BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Messi ka iya komawa Al-Hilal da taka leda, Real Madrid na zawarcin Bellingham

Dan wasan Argentina Lionel Messi Dan wasan Argentina Lionel Messi

Dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi, mai shekara 35, ka iya bin abokin hamayyarsa a duniyar tamaula, kuma dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, dan shekara 38, zuwa kulub din kasar Saudiyya, bayan yi wa dan wasan tayin fam miliyan 320 a duk shekara. Wannan bayani dai ya biyo bayan sanarwar da Messi ya yi na tabbatar da barin kulub dinsa na Paris St-Germain. (Telegraph - subscription required)

Kungiyar kwallon kafar Al-Hilal ta Saudiyya, ka iya samun abokan hamayya da ke zawarcin Messi kamar na League da Inter Miami, ta tsohon dan wasan Manchester United da zakaran tamaula na Ingila David Beckham. (Guardian)

Real Madrid na tattauna kan batun dan wasan Borussia Dortmund, kuma na tsakiyar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, sai dai kulub din na Jamus na cewa har yanzu kungiyar ta Sifaniya ba ta aiko da wasikar zawarcinsa ba.(Sky Germany)

Sheikh Jassim ya watsar da shirin sayan dan wasan gaba na Brazil Neymar, mai shekara 31, ya na dai hakilon idan shirinsa na sayan Manchester United ya tabbata, zai yi zawarcin zakakurai kuma fitattun 'yan wasan kwallon Faransa, da ake yi wa lakabi da 'yan uku, wato Kylian Mbappe, mai shekara 24, da ke taka leda a Paris Saint-German, sai kuma dan wasan Bayern Munich Kingsley Coman, mai shekara 26, da dan wasan Real Madrid Eduardo Camavinga, mai shekara 20.(Bild's Christian Falk)

Dan wasan Tsakiya na Ingila da ke taka leda a West Ham Declan Rice, mai shekara 24, da dan wasan gaba na Faransa Moussa Diaby, dan shekara 23, da dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha, mai shekara 30, da dan wasan Ivory Coast kuma na tsakiyar Ingila Marc Guehi, 22, na daga cikin 'yan wasan da shugaban Arsenal Mikel Arteta da ya ke zawarci da fatan kai su kulub din domin taka leda. (Daily Mail)

Dan wasan gaba na Netherland Wout Weghorst na son ci gaba da taka leda a Manchester United, amma har yanzu kulub din ba su ba shi faragar tattaunawa kan batun zaman shi a Old Trafford ba idan kwantiraginsa ya kare da Burnley. (Telegraph - subscription required)

Roma ta sanya farashin fam miliyan 35 zuwa 40 kan dan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 25, gabannin bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa da ake saran kungiyoyin Manchester United, Tottenham da Paris St-Germain ka iya sha'awar daukar dan wasan. (Calciomercato - in Italian)

Marseille za ta na tuntubar Crystal Palace kan dan wasa Zaha idan sun kai bantensu na zuwa Champions League. (Foot Mercato - in French)

Newcastle ka iya ciwo kan Raphinha na Leeds zuwa Premier League kan farashin fam miliyan 70, domin dauko dan wasan na Barcelona kuma dan Brazil.(The Sun)