Boris Johnson ya ce Putin ya yi masa barazana da harin makami mai linzami a wani kiran waya na ba-zata da suka yi gabanin Rasha ta mamayi Ukraine.
Boris wanda yake firaminista a wancan lokaci, ya ce mista Putin ya faɗa masa cewa harin makami mai linzamin ba zai wuce ƙasa da minti ɗaya ba.
Mista Johnson ya ce Putin ya yi kalaman ne bayan da ya gargade shi cewa ƴaƙin zai iya zama “babban bala’i”, a wata tattaunawa ta waya mai tsawo da suka yi a watan Febrairun 2022.
An bayyana yadda tattaunawarsu ta kaya ne a wani shiri na musamman na BBC, da ke duba tattaunawar mista Putin da shugabannin duniya.
Mista Johnson ya gargaɗi Putin cewa mamaye Ukraine zai janyo ƙasashen yamma su ƙaƙaba wa Rashan takunkumi da kuma ƙara yawan dakarun Nato a iyakokin ƙasar.
Ya kuma yi ƙoƙarin hana matakan sojin Rasha ta hanyar faɗa wa Putin cewa Ukraine ba za ta shiga Nato ba a nan gaba.
Sai dai mista Johnson ya ce “ya yi mini barazana da cewa Boris ba na son in ɓata maka, amma ta hanyar amfani da makami mai linzami, ba zai fi minti ɗaya ko wani abu makamancinsa ba.
"Amma a tunanina kawai yana wasa da yunkuri da nake yi na ganin ya yarda an yi tattaunawar sulhu.”
Shugaba Putin ya kasance “sananne” lokacin kiran “wayar da ba a saba ganin irin ta ba”, a cewar mista Johnson.
Da wuya a iya gane cewa ko barazanar mista Putin ta gaske ne.
Duk da haka, idan aka yi la'akari da hare-haren da Rasha ta kai kan Birtaniya a baya-bayan nan a birnin Salisbury a 2018 - duk wata barazana daga shugaban na Rasha, duk da haka, mai yiwuwa mista Johnson ba shi da wani zaɓi illa ya ɗauki hakan da gaske.
Kwana tara bayan nan, a ranar 11 ga watan Fabrairu, sakataren tsaro Ben Wallace ya tashi zuwa Moscow domin ganawa da takwaransa na Rasha, Sergei Shoigu.
Shiri na musamman na BBC na Putin da ƙasashen yamma, ya gano cewa mista Wallace ya bar Moscow da tabbacin cewa Rasha ba za ta mamayi Ukraine ba, sai dai, ya ce dukkan bangarorin sun san hakan karya ne.
Ya kwatanta hakan da wani abu mai kama da cin zarafi, da ke nuna cewa: zan maka karya, ka san karya nake yi kuma na san ka san cewa karya nake yi sannan zan kuma yi maka karya.
"Ina tunanin hakan na nufin cewa ina da karfin iko,’’ in ji mista Wallace.
Ya ce karyar da suka yi, ya nuna masa cewa Rasha za ta mamayi Ukraine.
Bayan barin wajen tattaunawar, ya ce shugaban sojin Rasha, Janar Valery Gerasimov, ya faɗa masa cewa “ba za a ƙara musguna mana ba”.
Ƙasa da makonni biyu bayan nan, a daidai kuma lokacin da tankokin ƴaƙi ke ƙoƙarin shiga iyakoki a ranar 24 ga watan Febrairu, mista Johnson ya samu kiran waya da tsakar dare daga Shugaba Zelensky.
"Zelensky mutum ne da ba shi da matsala," in ji mista Johnson. "Sai dai, ya faɗa min cewa, ka sani, za su far wa ko’ina."
Mista Johnson ya ce ya buƙaci ya taimaka wa shugaban domin ya tsira.
"Bai amince da buƙatar taimako da na yi masa ba, inda ya yanke shawarar tsayawa a wajen da yake a wani abu mai kama da jarumta."