BBC Hausa of Tuesday, 21 February 2023

Source: BBC

Raunin shugabancin Buhari ya sake fitowa fili - El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, da ke arewacin Najeriya, Mallam Nasiru El-Rufai Gwamnan jihar Kaduna, da ke arewacin Najeriya, Mallam Nasiru El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, da ke arewacin Najeriya, Mallam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa dambarwar da suke yi da ɓangaren shugaban ƙasar a kan maganar daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi ta ƙara fito da raunin da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari yake da shi a fannin jagoranci.

Gwamnan ya sake nanata zargin da yake yi cewa wasu muƙarraban shugaban kasar ne suke ingiza shugaban, yake ƙara turjiya a kan batun canjin kuɗin domin su kada jam`iyyar APC a zabe.

A tattaunawarsa da BBC, Gwamna El-Rufai ya ce yana da yaƙinin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam`iyyarsu, APC, Bola Tinubu zai ci zaɓe.

Kuma da zarar ya samu nasara za su fallasa mutanen da ke musu makirci.

Gwamnan ya yi bayani a kan yadda suka cimma matsaya a taron da gwamnonin APC suka yi da shugabannin jam`iyyar cewa ya kamata kowa ya martaba hukuncin kotun ƙolin Najeriyar.

Sakamakon taronsu na ƙungiyar gwamnonin APC, gwamnan ya shaida wa BBC cewa, sun tsaya sun duba wannan tsarin da aka ɓullo da shi na canjin kuɗi da masifar da abin ya haifar wa al'umma da kuma ƙiyayya da ya ce an sa al'umma suka fara ji don su ɗora wa jam'iyyarsu ta APC.

''Kuma waɗanda suka fito da wannan tsari sun yi ne domin a kada jam'iyyarmu a zaɓe, '' in ji shi.

El-Rufain ya ce a taron da suka yi na gwamnonin sun yarda cewa kamata a bi abin da Kotun Ƙoli ta ce, a ci gaba da amfani da tsoffin da sababbin kuɗin sai an gama shari'a.

Game da yadda jam'iyyarsu ta bi ra'ayinsu kan batun, da cewa ko su gwamnonin sun tanƙwara shugabanta ne.

Gwamnan ya mayar da martani da cewa, shugaban jam'iyyarsu dattijo ne wanda ya ma haifi wasu daga cikinsu gwamnonin.

"To ta yaya za mu iya tanƙwara shi, ba wanda bai yi tir da wannan tsari ba, yadda ya sa mutan cikin wahala.''

''Akwai ma wasu shugabanni biyar da ba su goyi baya ba,'' in ji gwamman na Kaduna.

''Mu abin da ya dame mu a kan wannan ba maganar zaɓe ba ne domin mun san ayyukan da muka yi wa al'umma ya isa su zaɓi APC,'' a cewarsa.

Dangane da maganar cewa Shugaba Buhari ya kafa hujjar cewa wannan batu na sauya kuɗi zai taimaka wajen magance saye ƙuri'a.

Kuma su gwamnonin APC suna adawa da shirin, ko hakan ya nuna ke nan suna shirin sayen ƙuria ne?

Gwamman ya ce ba zai ce wasu ba su da niyyar sayen ƙuri'a ba amma su dai a jihar Kaduna ba su taɓa sayen ƙuri'a ba, ayyukan da suka yi wa al'umma su suke sa a zaɓe su.

''Kuma ba mu da wani haufi a zaɓe mai zuwa in Allah Ya yarda Asiwaju zai ci Kaduna,'' in ji shi. Kuma sauran 'yan takararsu duka za su ci zaɓe a cewarsa.

Da ya koma kan batun sayen ƙuri'a ya ce '' to yau aka ma fara sayen ƙuri'a ne?''

''Me ya sa ba a canza kuɗin a da ba. Da Naira kawai ake yi?''

''Za a iya bai wa mutane dala ko yuro ko CFA za a iya bai wa mutane abinci, akwai hanyoyin siyan ƙuri'a da yawa ba za ka iya cire kuɗi daga siyasa ba sai dai ka rage,'' in ji shi.

Gwamman na Kaduna ya ce ba wai sun tashi tseye ba ne a kan lamarin don zaɓe ba. '' Zaɓe Allah Ya riga Ya zaɓi shugaban ƙasa.''

ya ce abin ya dame su ne saboda wahalar da jama'a suka shiga kawai.

Abin da ya sa kansu ya rabu a jam'iyya ɗaya

Gwamnan na Kaduna ya ce dama su waɗanda ba sa adawa da shirin canjin kuɗin, ba 'yan jam'iyya ba ne, 'yan a ci bulus ne.

''Ka ga Godwin Emefiele daman PDP ta kawo shi sauran waɗanda ake ƙulle-ƙulle da su mun sansu idan lokaci ya yi za mu faɗi sunansu daman ba 'yan jamiyya ba ne 'yan ci bulusu ne,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa,'' da mun kada su za mu bayyana sunansu.''

Ya ce,''mutane ne da suke son durƙusar da jam'iyyar da ta ba su dama suka sami kuɗi na fiye da na cefane don wasaunsu mun sansu cefane yana musu wahala shekara takwas da ta wuce amma yanzu suna da kuɗi na fitar hankali.''

El-Rufai ya yi barazanar cewa sai sun bincike yadda suka samu kuɗin'' za mu tambaye su wallahi sai mun fito da su mun faɗi sunayensu mu ce inda suka samesu.''

A kan abin da ya sa ba sa sukar shugaban ƙasar sai wasu na gefe a kan tsare-tsaren da shi yake ɓullo da su waɗanda suke gani na kassara ƙasar.

Nasir El-Rufai, ya ce, '' shi shugaban ƙasa mutum ne mai yarda da mutane kuma an riga an ɓata mu an ce gwamnoni ɓarayi ne shi ya sa ba sa son wannan tsari''.

''Ko mun je mun yi masa bayani mun ce mai gida an maka ƙarya a nan in ya ce ya gane zai ɗauki mataki muna barin wurin za a zo a ce wallahi kar ka ɗauka.''

Dangane da hakan ne gwamnan ya ce Shugaba Buhari a matsayinsa na ɗan-Adam kamar kowa tara yake bai cika goma ba.

''A wannan muna da yaƙinin cewa shugaba ya yi kuskure,'' in ji shi domin yana da rauni.