BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

Source: BBC

Na cika wa Al Nassr alkawari duk da zawarcina da aka rika yi- Ronaldo

Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo

Kyaftin din Portugal Cristiano Ronaldo ya ce ya samu damammakin zuwa wasu manyan kungiyoyi kafin ya yanke shawarar zuwa Al Nassr.

A ranar Juma'a ne Ronaldo ya rattaba hannu da kungiyar ta Saudiyya, bayan yin baram-baram da tsohuwar kungiyarsa Manchester United.

Mai shekaru 37 din ya ce ya samu tayin zuwa kungiyoyi a Brazil, da Australiya, da Amurka da kuma kasarsa Portugal.

Sai dai a hirarsa ta farko da manema labarai yayin gabatar da shi ga magoya baya a Riyard, Ronaldo ya ce ''Na gama aikina a Turai.''

''Na ci komai, na buga wa kungiyoyi mafiya muhimmanci a Turai, yanzu kuma lokaci ne da zan fuskanci sabon kalubale a Asiya.''

Rahotanni sun ce Ronaldo zai rika karbar albashin da ba a taba karbar irinsa ba a tarihin kwallon kafa, da yawansa ya kai fam miliyan 177.

Yarjejeniyar Ronaldo da Al Nassr za ta kare ne a watan Yunin 2025.

Ya kara da cewa ya samu damammakin zuwa wasu manyan kungiyoyi amma dai ya yi wa Al Nassr alkawarin aiki da su don habaka kwallon kafa a Saudiyya.

Sau biyar Ronaldo na lashe kambun Ballon d'Or, kuma ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayan sabuwar kungiyar tasa.

Kazalika ya amsa tambayoyi daga jami'an kungiyar, sai dai bai ba da dama ga sauran yan jarida su yi masa tambaya ba.