BBC Hausa of Wednesday, 6 September 2023

Source: BBC

Najeriya ta tsaya jiran hukuncin kotun zaɓen shugaban ƙasa

Hoton alama Hoton alama

Bayan kwashe kusan wata huɗu suna zaman saurare, alƙalan kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, sun shirya sanar da hukuncin da suka yanke.

Kotun wadda ta yi zamanta a Abuja, za ta sanar da hukunci uku kan ƙararrakin da wasu 'yan takara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023, suka shigar gabanta.

Atiku Abubakar, jagoran adawa a Najeriya, da Mista Peter Obi, ɗan takarar da ya zo na uku da kuma jam'iyyar APM, duka suna ja da sakamakon da ya bai wa Bola Tinubu nasara a zaɓen.

Hukunce-hukuncen da kotun ta ce za ta bayyana kai tsaye ta kafar talbijin "don inganta yin komai cikin gaskiya, ba tare da rufa-rufa ba," na da matuƙar muhimmanci ga makomar siyasar Najeriya.

A baya dai, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar a riƙa nuna zaman kotun kai tsaye a talbijin.

Har yanzu, zaɓen, ɗaya daga cikin mafiya zafi da Najeriya ta gani, kuma da aka fi fafatawa tsakanin manyan 'yan takarar uku, bai daina tayar da ƙura ba, da janyo muhawara musamman tsakanin magoya baya a shafukan sada zumunta.

Hukuncin kotun na zuwa ne daidai lokacin da Bola Tinubu yake cika kwana 100 da hawa mulki. Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) ta ce ya ci zaɓen watan Fabrairu, da yawan ƙuri'a 8,794,726.

Sai dai, manyan abokan takararsa sun ce ba su yarda ba, kowannensu na cewa shi ne ya yi nasara, don haka shi ya fi cancanta da halarcin zama shugaban Najeriya.

Magoyan bayan 'yan takaran musamman a shafin sada zumunta na X, tsohon dandalin Tuwita, suna bayyana kyakkyawan fata.

Wuƙa da nama duka yanzu, sun koma hannun alƙalan da za su raba gardama.

Tun ranar 1 ga watan Agusta, kotun mai alƙali biyar a ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani, ta yanke hukunci guda biyu, amma ta jingine su.

Sanarwar da babban magatakardan kotun, Umar Bangari ya fitar ranar Talata, ta ce sai wanda aka tantance ne kawai, za a bai wa damar kusantar ginin kotun.


Ana kallon hukuncin a matsayin jagora a jerin hukunce-hukuncen zaɓukan gwamnoni na watan Maris, waɗanda alƙalai daban-daban suka saurara a matakan jihohi, kuma nan gaba ne su ma za a sanar da sakamakon ƙararrakin.

Ba shakka, lokaci ne mai cike da zulumi da zaman ɗar-ɗar aƙalla ga 'yan siyasa da magoya bayansu.

Hukumomi sun ce sun ɗauki matakai don tabbatar da doka da oda a lokacin sanar da hukuncin da kuma bayan hakan. 'Yan sanda sun ce sun ƙara tura jami'ansu sassan Najeriya don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Cikin amo mai ƙarfi, rundunar 'yan sanda ta ja hankalin waɗanda ta kira 'yan jamhuru da jiga-jigan siyasa, a kan su yi hattara wajen furta kalamai da ayyukansu, don kuwa ba za ta lamunci iza wutar tarzoma ko abin da zai jefa ƙasar cikin zaman kara zube ba.

Masharhanta na cewa ba a taɓa soke zaɓen shugaban ƙasa a tarihin Najeriya ba, tun bayan komawar ƙasar tafarkin dimokraɗiyya a 1999.

Sai dai, ga alama hakan ba shi da wani tasiri a dimokraɗiyya da ke ƙara ƙarfi da haɓaka kamar ta Najeriya. A 2015, Muhammadu Buhari ya kafa tarihi irinsa na farko a ƙasar, inda ya kayar da shugaban ƙasa mai ci, Goodluck Jonathan.

Yayin sauraron shari'ar, masu ƙorafe-ƙorafen sun yi iƙirarin cewa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, ba su cancanci tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar ba.

Haka zalika sun kafa hujjar cewa Tinubu ya gaza samun kashi 25 na ƙuri'un da aka kaɗa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Sun kuma yi zargin cewa, takardun karatun da ya gabatar wa INEC, na jabu ne da sauran zarge-zarge.

Lauyoyin Tinubu dai, sun sa ƙafa sun shure zarge-zargen, kuma suka ce dukkansu ba gaskiya ba ne.

Sun kuma nemi kotun kada ta amince da ƙorafe-ƙorafen, sannan ta yi watsi da su. Sun ce ɗan takarar na jam'iyyar APC shi ne ya lashe zaɓen, kuma hukumar zaɓe ta INEC ta yi daidai bisa tanadin tsarin mulki, da ta ayyana shi matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Wasu 'yan Najeriya kamar Dr Hafsatu Daladi, da ke tsokaci a shafin X game da hukuncin da kotun za ta sanar, na kira ga ɓangaren shari'ar ƙasar ya sanya muradin kare tsarin mulkin Najeriya a gaba da komai.


Akwai damar ɗaukaka ƙara

Masana shari'a a ƙasar kamar fitaccen lauyan Najeriyar nan, Femi Falana mai lambar SAN na cewa yankan baya da razanarwar da ake yi wa ɓangaren shari'a irin wanda ba a taɓa gani ba game da hukuncin kotu, abu ne da ba shi da wata ma'ana.

Ya ce duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, to yana da damar ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙolin Najeriya.

Yayin hira da gidan talbijin na Channels TV, Femi Falana ya ce ya damu a kan yadda mutane suke nuna cewa komai ya ƙare a sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.

A cewarsa, hakan ba gaskiya ba ne.

Duk ɓangaren da bai yi nasara ba, kuma ya ji bai gamsu da hukuncin ba, to yana da damar garzaya wa gaban Kotun Ƙoli.