BBC Hausa of Sunday, 11 June 2023

Source: BBC

Muna magana da Tinubu kan shiga gwamnatinsa - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya yi masa tayin muƙami a gwamnatinsa, sai dai ya ce har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba.

Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne lokacin da ya ke yi wa BBC karin bayani kan ganawar da suka yi da shugaban kasar a jiya Juma'a ta kimanin sa'a biyu.

Tattaunawar na zuwa ne adaidai lokacin da dambarwa ke sake kamari tsakanin ɓangaren sabuwar gwamnatin Kano da kuma gwamnatin APC da ta shuɗe.

Sai dai da alama tattaunawar tsakanin Kwankwaso da Tinubu na sake nuna kyakyawan alaƙa da mara-baya da NNPP ke iya samu daga bangaren gwamnatin Tarayya.

Kwakwaso dai ya ce daga cikin abubuwan da suka mayar da hankali a ganawar akwai abinda ya shafi harkokin siyasa da harkoki na gwamnati.

'Tinubu ya gamsu da rusau a Kano'

Sanatan ya ce sun tattauna a kan abubuwan da ke faruwa a Kano da shugaban kasa kuma an samu fahimtar juna a wannan rana.

A cewarsa shugaba Tinubu ya nuna gamsu wa kan matakan da gwamnatin Kano ta dauka na rushe-rushe a wasu wurare na birnin Kano.

Ya ce shugaba Tinubu ne ya soma tunkararsa da magana kuma abin mamaki yana soma yi masa bayyani, sai mamaki ya lulube shugaban kasar, bayan ya fahimci duk abubuwan da ake fadamasa babu gaskiya a ciki.

Kwankwaso ya ce ya yi wa shugaban ƙasar cikakken bayani kan filayen da gwamnatin Ganduje ta sayar wa mutane.

"Walahi duk maganganun mafi yawa, bakinsa a buɗe yake. Ya yi mamaki, bakinsa a buɗe yadda ka san…….da mamaki da tausayi tun da shi ma ya yi gwamnan nan".

Tsohon gwamnan ya ce sun dauki matakin rushe- rushen domin hana sake faruwa al'amarin irin wannan nan gaba, kuma ya na cikin alkauran da suka yi wa mutane a lokacin yaƙin neman zaɓe.

"Babu wani gwamna da za mu kyale, ba wai Ganduje kawai ba, ko wanene ya zo, ko shi Abba ne ya tafi ya sauya ra'ayi, ya sa su rika gini a masallatai da makarantu da sauransu, za mu gaya masa, mu ce ba mu yada ba".

'Tinubu na son mu yi gwamnatin haɗaka'

A kan harkan gwamnati kuma ya ce sun tattauna yadda za a iya yin aiki tare, to amma har yanzu ba su yanke shawarwari ba, sai bayan an ranstar da 'yan majalisa za su ga yadda za a yi aiki tare.

Injiniya Rabi'u Kwankwaso ya kuma jadada cewa batun tayin mukami da Tinubu ya yi masa suna kan tuntubar juna, kuma hakan ba wai yana nufin zai sauya jam'iyya ba ne, domin yana da tabbacin cewa gwamnatin hadaka Tinubu ke magana a kai.

Kwankwason ya ce nan da mako biyu za a fahimci inda suka dosa da shawarar da suka yanke.

Sannan ya mayar da martani a karshe kan kalaman Ganduje da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa da sunyi tozali da babu mamaki ya "mari Kwankwaso".

Tsohon gwamnan ya ce wannan kalamai barazana ce wanda babu wanda ya isa ya kalle idonsa da irin wadanan maganganu.