BBC Hausa of Tuesday, 2 May 2023

Source: BBC

Rikicin Sudan zai fitar da mutum sama da dubu 800 daga ƙasar - MDD

Tutar Sudan Tutar Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane sama da dubu dari takwas ka iya tserewa daga Sudan sakamon kazamin fadan da ake yi tsakanin bangarorin soji biyu da ke gaba da juna.

Ana ci gaba da gwabza fada a babban birnin kasar Khartoum duk da alkawarin dakatar da bude wuta tsakanin bangarorin biyu.

Tuni dubban 'yan kasar da ma kasashen waje suka fice daga kasar ta gabashin Afirka.

Kazamin fadan wanda ya barke tun sama da mako biyu da ya gabata tuni daman ya riga ya haifar da kwararar dubban ‘yan kasar ta Sudan zuwa kasashe makwabta da suka hada da Masar da Chadi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Haka suma ‘yan kasashen waje gwamnatocin kasashensu da sauran hukumomi na ci gaba da kokarin kwashe su daga kasar, inda tuni suma dubbai suka fice .

A wani taron manema labarai kakakin ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka Vedant Patel, ya ce Amurkawa sama da 700 da ‘yan wasu kasashen aka kwashe ta tashar jirgin ruwa da ke garin Port Sudan a cikin kwana ukun da suka gabata, inda yawan Amurkawan da ake fitarwa daga kasar ya karu tun lokacin da aka fara rikicin.

Ya ce; ''A kokarin hadaka na kasashe, gwamnatin Amurka da hadin gwiwar kawayenta da abokan hadin gwiwa ta fitar da ‘yan Amurka sama da 1,000 daga Sudan tun lokacin da aka fara tashin hankalin.''

Sai dai wasu Amurkawa ‘yan asalin kasar ta Sudan a tashar jirgin ruwa ta Port Sudan da ke jiran a kwashe su sun ce suna nan zaune zaman jiran da ba su san takamaimai halin da ake ciki ba game da shirin tserad da su.

Suna kokawa da rashin samun wasu cikakkun bayanai daga hukumomi, inda har ta kai suna sayen abinci da ruwan sha da kudadensu a cewarsu.

Wani daga cikinsu ya ce kusan sa’a biyar suna zaman jiran tsammani babu wani bayani illa dai tun da farko an ce musu su yi hakuri.

Mohamed Madany ya ce shi bai ma sani ba ta jirgin ruwa za a kwashe su ko ta jirgin sama bai shi da masaniyar lokacin da zai bar wannan wuri.

Ya ce kusan kwana biyu bai ko runtsa ba, halin da suke ciki na da tsanani amma duk da haka sun jure.

Rikicin da ya shiga mako na uku, a tsakanin rundunar sojin kasar bisa jagorancin shugaban mulkin soja Janar Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun kar-ta-kwana na Rapid Support Forces, ko RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, na ci gaba da tsananta a sassan kasar daban-daban.

A babban birnin kasar Khartoum ya fi tsanani a wurin babban filin jirgin sama na kasar da fadar shugaban kasa da kuma hedikwatar sojoji.

Fadan da ya barke ranar 15 ga watan Afirilu da ya kare zuwa yanzu a kiyasin hukumomi ya hallaka mutane sama da 600, da jikkata sama da dubu biyar.