Janye tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi ya jefa da dama daga cikin al'ummar ƙasar cikin tsaka-mai-wuya sakamakon sabon farashin man fetur.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyar maye gurbin motoci masu amfani da man fetur da motoci masu amfani da lantarki da kuma iskar gas.
A ranar Talata 18 ga watan Yuli gidajen mai a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya suka ƙara farashin litar man fetur daga naira 537 zuwa sama da naira 600.
Ƙarin farashin litar man ya zo makwonni ƙalilan bayan gidajen mai sun mayar da farashi naira 500 daga naira 198 jim kaɗan bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar babu tanadin tallafin mai cikin kasafin kuɗin shekara ta 2023.
A dangane da hakan tuni al`ummar ƙasar mai arziƙin mai, suka fara nemar wa kansu mafita ta hanyar sauya injinan motocinsu masu amfani da fetur zuwa masu amfani da iskar gas, bayan masana sun tabbatar da cewar hakan ba shi da hatsari.
Ko amfani da gas ya fi arha?
Wani masanin makamashi Injiniya Patrick Ezenachi ya shaida wa BBC cewar amfani da gas maimakon fetur abu ne mai kyau musamman idan aka yi la`akari da yadda gas yake fitar da taƙaitaccen hayaƙi mai gurɓata yanayi (carbon).
Da aka tambaye shi ko nawa ne farashin kafa tukunyar gas a mota? Injiniya Ezenachi ya ce ba ya wuce naira 200,000 zuwa naira 300,000 wajen sayen ƙunshin na`urorin da ake amfani da su ko da yake aikin ya danganta da yanayin mota.
Sauyin yana sa inji ya daɗe bai lalace ba
Injiniya Fahiz Olamilekan ya bayyana cewar sauyin ba shi da hatsari kuma yana sa injin mota ya yi ƙarko idan aka kwatanta ta injin da yake amfani da fetur.
Ya ƙara da shawartar masu son komawa amfani da gas maimakoin fetur a motocinsu, su tuntubi ƙwararru don kauce wa matsala.
Yadda ake sauyawa
Masu aikin sauya yanayin mota, za su sanya tukunyar gas a bayan motar daga nan gas din zai shiga bututun da motar za ta yi amfani da shi don aiki.Akwai wani makunni a ɓangaren direba da shi ake amfani wajen sauya motar ta yi amfani da gas maimakon fetur.
Tukunyar gas ɗin za ta iya ajiye kilogram takwas ko takwas da rabi na gas wanda za a iya tafiyar nisan kilomita 150 da shi, idan kuma akwai cunkoson ababen hawa a hanya gas ɗin zai iya tafiyar kusan kilomita 125 ne kawai.
Idan tukunyar gas a cike take direba yana iya tafiyar kilomita 200 a babbar hanya.