BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

PSG ta dakatar da Messi saboda ya je Saudia Arabia ba tare da izini ba

Lionel Messi Lionel Messi

Paris St Germain ta dakatar da Lionel Messi mako biyu, bayan da ya je Saudi Arabia ba tare da izinin ba.

Messi ba zai yi atisaye a PSG ba a tsawon hukuncin dakatarwar da aka yi masa.

An fahimci cewar kyaftin din Argentina, mai shekara 35, ya nemi izinin yin tafiyar domin kulla yarjejeniyar tallace-tallace ta kashin kansa, amma ba a amince ba.

Messi yana yi wa Saudi Arabia aikin jakadan hukumar yawon bude ido ta kasar.

Wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022, tsohon dan wasan Barcelona, kwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan a PSG.

Mataimakin Barcelona, Rafael Yuste ya sanar a cikin watan Maris cewar sun tuntubi Messi kan batun ya koma Camp Nou da murza leda.

Messi ya ci kwallo 31 ya kuma bayar da 34 aka zura a raga a fafatawa 71 a dukkan karawar da ya yi wa PSG da lashe Ligue 1 a kakar da ta wuce.

Messi ba zaii buga karawa da Troyes da kuma Ajaccio ba, bayan da PSG ta bayar da tazarar maki biyar a teburi, saura wasa biyar a karkare gasar bana.

PSG na fatan lashe Ligue 1 na tara daga kaka 11 baya.

Lionel Messi ya dauki hukunci a hannunsa, wanda wasu ke ganin ya gama taka leda a PSG.

Dama kuma magoya bayan kungiyar ba sa kaunar Messi, kenan da kyar idan PSG za ta tsawaita yarjejeniyarsa.