Messi ya bai wa PSG haƙuri kan zuwansa Saudiyya
Lionel Messi ya nemi ahuwr abokan kwallonsa na PSG tare da cewa yanzu yana jira ya ga hukuncin da ƙungiyar za ta yanke a kansa bayan zuwansa Saudiyya ba tare da izini ba.
An dakatar da kyaftin ɗin Argentinan na mako biyu saboda tafiyar da ya yi.
Wannan na zuwa ne bayan rashin nasarar da PSG ta yi a gida a hannun Lorient a ranar Lahadi – rashin nasara na uku kenan cikin wasa shida – kuma Messi ya buga minti 90 na wasannin.
“Ina ba da haƙuri kan abin da na yi, ina jiran hukuncin da kulob zai yanke a kaina,” kamar yadda Messi ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa a Instagram.
"Gaskiya na yi tsammanin za mu samu rana guda ta hutu kamar yadda muka saba a makonnin baya.
“Na shirya tafiyar nan zuwa Saudiyya a baya ina sokewa. A wannan karon ba zan iya sokewa ba.”
Messi ya shirya barin PSG a ƙarshen wannan kakar idan kwantaraginsa ya ƙare.
Ɗan wasan mai shekara 35 wanda ƙungiyar ta ci tararsa, yana da matsayin wakilin buɗe ido na Saudiyya.
Kocin PSG Christophe Galtie ya ce “babu abin da ya shafe shi” da dakatar da Messi, kuma ya yi Allah-wadai da zanga-zangar da magoya baya suka yi a ƙofar gidan Messi.
“Dakatarwar da aka yi wa Messi na da alaƙa da rashin ƙoƙarinsa a ƙungiyar, ba za mu boye komi ba.
“Babu abin da ya shafe ni da wannan hukunci. Ni ma labari aka ba ni. In nace na ji daɗi na yiƙarya.”
PSG ne ke matsayi na 1 da tazarar maki biyar da kuma wasanni biyar da ke gabansu, sai dai an cire su daga Champions Lig an kuma cire su daga kofin French.
An samu zanga-zangar magoya baya bayan rashin nasarar da PSG ta yi a hannub Lorient.
Sun taro a wajen gidan ɗan wasan gaban Brazil Nyemar a ranar Laraba suna ihu kan cewa sai ya bar ƙungiyar.
Tun bayan raunin da ya ji a idon sawunsa ɗan wasan mai shekara 31 yake jinya.
Wannan mataki na magoya bayan ya sanya hukumomin ƙungiyar ƙara yawan jami’an tsaro a gidan Messi da Nyemar da ɗan wasanta na tsakiya ɗan Italiya Marco Verratti da kuma Galtier, haka kuma an ƙara jami’an tsaron a filin atisayensu.