BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

Na kasance ba zan iya amincewa da kowa ba – Yarima Harry

Yarima Harry Yarima Harry

Yariman masarautar Birtaniya, Harry ya zargi wata kafar jarida da satar tattaunawarsa ta waya a lokacin da yake ƙarami, wani abu da ya sanya shi ya ji cewa ba zai iya aminta da kowa ba.

A wata takardar shaida ta kotu kan rukunin kamfanin jaridar ‘Mirror Group Newspapers’, Harry ya ce ƴan jarida sun rinƙa bayyana shi a matsayin macuci.

Harry ya yi zargin cewa ƴan jarida sun tattara bayanai game da shi ta hanyar da ba ta dace ba, sai dai jaridar ta musanta hakan.

Harry ya zama ɗan masarautar Birtaniya mai girman muƙami na farko da ya gurfana a gaban kotu domin bayar da shaida tun bayan Edward VII a 1981.

A cikin rubutaccen bayanin da aka gabatar lokacin da ya bayyana a wata babbar kotu da ke Landan, Yarima Harry ya zargi jaridar siffanta ƴaƴan masarautar ta sigar da suka ga dama.

“Sai su rinƙa siffanta ka da ‘shirmammen yarima, ‘wanda ya gaza’, ko ‘wanda aka jefar,’ ni kuma sai suna kira na ‘dolo’, ‘macuci’, ‘ƙaramin mashayi’, ‘mai shan ƙwayoyi.’

Ya kuma zargi kafafen jarida da yunƙurin farraƙa tsakaninsa da masoyiyarsa ta hanyar bayar da labaran da ba haka suke ba.

Bugu da ƙari ya zargi gwamnatin Birtaniya da hannu cikin lamurran.

Ya ce ƴan jarida sun rinƙa satar bayanan tafiye-tafiyen tsohuwar budurwarsa a duk lokacin da ta zo ganinsa.

Bayanansa sun soki jaridu, sannan ya yi zarge-zarge a kan musamman jaridar Daily Mirror, da Sunday Mirror da kuma The People.

Ya ce zai ci gaba da fafutika har sai an kai ƙarshe