Landan - Kamar shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa - kuma yakan gana da jakadun ƙasashe masu ofisohin jakadanci a Landan.

    A ziyararsa ta farko, Charles ya je Jamus ne, inda ya zama basaraken Ingila na farko da ya yi jawabi a gaban majalisar dokokin ƙasar.

    Sarkin shi ne shugaban ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila wato Commonwealth mai mambobi 56 a ƙarƙashinta, da yawan mutane kimanin biliyan biyu da rabi.

    Uwargidan sarki, Camilla na taimaka masa wajen gudanar da ayyuka, yayin da ita ma take gudanar da ayyukan da suka shafi ƙungiyoyin ba da agaji guda 90 da take da alaka da su.

    Mafi yawan ƙungiyoyin masu ba da agaji kan harkar lafiya da kuma agaza wa waɗanda aka yi wa fyade.

    Me zai faru a bikin naɗin sarautar Sarki Charles?Za a naɗa Sarkin da Sarauniya a bikin da za a gudanar a cocin Westminster Abbey.
    b


    Bikin, wata hidima ce ta addini da ake gudanarwa a ƙarƙashin dokokin ɗarikar Anglican wadda shugaban cocin Ingila zai jagoranta. Za a shafa wa sarkin wani mai na musamman sannan a miƙa masa Sandar Girma.

    Daga ƙarshe, shugaban cocin zai ɗora kambin sarauta na St Edwards a kansa-wanda aka ƙera shi da zinariya tun a 1661.

    Shi dai wannan kambi sarkin zai sanya shi ne sau ɗaya a tsawon rayuwarsa.

    Naɗin sarautar biki ne na gwamnati, kuma ita ce take ɗaukar ɗawainiyar gudanar da shi, tare da tantance waɗanda za su halarta.

    Su wane ne 'yan gidan sarautar?
  • Yarima William shi ne babban ɗan Sarki da matarsa ta farko, Gimbiya Diana. Bayan rasuwar Sarauniya, sai ya gaji sarautar yariman Wales da Cornwall tare da ci gaba da riƙe sarautarsa ta yariman Cambridge. Sunan matarsa Catherine kuma ita ce Gimbiyar Wales da Cornwall da kuma Cambridge. Suna da yara uku: Yarima George da Gimbiya Charlotte da Yarima Louis.


  • Gimbiya Anne ita ce kaɗai ƴa mace da Sarauniya ta haifa. Tana auren Vice Adm Timothy Laurence. Ta haifi yara biyu da mijinta na farko, Captain Mark Phillips, su ne Peter Phillips da Zara Tindall.


  • Yarima Edward shi ne Yariman Edinburgh, kuma shi ne ɗan autan Sarauniya. Matarsa, Sophie Rhys Jones, ita ce gimbiyar Edinburgh. Suna da yara biyu, Lady Louise Windsor da kuma James Moutntbatten-Windsor, yariman Wessex.


  • Yarima Andrew shi ne ɗan Sarauniya na biyu kuma yariman York. Yana da yara biyu da matarsa ta farko gimbiyar York, Sarah Ferguson, su ne Gimbiya Beatrice da Gimbiya Eugenie. Yarima Andrew ya yi murabus daga harkokin sarauta bayan wani shirin 'BBC Newsnight' kan zargin da aka yi masa na cin zarafin wata mata da ake kira Virginia Giuffre. A watan Fabrairun 2022 ya biya wasu kuɗaɗen da ba a bayyana adadinsu ba domin sasantawa a kan ƙarar da Virginia Giuffre ta shigar a wata kotun Amurka.


  • Yarima Harry shi ne yariman Sussex kuma shi ne ƙanin Yarima William. Sunan Matarsa Meghan Markle wadda ita ce Gimbiyar Sussex. Suna da yara biyu, Yarima Archie da kuma Gimbiya Lillibet. A shekara ta 2020 sun bayyana cewa za su yi murabus daga harkokin saurauta, su koma birnin California da zama.


  • Yayab ake gadon sarautar Birtaniya?

    Tsarin gadon sarauta ya fayyace wane ne a cikin ƴaƴan masarauta zai gaji wanda ke kan mulki a lokacin da sarki ya rasu, ko kuma ya sauka don raɗin kansa.

    Na farko a cikin jerin masu gadon sarauta shi ne babban ɗan sarkin da ke kan mulki.

    An yi gyara ga dokar tsarin gadon sarautar a 2013 domin tabbatar da cewa ba a fi bai wa ƴaƴa maza muhimmanci a kan yayyensu mata a wajen gadon sarauta ba.

    Magajin Sarki Charles shi ne babban ɗansa namiji, Yariman Wales.

    Babban ɗan Yarima William, Yarima George shi ne na biyu a jerin magadan sarautar, sannan ƴarsa mace, Gimbiya Charlotte ita ce ta uku. Yarima Louis shi ne na huɗu sai Yarima Harry a matsayi na biyar.

    Ya karɓuwar 'yaƴan sarautar Birtaniya a wajen al'umma?

    Domin tantance tunanin al'umma game da sarautar Birtaniya gabanin naɗin sarautar Sarki Charles, shirin BBC Panorama ya nemi jin ra'ayin al'umma.

    Sakamakon da aka samu ya bayyana cewa kashi 58% na al'umma na goyon bayan ci gaba da bin tsarin masarauta a maimakon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, wanda ya samu kashi 26%.

    A ina iyalan masarautar Birtaniya ke zama?

    Sarki Charles da Sarauniya Camilla na rayuwa ne a fadar Buckingham. A baya suna zama ne a gidaje biyu, wato Clarence House da ke Landan da kuma Highgrove da Gloucestershire.

    Sauran gidajen da iyalan masarauta ke zama sun haɗar da gidan sarauta na Windsor, Sandringham a Norfolk da fadar Holyroodhouse da ke Edinburgh da gidan sarauta na Balmoral da ke Aberdeenshire.

    A watan Agustan 2022, Yarima William da Gimbiya Catherine na Wales sun bar fadar Kensington da ke yammacin Landan, inda suka koma rayuwa a Adelaide Cottage, da ke rukunin gidajen sarauta na Windsor.