BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

'Mutuwa ce ke jiran mu idan mun koma ƙasarmu'

Hoto dga bidiyon | Hoton alama Hoto dga bidiyon | Hoton alama

A wani bidiyo mai tayar da hankali da aka ɗauka ta waya, an ji muryar wata mata da ke tsorace, an yi ta yawo da kyamarar da ke tsaye a daidai ƙofar wani sansanin 'yan gudun hijira.

A wajen sansanin, 'yan sandan Pakistan ne ke zagaye da shi, suna neman 'yan ƙasashen wajen da ba su da takardun izinin zama a ƙasar.

An kuma nuna jami'an 'yan sandan na bincikar takardun 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin.

Daga nan sai aka yanke bidiyon.

A gaba ɗaya faɗin Pakistan, ana samun ƙaruwar dirar mikiyar jami'an tsaro kan sansanonin 'yan gudun hijira domin zaƙulo mutanen da ba su da takardun izinin zama a ƙasar.

Mutanen da lamarin ya shi shafa su ne 'yan Afghanistan, waɗanda ke fuskantar ƙalubalen mayar da su gida.

Da dama daga cikinsu na fargabar komawa Afghanistan, bayan Taliban ta karɓi mulkin ƙasar a shekarar 2021.

Sun haɗar da 'yan jarida da masu rajin kare haƙƙin bil-adama, da masu rajin auren jinsi, da 'yan kwangilar da ke yi wa jami'an tsaron Amurka da na Aghanistan aiki, da mata da 'yan matan da ba sa samun damar karatu a ƙasashensu.

To amma samamen da aka kai a bidiyon da aka aika wa BBC, an kai shi ne wani yanki da 'yan ƙabilar Hazara ke zaune, mafi yawancinsu 'yan shi'a ne, kuma an zargi 'yan sunni da jimawa suna cin zarafinsu.

Mabiya waɗannan ɓangarorin addini biyu sun yi imani da abubuwa masu yawa, to amma sun bambanta a wasu ɓangarorin addini, kuma wannna bambancin ra'ayi ya raba kan al'umomin tsawon shekaru.

Saboda fargabar cin zali a Afghanistan, da yawa daga cikin 'yan ƙabilar Hazara sun yanke shawarar tsallaka kan iyaka zuwa Pakistan.

"Rayuwa a ƙarƙashin mulkin Taliban, tamkar zaman gidan yari ne, ba sa daukarmu a matsayin musulmai, suna kiranmu da kafurai. Ba ma jin nutsuwa a zama da su,'' kamar yadda Shakeba, wata matashiya 'yar ƙabilar Hazara mai shekara 17 ya shaida wa BBC.

Ta ce Pakistan a farkon shekarar 2022.

Shakeba ta ce yadda 'yan sanda suka kai samame gidan makwabciyarta, to amma dai har yanzu ba su je gidanta ba.

Tana cikin fargabar kama ta ko kama wani daga cikin danginta idan suka fita daga gidan, don haka suka shafe kusan mako uku suna ɓuya.

"Fuskokinmu daban suke. Ko da mu sanya tufafin 'yan Pakistan, da wuri ake gane mu. Suna gane mu za su fara yi mana tsawa suna cewa kai! 'yan Afghanistan! kai 'yan Afghanistan!.

Ƙabilar Hazari ta samu asali ne daga tsakiyar yankin Asiya, don haka kamaninsu sun sha bamban da na 'yan Pakistan da Afghanistan.

Kamar sauran 'yan Afghanistan da ke cikin wannan maƙala, an sauya sunan Shakebe na ainihi don kare shi.

'Yan Afghanistan sune kusan 'yan ƙasar waje miliyan 1.7 da Pakistan dta kiyasta cewa suna zaune a ƙasar ba tare da takardun izini ba.

Pakistan ta ɗauki matakin mayar da baƙin da ke zaune a ƙasar ba tare da izini ba, bayan da ake samun ƙaruwar hare-haren kan iyaka

Hare-haren da ƙasar ta ɗora alhakinsu kan 'yan tayar da ƙayar bayan Afghanistan. Iƙirarin da gwamnatin Taliban ta musanta.

Cikin watanni biyun da suka gabata, fiye da mutu 400,000 ne suka koma Afghanistan daga Pakistan.

Inda suke rayuwa ƙarƙashin halin rashin tabbas, inda wasu na zaune a sansanoni, wasu kuma sun shiga gari domin fara sabuwar rayuwa, da ɗan abin da suke samu a yayin da ake tunkarar hunturu.

Da yawa daga cikin waɗanda suka je Pakistan daga Afghanistan tun 2021, na fuskantar jinkiri wajen samun takardun izinin zama, ciki har da waɗanda suka zo a matsayin 'yan gudun hijira.

Wannan ta sa suke da zaɓi biyu bayan da aka ɓullo da sabuwar dokar, zaɓi na farko shi ne ko dai su koma Afghanistan, ko kuma su ci gaba da zama cikin fargabar jiran samamen 'yan sanda.

Amma ga Shakeba, har yanzu ba ta san matakin da za ta ɗauka ba.

"Wanna ba mataki ba ne,"in ji ta. Ita da danginta sun je Pakistan ne bayan da aka yi ta yi musu barazana kan rayuwarsu, ta ce "Na faɗa wa dangina, za mu ci gaba da zama a nan, har sai sun tilasta mana komawa gida. Amma dai Afghanistan ba wurin zaman 'yan ƙabilar Hazara ba ne, nan ne ya kamata mu zauna domin mu yi wa kanmu adu'ar samun mafita".

Fida Ali, wani ɗan ƙabilar Hazara ya ce "Haƙiƙa akwai tsanani a Pakistan, amma tsananin Afghanistan na daban ne.

Fida - wanda tsohon malamin makaranta ne - ya je Pakistan ne shekara biyu da suka wuce, jim kaɗan bayan Taliban ta karɓi mulkin ƙasar, bayan ficewar dakarun ƙetare daga ƙasar.

"A lokacin da gwamnatin da duniya ta yarda da ita ta tushe, cibiyoyi da dama da muke aiki a ƙarƙashinsu suka rushe. Dalilinmu na biyu da muke zaune a nan shi ne kasancewarmu marasa rinjaye, mu ne na farko da ake fara tsangwama."

Fargabar komawa

Ga 'yan ƙabilar Hazara, ba sa jin Pakistan a matayin wurin da suke da kariya, amma duk da haka bayan Taliban ta sake karɓar mulkin, Hazarawan sun bi ahun dubban mutanen da suka fice daga ƙasar.

"E, Hazarawa na fuskantar muzgunawa a Pakistan, amma sukan ji tamkar an kai su gidan kisa idana aka mayar da su Afghanistan,'' in ji Jalila Haider, wata lauya mai kare haƙƙin bil-adama.

'Yar ƙabilar Hazarar ta kasance tana taimaka wa mutane ta fuskar shari'a, waɗanada aka kama sanna aka yi musu barazanar mayar da su gida a makonni da suka gabata.

Ta ƙara da cewa akwai rashin amana tsakanin Hazara da 'yan Taliban saboda abu ne da ke da alaƙa da tarihi.

Shakeba ta ce wannan ne ya haifar da fargabar.

"Muna tsoron Taliban, saboda za su iya kashe mu kamar yadda suka sha yi a baya, kamar yadda ta shaida wa BBC.

A lokacin da Taliban ke kan mulki tsakanin shekarun 1996 - 2001, 'Yan ƙabilar Hazara sun yaƙe su. Inda ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Human Right Watch ta zagi Taliban da kashe da yawa daga cikin 'yan ƙabilar ta Hazara.

WRH ta kuma zargi Taliban da aikata kisan kiyashi a Mazar-i-Sharif a shekarar 1998 da Yakaolang a 2001 da Robak a Mayun 2000, inda ba su bambance tsakanin mayaƙa da fararen hula ba.

Sai dai mai magana da yawun Taliban ya ce wannan iƙirari ba gaskiya be, yana mai cewa an same mace-macen ne akamakon rigimar masu ɗauke da makamai, inda duka ɓangarorin suka yi asarar rayuka.

Kungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta ce ta tattara bayanan cin zarafin da aka yi wa 'yan ƙabilar Hazara tun lokacin da taliban ta dawo kan mulki.

Zargin da gwamnatin Taliban ɗin ta musanta. Haka kuma 'yan ƙabilar Hazara sun kasance mutanen da ƙungiyar IS ke kai wa hare-hare.

Firaminitan riƙon ƙwaryar Pakistan Anwaar-ul-Haq Kakar ya alƙawarta cewa ba za a mayar da mutanen da ke cikin hatsari Afghanistan ba.

"Akwai bayanan irin waɗannan mutane a ma'aikatar cikin gida ta karamu ,'' kamar yadda ya shaida wa kamar yaɗa labarai ta Arab News a baya-bayan nan.

To sai dai bai yi ƙaroin bayanin kan yadda suka tattara bayanan mutanen ba kuma ma'aikatar ba ta amsa tambayar da BBC ta aike mata kan hakan ba.

Haka kuma kwamishinan Pakistan da ke kula da 'yan gudun hijirar Afghanistan, Abbas Khan ya ce batun cin zarafin 'yan ƙabilar Hazara a Pakistan ba gaskiya ba ne.

Duka Hazarawan da BBC ta tattauana da su, sun nuna ɓacin ransu kan fargabar da suke da shi kan muzgunawar da ake yi musu.

Baqir, wanda a baya ya yi aiki da sojoji da kuma gwamnatin Afghanistan, na rayuwa da iyalansa.

Sun je Pakistan ne shekara biyu da suka wuce, ya kuma ce komawa Afghanistan tamkar ''wasa da rayuwarsa ne''.

"Za mu iya komawa ƙasarmu, watakila ajali ne ke jiranmu a can, kuma a nan babu wanda ke jin kukanmu, mu kam rayuwarmu na cikin gararai!''.

A yayin da suke zaune ba tare da takardun izinin zama ba, da rashin ɗaukarsu a matsayin 'yan gudun hijira, sun ce za su jira su ga abin da hali zai yi.

"Haƙiƙa ba mu san abin da za mu yi, ba mu kuma son yadda za mu yi ba,'' in ji Shakeba.

Ta kara da cewa "Mun rasa komai. Duka fatan da nake da shi a rayuwata ya gushe''.