Barcelona za ta ziyarci Elche ranar Asabar, domin buga karawar mako na 27 a gasar La Liga.
Kungiyar Camp Nou ta yi wasa 20 a dukkan karawa tu bayan kammala gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, wanda Argentina ta lashe.
Cikin wasannin Raphinha ne kadai ya buga dukkan fafatawa 20 a Barcelona tun daga bayan wasannin Qatar.
Dan kwallon tawagar Brazil na taka rawar gani da Xavi ke amfani da shi a fafatawar da yake fuskanta a kakar nan.
To sai dai Raphinha ba zai yi wasa da Elche ba, sakamakon katin gargadi biyar da ya karba, zai yi hutun karawa daya kenan.
Kawo yanzu a kakar nan, wasa biyu ne dan kwallon Brazil, bai yi wa Barcelona ba, sune tun kafin fara gasar kofin duniya.
Bai yi wasan farko a Champions League ba a fafatawa da Viktoria Pilsen a bana da kuma na La Liga da Athletic Club a Camp Nou.
Kafin fara wasannin kofin duniya an yi fafatawa 20 - kawo yanzu Raphinha ya ci kwallo tara a kakar nan ya kuma bayar da tara aka zura a raga.
Dan kwallon na kara samun kwarewa kan taka leda, wanda ya yi wa Brazil wasanni a Qatar.
Raphinha, wanda ya koma Barca daga Leeds ya ci kwallaye masu mahimmaci a kungiyar Sifaniya a bana, ciki har da wadda ya zura a ragar Osasuna da Valencia da Athletic Club a La Liga.
Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da maki 68, sai Real Madrid ta biyu mai maki 56.