BBC Hausa of Saturday, 15 May 2021

Source: BBC

Rikicin Isra'ila da Falasdinawa: Mece ce garkuwar makaman roka ta Isra'ila?

Na'urar garkuwa Iron Dome na tare rokan Hamas da Falasdinawa, inji Isra'ila Na'urar garkuwa Iron Dome na tare rokan Hamas da Falasdinawa, inji Isra'ila

A rikicin bayan-bayan nan tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, sojojin Isra'ila sun ce kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa masu rike da makamai sun kaddamar da harin makaman roka fiye da 1,500 zuwa Isra'ila.

Amma na'urar garkuwa daga makaman roka ta Isra'ila da aka fi sani da Iron Dome, ta kakkabo akasarin wadannan makaman rokar.

Mahukuntan kasar Isra'ila sun ce na'urar na da nasarorin aiki na kashi 90 bisa dari wajen lalata makaman roka a tsakiyar sararin samaniya kafin su kai ga fadawa kan yankunan birane masu yawan al'umma na Isra'ila.

Yaya garkuwar makaman roka take aiki?

Na'urar Iron Dome bangare ne na jerin tsarin na'urorin kariya da ke aiki a kasar Isra'ila, da aka kashe biliyoyin daloli a kai.

Na'urar na amfani da na'urorin hangen nesa wajen bin diddigin makaman roka masu tahowa, daga nan sai su harba makamai masu linzami da za su tarwatsa su.

Fasahar na banbancewa tsakanin makamai masu linzami da ka iya fadawa kan yankunan da jama'a suka taru da kuma wadanda suka kuskure hanyarsu.

Wadanda suka doshi yankunan birane ne kawai ake harbowa, da hakan ya sa na'urar ke da tsadar gaske.

Ko wane reshen na'urar da k tarwatsawar na cin kimanin dala 150,000, kamar yadda jaridar Times ta Isra'ila ta bayyana.

Ta yaya aka kirkiro ta?

Na'urar Iron Dome na da tushen ta a lokacin rikicin shekarar 2006 da Isra'ila ta fafata da mayakan Hezbollah, masu tsattsauran ra'ayyin addinin Islama da ke da mazauni a kudancin kasar Lebanon.

Hezbollah ta kaddamar da dubban makaman roka, da ya haddasa mummunar barna tare da hallaka gwamman 'yan kasar Isra'ila.

Bayan shekara guda, Isra'ila ta sanar da kamfanin samar da tsaro na kasa da ake kira Rafael Advanced Defense Systems, da zai kirkiri sabuwar na'urar kariya.

Aikin ya samu tallafin kudi da yawa na dala biliyan 2000 daga Amurka.

Bayan shafe shekaru ana gudanar da bincike, an yi gwajin na'urar a wani artabu a karon farko cikin shekarar 2011, lokacin da ta tarwatsa makamin kare dangi da aka harba a kudancin birnin Beersheba.

Shin tana da aibu?

Likitocin Isra'ila sun ce makaman rokar da aka harba daga Gaza sun hallaka akalla mutane bakwai da suka hada da kananan yara biyu.

Yanzu haka adadin wadanda suka mutu a Gaza daga hare-hare ta saman a Isra'ila ya kai mutane 83, akalla 17 daga cikin su kananan yara ne, kamar yadda hukumomin kiwon lafiya na Palasdinu suka bayyana.

Ko shakka babu na'urar Iron Dome ta samar da kariya da 'yan kasar Isra'ila da dama daga hare-haren da ka iya haddasa mace-mace.

Wakilin BBC mai yin sharhi kan harkokin kasashen waje Jonathan Marcus ya bayar da rahoton cewa da alamu batirin na'urar da ke kare birnin Ashkelon ya mutu saboda tangarda lokacin barkewar rikici tsakanin Isra'ila da mayaka masu gwagwarmaya da makamai na Gaza.

Masu suka sun bayyana cewa nasarar kasha 90 bisa dari wajen kakkabe makaman rokar daka harbo daga Gaza ka zama matsala idan aka fuskanci wasu abokan gabar na daban a nan gaba.

Yonah Jeremy Bob, wani edita kan harkokin liken asiri na jaridar The Jerusalem Post y ace mayakan Hezbollah na da karfin kaddamar da karin makamai masu linzami a cikin kankanen lokaci, da ka iya zama da wahala wa na'urar Iron Dome ta iya kakkabe su duka.

'Yan kasar Isra'ila da suka samu kan su cikin tsakiyar rikici a baya bayan nan nuna jin dadin su ga na'urar ta Iron Dome kan ceton rayuka.

Amma kuma Dr Yoav Fromer, masani kan al'amuran kimiyyar siyasa daga Jami'ar birnin Tel Aviv ya ce, dogaro da kariyar na'urar ya sa Isra'ila neman hanyoyin warware matsalar rikicin na tsawon lokaci a siysance.

"Abin dubawa a nan shi ne, kyawawan nasarorin na'urar Iron Dome sun taka rawa wajen gazawa a manufofin kasashen waje, wanda ya kara rurwa wutar rikicin da farkon fari,'' ya shaida wa BBC.

"Bayan shekaru da dama, mun sake fadawa tarkon maimaicin abu day ana wanzuwar tashe-tashen hankula.''