Kocin Roma Jose Mourinho ya kamanta dan wasan gaban Napoli Victor Osimhen da Didier Drogba, inda ya kara da cewa ''zan iya sayen sa da ace ina aiki da kungiyar da ke da kudi sosai.''
Sai dai kuma ya gargadi dan wasan gaban na Najeriya kan zuwa gasar Premier League a irin salon wasa da yake yi.
Mourinho na magana ne a taron manema labarai, bayan kammala wasansu da Napoli, wanda suka yi rashin nasara 2-1 a filin Maradona da ke Naples.
''Osimhen kamar Drogba yake, amma Didier baya faduwa dagangan'', in ji Mourinho.
Ya kara da cewa '' na fada mashi cewa ya ci kwallo mai kyau kuma akwai bukatar ya daina faduwa dagangan''.
''Kwallon da ya ci ta kayatar, ya taba cin irinta a farko haduwar mu a wannan kaka, saboda haka dan wasa ne mai kyau. Sai dai dole ya daina faduwa dagangan'', in ji Mourinho.
Napoli ce ke jan teburin Serie A da maki 53 a wasanni 20, kuma sau daya aka doke ta ta kuma yi canjaras biyu.
Kazalika ta bai wa Inter Milan da ke binta maki 13 wadda ke da maki 40, sai Lazio da Atalanta da AC Milan masu maki 38 kowannen su.