BBC Hausa of Thursday, 13 April 2023

Source: BBC

Najeriya na bincike kan zargin biyan miliyoyin kuɗi don yi wa 'yan sanda ƙarin girma

Hukumar kula da aikin 'yan sanda a Najeriya Hukumar kula da aikin 'yan sanda a Najeriya

Hukumar kula da aikin 'yan sanda a Najeriya ta ce ta kafa kwamitin bincike don bin diddigin zargin cewa ana biyan sama da naira miliyan bakwai kafin a yi wa manyan jami'an 'yan sanda ƙarin girma.

Hukumar ta yi kira ga duk wani da ke da wata shaida kan wannan zargi, ya bayyana gaban ta, don gudanar da bincike.

Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce matakan, martani ne kan wani rahoto da wata jaridar intanet a Najeriya ta buga mai taken 'badaƙalar cin hanci ta tashi hankula a hukumar kula da aikin 'yan sanda'.

Rahoton ya yi zargin cewa sai an biya cin hancin $10,000, kimanin naira miliyan bakwai, a yi wa manyan 'yan sanda ƙarin girma a hukumar.

Ta dai yi alƙawarin ɗaukar mataki a kan duk jami'in da aka samu da hannu kan zargin karɓar cin hancin.

Kwamitin a cewar sanarwar Mista Ani, ya ƙunshi jami'an rundunar 'yan sanda da kuma na hukumar kula da aikin 'yan sanda.

Hukumar kula da aikin 'yan sanda dai ta ce hankalinta ya kai ga wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa a ranar Talata 11 ga watan Afrilun 2023.

Rahoton na da taken "Badaƙalar Cin Hanci ta Gigita Hukumar kula da Aikin 'Yan Sanda ta Najeriya inda Jami'an 'Yan sanda ke Zargin Biyan $10,000 Kafin su Samu Ƙarin Girma".

Sanarwar hukumar ta ci gaba da ruwaito labarin da cewa, wata ƙungiya ce mai ƙumbiya-ƙumbiya da ke bayyana kanta a matsayin jami'an 'yan sandan da suka fusata.

Suna dai zargin cewa ana fifita ƙananan 'yan sanda a kan manyansu ta hanyar yi musu ƙarin girma na musamman bisa zargin suna ba da cin hancin dala dubu goma.

Fusatattun 'yan sandan a cikin wata sanarwa da wani Mista Chijioke Okonkwo ya rubuta a madadin sauran takwarorinsa in ji Ani, "sun nemi fadar shugaban ƙasa ta yi bincike kan badaƙalar da ake tafkawa a rundunar 'yan sanda".

Me hukumar PSC ta ce?

Hukumar kula da aikin 'yan sanda a cikin sanarwar da ta fitar ta musanta sayar da ƙarin girma kuma ta ce tun da a baya ba ta yi ba, to kuwa ba za ta fara yanzu ba.

Ta ƙara da cewa zuwa lokacin fitar da wannan sanarwa ba ta karɓi wani ƙorafi a hukumance game da wannan zargi ba.

Hukumar ta ce ba gaskiya ba ne batun sayar da ƙarin girma a tsakanin 'yan sanda musamman a yanzu da ake ƙara ƙoƙari na sake fasalin rundunar 'yan sandan Najeriya da sake zaburas da ita.

Zargin dai na zuwa ne kwanaki ƙalilan da sabon shugaban hukumar kula da aikin 'yan sanda Mista Solomon Arase ya kama aiki.

Hukumar ta dai buƙaci duk wani jami'i da aka ɓatawa ya yi amfani da wannan dama ta kwamitin bincike da aka kafa kuma ya gabatar da ƙwaƙƙwarar shaida da za ta taimaka wajen gudanar da bincike.

Ta kuma nanata cewa duk jami''inta da aka samu da hannu a binciken da ake yi, zai fuskanci fushin doka.

Sai dai ta ce ba za ta lamunci zarge-zargen ƙarya da kuma ƙage game da irin wannan babban zargi ba