BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Misrawa ba su manta da kisan ɗaruruwan 'Yan Uwa Musulmi ba bayan shekara 10

Hoton alama Hoton alama

Shekara 10 da suka wuce, an kashe ɗaruruwan mutane, mafi yawansu fararen hula, lokacin da sojoji suka yi dirar mikiya kan masu zanga-zangar zaman dirshan don nuna goyon baya ga shugaban da aka kawar mai kishin Musulunci. Kisan na magoya bayan Mohammed Morsi, shi ne abu mafi muni da aka taɓa ganin irinsa, kuma ɗaya daga cikin munanan abubuwan tarihi a Masar.

Kamar yadda wakiliyar BBC Sally Nabil ta ruwaito cewa daga birnin Alƙahira, har yanzu ba a manta da abin da ya faru ba a ranar.

"Na yi fatan a ce ba na raye a yau," inji Amr, wanda aka yi zaman dirshan ɗin na kwana 50 da shi, a dandalin Rabaa al-Adawiya da ke gabashin babban birnin ƙasar.

Amr yana ɗan shekara 20 ne kacal lokacin da ya ga "motocin rusa gini suna ruguza sansanin da mutane ke ciki, suna kuma kwashe duk wani abu da ya shiga gabansu".

Ya ce: "An kashe duk wani nau'in tausayi da jin-ƙai a ƙasar Masar, a wannan rana".

Watanni bayan abin da ya faru a Rabaa ne aka kama Amr, aka kuma zarge shi da ɓarnata kayan gwamnati da kawo tashi hankali da kuma wasu laifukan na daban. Ya shafe aƙalla shekara biyar a gidan yari, kafin ya gudu daga Masar a 2018 ya kuma samu mafaka a Birtaniya.

Ya ce ya shiga zanga-zangar zaman dirshan ɗin ne saboda tsoron kada ƙasarsa ta faɗa hannun janar-janar ɗin soji.

Amfani da ƙarfin soji wajen tarwatsa zaman dirshan ɗin na Rabaa da kuma irinsa da aka yi a dandalin Nahda a rana guda babban abin tashin hankali ne a tarihin Masar, ya kuma kawo gagarumin sauyi a kan makomar ƙasar wadda ta fi kowacce yawan jama'a a ƙasashen Larabawa.

Lokacin da Mohammed Morsi, jagora a ƙungiyar ƴan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood ya hau mulki a 2012, shi ne farar hula na farko da ya samu zama shugaban ƙasar ta hanyar dimokuraɗiyya. Babbar nasara ce ga magoya bayansa.

Shekara ɗayan bayan hawan nasa ne aka fara zanga-zangar ƙin jinin Morsi a kan titunan ƙasar. Masu zanga-zangar sun zarge shi da aiwatar da manufar Musulunci, kuma sun ce ya gaza zama shugaba ga dukkan jama'ar Masar. Rundunar sojin Masar wadda ta shafe shekara 70 baya suna shisshigi a harkokin siyasa ƙasar, tana gefe guda tana kallo.

Bayan ɓarkewar zanga-zangar, ministan tsaro Abdul Fattah al-Sisi ya kifar da gwamnatin Morsi, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin farar hular da bai daɗe ba. Bayan shekara ɗaya kuma aka zaɓi al-Sisi a matsayin shugaban ƙasa kuma har yanzu yana rike da wannan muƙami.

'Gwarwaki ta ko'ina'

Hukumomi a Masar sun sha iƙirarin cewa sun yi kira ga shugabannin ƙungiyar ƴan uwa Musulmin su kawo ƙarshen abin da suka kira ''zaman dirshan da ya saɓa doka'' amma ba su ji ba. Gwamnatin tana kallon abin da ke faruwa a dandalin Rabaa al-Adawiya a matsayin wata tirjiya da ya zama wajibi a yi maganin ta.

Amr bai taɓa tunanin za a iya amfani da harsashin gaske kan masu zaman dirshan ɗin ba. Ya yi zaton ƴan sanda za su yi amfani da matakai masu sassauci kamar watsa ruwa ko hayaƙi mai sa hawaye a kansu. Ya ce ya yi mamakin irin rayukan da aka kashe saboda banbancin siyasa.

Ya tuno yadda abin ya faru, yana mai cewa "gawarwaki ne ta ko'ina". "Ba mu iya ƙirga yawansu ba. Ba mu iya taimakon juna ba."

Numfashinsa ya koma sama-sama, yayin da yake bayar da labarin abin da ya faru a ranar.

"Jerin-gwanon fararen hula ne, ciki har da mata da ƙananan yara, hannuwansu a sama suna barin dandalin zaman dirshan ɗin a daidai lokacin da aka fara harbin su da bindiga daga nesa. Na gan su da idona."

Hukumomi sun ce sun yi tanadin hanyar da mutane za su iya ficewa daga dandalin cikin ruwan sanyi kafin su tura dakarun.

Amma a cikin wani rahoto da aka wallafa shekara ɗaya bayan faruwar lamarin, ƙungiyar kare haƙƙin an Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta ce jami'an tsaro sun ''shafe tsawon ranar suna murƙushe masu zanga-zanga inda suka riƙa buɗe wuta daga manyan hanyoyi na shiga dandalin, kuma ba su bar wata hanyar tsira ba.

Masar ta ce mutane fiye da 600 aka kashe, mafi yawansu fararen hula. Sai dai kuma ƙungiyar ƴan uwa Musulmi, wadda a yanzu aka haramta ta a ƙasar ta ce an kashe mutane fiye da 1,000. Ita ma Human Rights Watch ta ce mutane 817 ne aka kashe.

Mafi yawan waɗanda aka kashen dai ƴan ƙungiyar ƴan uwa Musulmai ce, amma akwai wasu ƴan sanda da aka kashe. An ci gaba da rikici kwanaki bayan an tarwatsa su.

'Rayayyen Shahidi'

Mahaifiyar ɗaya daga cikin waɗannan ƴan sanda da aka kashe ta bayyana yadda take ji bayan mutuwar ɗanta.

Wafaa ta ce Mustafa ya fito daga rikicin ranar 14 ga watan Agusta lami lafiya. Amma kwana biyu bayan faruwar lamarin aka harbe shi har sau uku, yayin wata musayar wuta a kudancin birnin Alƙahira.

Mustafa yana da shekara 20 da wani abu lokacin da ya mutu a 2016, bayan ya yi jinyar shekara uku bai san inda kansa yake ba. A tsawon lokacin jinyarsa, Wafaa tana zaune a gefen gadonsa a cibiyar kula da masu matsanancin ciwo.

Ta ce: "Mutanen da suka san shi suna yi masa kirari da shahidin da ke raye."

Ta riƙa share hawaye a lokacin da take yi mani bayani kan babban ɗanta, wanda kuma ta fi shaƙuwa da shi.

"Muna cikin mawuyacin hali na tashin hankali, babu abin da ke mani daɗi saboda rashin sa, tamkar ba mu raye ne."

Duk bangwayen gidan suna dauke da hoton Mustafa. Wafaa tana samun sassauci ne saboda tana tare da babban jikanta, wanda aka sanya wa sunan Mustafa, kawunsa.

Tun bayan mutuwar Mustafa, iyayensa suke fama da ciwo, lamarin da suka danganta da tashin hankalin rashinsa da suke ciki.

Da na tambayi Wafaa a kan iƙirarin ƙungiyar ƴan uwa Musulmi cewa zanga-zangar lumana ce suka yi, ta bayar da amsar kai-tsaye.

"Taron maƙaryata ne," kamar yadda ta ce a cikin fushi.

Ƙungiyar Human Rights Watch ta ce kisan da aka yi a Rabaa "ba saɓa dokar ƙasa da ƙasa a kan ƴancin ɗan Adam kaɗai ya yi ba, ya kuma nuna ƙololuwar rashin mutumta ɗan Adam".

Hukumomi a Masar sun musanta duk waɗannan zarge-zarge. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce masu zanga-zangar suna ɗauke da makamai masu barazana ga doka.

"Har yanzu numfashina yana ɗaukewa a duk lokacin da na ji karar jiniyar ƴan sanda ko ƙarar jirgin sama yana yawo a sama. Nan take nake tuno abin da ya faru," inji Amr, wanda aka kama watanni kaɗan bayan zanga-zangar kuma ya shafe shekara biyar a gidan yari.

Ya ce iyalinsa sun yi fama da tashin hankali tun 2013. Ƙaninsa wanda aka yanke wa ƙafa yana tsare har yanzu inda ake zargin sa da shiga ƙungiyar ta'addanci mahaifinsa kuma, wanda ya rasu, ya sha ɗauri bisa zargin yin zanga-zanga babu izini.

Ya ce: "Ko na samu damar komawa Masar, ba za a iya dawo mani da rayuwar da nake da ita a baya ba don kuwa ta riga ta tafi".