Yaya Toure ya ce sai da ya ce wa Manchester City ta ɗauko Sadio Mane daga Southampton lokacin yana ƙungiyar.
Dan wasan Senegal ɗin ya ci kwallo 21 cikin wasa 67 da ya buga a Premier a ƙungiyar Saints daga 2014-2016 gabanin Liverpool ta ɗauke shi kan kuɗi fan miliyan 43.
Sai da ya zama ɗaya daga cikin abun dogaro ga kocin Jurgen Klopp wanda ya lashe gasar zakarun Turai a 2019 kuma ya lashe gasar Premier 2019-20.
"Na so a ce na buga kwallo da shi (Mane)," in ji Toure.
Toure ya kwashe shekara takwas a City daga 2010-2018, wanda yana cikin waɗanda suka ci wa ƙungiyar gasar Premier ta farko da kuma FA.
Da yake magana a shirin Match of the Day Africa: inda ya zaɓi manyan 'yan wasan Africa 10, tsohon ɗan kwallon Ivory Coast ɗin ya ce "Lokacin da nake City yana Southampton, ina mutunta shi kwarai da gaske, na riƙa yi wa manyanmu magana a ɗauko shi amma hakan bai yiwu ba.
"Kalli yadda ya zama bayan Klopp ya ɗauke shi, ɗan wasa ne mai basira. Ina matuƙar son shi. ina son yadda yake kwallonsa.
A watan Yunin 2022 ne Mane ya koma Bayern Munich kan kuɗi fan miliyan 35.
Mane ya ci kwallo 120 cikin wasa 269 da ya yi a Anfield, ya ci manyan kyautuka shida.
Toure ya ce kyaftin ɗin Senegal ɗin "wani gagarumin misali ne" kan ƙoƙarin da yake a rayuwarsa da ta sha banban da ta kwallo.
A watan Maris 2020 Mane ya bayar da tallafin fan 41,000 ga kwamitin ƙasarsa da yake yaƙi da sutar Korona.
Ya kuma bayar da kyautar rigar Liverpool 300 ga mutanen garinsu gabanin wasan ƙarshe da ƙungiyar ta buga da REal Madrid wanda ta yi rashin nasara.
"Yadda yake tafiyar da lamuransa a nutse da taimakon da yake bai wa mutanensa da ya baro abin a yaba ne," in ji Yaya Toure.
"Wani lokacin da na ga 'yan jarida sun masa tambaya, amsar da ya basu sai da ta rikita ne, an tambaye shi, Me ya sa ba ka hawa Ferrari da sauran abubuwan ƙawa? sai ya ce 'A'a ba na buƙatar hakan, na fi son na hau mota irin wadda kowa ke hawa."