Napoli won their first Serie A title for 33 years as they drew with Udinese at Dacia Arena to spark jubilant celebrations back in Naples.
A karon farko cikin sama da shekara 30 Napoli ta lashe gasar Serie A.
Napoli ta samu wannan nasarar ne bayan kunnen doki da ta yi da Udinese a filin wasa na Dacia Arena. Kuma daga nan ƙungiyar ta fara murnar nasarar tata.
A 1990 ne ƙungiyar ta ci kofin na ƙarshe lokacin Diego Maradona yana buga mata, kuma ta ci kofin shekara uku kafin wannan.
Victor Osimhen ne ya farke kwallon da aka ci Napoli, ya ci kwallon ne a minti na 52 bayan Sandi Lovric ya ci wa Udinese kwallonta da ka.
Dama maki ɗaya Napoli ke nema ta ci gasar Serie A karo na uku a tarihi, yayin da ya rage wasanni biyar a kammala gasar.
“ Ganin yadda magoya bayan ƙungiyar ke murna ya ishe ka fahimtar irin farin cikin da suke ciki,” in ji kocin ƙungiyar Luciano Spalleti.
“Suna kallon wannan yanayin a matsayin mai matukar tsauri, to suna da dukkan dalilin na su yi farin ciki kan wannan nasarar.
“Za ka ji sanyi a ranka ganin cewa ka ba su damar yin farin ciki.”
Napoli ta kawo ƙarshen haushin shekaru 30
Napoli ta ci kofinanta biyu na ƙarshe ne lokacin da Maradona yake buga mata a 1987 da 1990 – wanda a yanzu suka sanya wa filin wasansu sunan shi.
Bayan waɗannan lokuta masu daɗi ƙungiyar ta faɗa cikin matsalar kuɗi, ta koma matakin Serie C a nan baya-bayan nan 2006.
Sun ci Coppa Italiya sau uku cikin kaka 11amma ba wannan ne kwaɗayin magoya bayan Napoli ba.
Yanzu sun samu wani sabon taurarin, Victor Osimhen ɗan wasan Najeriya, ya ci kwallo 21 cikin wasa 26 da kakar bana.
Sai kuma Khvicha Kvaratskhelia wanda ya ci kwallo 12 ya kuma taimaka aka ci kwallo 10.
Amma a ɓangaren kocin ƙungiyar Luciano Spelletti, wanda ya ci Coppa Italiya sau biyu tare da Roma, ya zama shi ne koci mai fi shekaru da ya taɓa lashe Serie A.
Tun makon jiya Napoli ta samu damar lashe kofin gabanin wasa shida da suka yi ragoa, sai dai sun kasa ko canjaras da abokan hamayyarsu ta cikin gida Salernitana.
Amma yanzu sun samu nasarar ɗaukar kofin bayan da suka bai wa Lazio da ke mataki na biyu maki 16.
Kwallon da Osimhen ya farke ta janyo sowa
Wasansu da Udinese kamar tsararre ne. Magoya bayan Napoli sun shirya shagali a filin wasansu da ake kira Diego Armando Maradona, da yawa ba sun sun kalli wasan ne ta majigi.
Sama da mutum 10,000 ne suka bi ƙungiyar yankin arewaci, sai dai an rufe musu baki ne a minti na 13 lokacin da Lovris ya jefa musu kwallo guda a raga.
A minti 45 ɗin farko Napoli ta yi ta fama, amma bayan an dawo hutun rabin lokaci sai Osimhen ya farke mata wanda hakan ya bai wa magoya bayansu sabon kwarin gwiwa.
Bayan farkewar, Napoli ta ci gaba da jan ragamar wasan har zuwa ƙarshen wasa.
Ana busa usur ɗin ƙarshe magoya baya suka fantsama cikin fili suka fara murna tare da magoya bayan Udinese din baki ɗaya.