Real Mallorca da Barcelona sun tashi 2-2 a wasan mako na bakwai a gasar La Liga da suka fafata ranar Talata.
Mai masaukin baki ce ta fara cin kwallo ta hanun Vedat Muriqi a minti na takwas da fara wasa, saura minti hudu su je hutu Barcelona ta farke ta hannun Raphinha.
Sai dai Abdon ya ci wa Mallorca na biyu, amma kuma Barca ta kara farkewa.
Barcelona, wadda ta fara tashi 0-0 a gidan Getafe da fara kakar bana ta ci wasa biyar a jere da hada maki 16 daga fafatawa shida kafin ranar ta Talata.
Yanzu ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da maki 17.
Barcelona za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan mako na takwas a La Liga ranar Juma'a 29 ga watan Satumba.
Daga nan za ta je gidan Porto, domin buga wasa na biyu a cikin rukunin farko a Champions League da za su fafata ranar Laraba 4 ga watan Oktoban 2023.
Za a ci gaba da wasannin mako na bakwai ranar Laraba:
- Athletic Bilbao da Getafe
- Real Madrid da Las Palmas
- Villarreal da Girona
- Valencia da Real Sociedad
- Cadiz da Rayo Vallecano