BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023

Source: BBC

Real Madrid ta bai wa Joselu riga mai lamba 14

Joselu Joselu

Real Madrid ta gabatar da sabon dan wasan da ta dauka aro Joselu ranar Talata a filin Alfredo Di Stefano.

Tuni kuma ta bai wa dan wasan riga mai lamba 14 da zai yi amfani da ita zuwa karshen kakar bana.

Fitattun 'yan wasan da suka sa riga mai lamba 14 a Real Madrid sun hada da Xabi Alonso da Guti da Luis Milla da Javier Hernández da kuma Casemiro.

Real Madrid ta ɗauki aron Joselu daga Espanyol da yarjejeniyar za ta saye shi matuƙar ya taka rawar gani.

Joselu, mai shekara 33, shi ne na uku a yawan cin ƙwallaye a La Ligar da aka kammala.

Ya jefa ƙwallo 16 a raga, amma duk da haka ƙungiyarsa ta faɗi daga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Tsohon ɗan wasan kulob ɗin Stoke City da Newcastle United, ya ci wa Sifaniya ƙwallo a Gasar Nations League da ƙasar ta lashe kofin ranar Lahadi a Netherlands.

Real ta ɗauki ɗan wasan ne, bayan Karim Benzema ya bar Santiago Bernabeu a ƙarshen kakar nan zuwa Al-Ittihad ta Saudiyya.

Kenan Real tana neman wanda zai maye gurbin gwarzon ɗan wasan wanda ya ci Ballon d'Or ta bana, inda ya zama na biyu a yawan ci wa ƙungiyar ƙwallaye a tarihi, bayan Cristiano Ronaldo.

Ana kuma alaƙanta ɗan wasan tawagar Ingila da Tottenham, Harry Kane a matakin wanda zai maye gurbin Benzema a Real Madrid.