BBC Hausa of Wednesday, 6 December 2023

Source: BBC

Pope golan Newcastle zai yi jinyar wata hutu

Golan tawagar Ingila da Newcastle United, Nick Pope Golan tawagar Ingila da Newcastle United, Nick Pope

Golan tawagar Ingila da Newcastle United, Nick Pope za a yi masa aiki a allon kafada, wanda ake cewar zai yi jinyar wata hudu.

Mai shekara 31 ya ji rauni a lokacin da ya yi tsalle ya cire kwallon da ya nufi raga a wasan da Newcastle ta ci Manchester United 1-0 ranar Asabar.

Hakan ya sa aka sauya shi da golan Slovakia, Martin Dubravka a minti na 86, bayan da jikinsa ya yi tsami a wasan Premier League a St James Park.

Pope, wanda ya koma St James Park da taka leda a Junin 2022, ya bi sawun masu jinya a kungiyar da ya hada da Callum Wilson da Harvey Barnes da Jacob Murphy da Joe Willock da Sven Botman da kuma Dan Burn.

Tsohon golan Burnley, ya buga wa Newcastle dukkan wasannin Premier League da na Champions League a kakar nan.

Raunin da ya ji ya sa ana ta rade-radin cewar Newcastle za ta dauko David de Gea a watan Janairu, domin maye gurbin Pope.

A kakar nan Pope ya hana kwallo ya shiga ragarsa a Premier League a karawa biyar - kamar yadda golan Crystal Palace, Sam Johnston da na Manchester United, Andre Onana suke da wannan kwazon.

Wannan raunin zai zama koma baya ga Pope da tawagar Ingila a shirin shiga gasar nahiyar Turai Euro 2024 a Jamus.

Za a fara Euro 2024 a cikin watan Yuni zuwa Yulin 2024