BBC Hausa of Thursday, 20 July 2023

Source: BBC

Milos Kerkez ya koma Bournemouth

Milos Kerkez Milos Kerkez

Bournemouth ta sayi dan wasan bayan kasar Hungary Milos Kerkez daga AZ Alkmaar kan kudin da ba a bayyana ba.

Kungiyar ta sanar da cewa dan wasan bayan mai shekaru 19 ya amince da kwantaragin shekaru da dama.

Zuwan Kerkez ya biyo bayan sayen dan wasan gaban kasar Holland Justin Kluivert, mai shekara 24, daga Roma, da kuma dan wasan tsakiyar Lyon, Romain Faivre, mai shekara 24.

Kerkez ya koma AZ a watan Janairun 2022 bayan ya fara wasa a bangaren matasan AC Milan.

Ya buga wasanni 52 a cikakkiyar kakarsa ta farko a kulob din ta Eredivisie, inda ya taimaka musu zuwa matsayi na hudu a teburin gasar Holand kuma inda ya zura kwallo biyar a raga.

Matashin ya taka rawar gani a lokacin da AZ ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin Europa, inda ta sha kashi da ci 3 -1 jimilla a hannun West Ham.

Kerkez ya ci wa Hungary wasa na farko cikin manyan wasanni takwas a watan Satumba, inda ya buga dukkan mintuna 90 na wasan da suka doke Jamus da ci 1- 0 a gasar Nations League a Leipzig.