Tawagar ƙwallon kafa ta Jamus ta yi rashin nasara a wasan farko da Julian Nagelsman ya ja ragama a gida.
Turkiya ce ta je Jamus ta ci 3-2 a wasan sada zumunta da suka yi a Berlin a shirin da take na karɓar baukuncin Euro 2024.
Nagelsman ya maye gurbin Hantsi Flick a cikin Satumba, sakamakon rahin ƙoƙari da tawagar Jamus ke yi a lokacin.
Jamus ta buga wasan a Berlin a gaban 'yan kallo 70,000 da suka cika sitadiya makil
Kai Havertz ne ya fara ci wa Jamus ƙwallo, sai Turkiya ta farke ta hannun Ferdi Kadioglu, sannan Kenan Yildiz ya ƙara na biyu.
Daga baya Jamus ta farke ta hannun Niclas Fullkrug, daga baya Turkiya ta ƙara na uku ta hannun Yusuf Sari a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Ranar Talata Jamus za ta ƙara buga wani wasan sada zumunta, amma da Austria, duk dai a shirin da take na ganin ta taka rawar gani a Euro 2024.