BBC Hausa of Monday, 24 July 2023

Source: BBC

'Raba wa talakawa kuɗi don rage radadin cire tallafin mai ba shi ne mafita ba'

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya soki tsarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi na raba wa ƴan Najeriya tallafin rage radadin cire tallafin mai.

Ita dai gwamnatin ta ce za ta raba wa ƴan kasar miliyan goma sha biyu ne, daga cikin su sama da miliyan 200, Naira dubu dari takwas har tsawon watanni shida.

Sai dai a cewar gwamnan na Kaduna, babu fa'ida a wannan al'amari domin ba zai taimaka kamar yadda ita gwamnatin ke fata ba.

Ya ce ''Abin da muka gano shi ne mu a nan Arewa, kashi 75 cikin 100 na al'ummarmu ba su da asusun ajiya, idan kuma mutum bai da asusun ajiya a banki ta yaya wannan tallafi zai same shi?''

Gwamna Uba Sani, ya ce shi ya sa duk lokacin da aka yi maganar bayar da tallafi a Najeriya sai ka ga ƴan Kudu ne ke amfana, domin yawancinsu, na da bankunan ajiya, da kuma sani kan yadda za su ci gajiyar tsarin.

''Kuma yanzu idan aka ce za a raba wannan kudi da ake magana sama da dala miliyan 800 da za a karbo daga wajen Bankin Duniya, ina tabbatar maka da cewa daga karshe yan Arewa ba za su ci gajiyar ko kashi goma ba'' in ji shi.

Ya ce a kokarin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsari, za ta fara shiga yankunan karkara domin tabbatar da bude wa jama'a asusun banki, don samun saukin tafiyar da harkokinsu.

A halin da ake ciki a iya cewa cire tallafin man fetur din da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar ya jefa ƴan kasar da dama cikin tasku, la'akari da yadda farashin komai ya tashi, kama daga kan sufuri, kayan abinci, da sauran bukatun yau da kullum.

A yawancin jihohin kasar dai maganar da ake ana sayar da litar man fetur sama da Naira dari shida, sakamakon kari na biyu na baya-bayan nan da aka yi.

Sai dai gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin cewa tsarin da ta bullo da shi na raba wa mutum miliyan 12 Naira dubu takwas zai taimaka wajen rage wa jama'a radadin taskun da suka shiga.

Masu suka dai na ganin cewa duk da cire tallafin ya zama dole a halin da ake ciki, gwamnatin ba ta yi kyakkyawan tsari na yadda za a aiwatar da shi ba.