BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Newcastle ta ɗauki Harvey Barnes daga Leicester City

Harvey Barnes (left) Harvey Barnes (left)

Newcastle United ta ɗauki ɗan kwallon tawagar Ingila, Harvey Barnes daga Leicester City kan fam miliyan 38.

Mai shekara 25, wanda ya buga wa Ingila wasa ɗaya ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar.

Shi ne na uku da Newcastle ta ɗauka a bana, bayan Yankuba Minteh da ɗan kwallon tawagar Italiya, Sandro Tonali.

Newcastle ta karkare a mataki na huɗu a teburin Premier League kakar da ta wuce, wadda za ta buga Champions League a kakar 2023-24 kuma a karon farko tun bayan 2003-04.

Barnes shi ne na baya-bayan nan da ya bar Leicester City, wadda ta faɗi daga Premier League za ta buga Championship a bana.

Ya buga wa Leicester City wasa 146 a Premier League da cin kwallo 35 da bayar da 25 aka zura a raga.

Ɗan wasan ya ci kwallo 13 a kakar 2022/23, hakan bai hana Leicester faɗuwa daga babbar gasar tamaula ta Ingila ba.

Cikin waɗanda suka bar Leicester kawo yanzu sun haɗa da James Maddison zuwa Tottenham kan fam miliyan 40 da Youri Tielemans da ya koma Aston Villa da kuma Caglar Soyuncu da ya koma Atletico Madrid.