BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Roberto Firmino ya koma Al-Ahli ta Saudiyya

Roberto Firminho Roberto Firminho

Roberto Firmino ya kammala komawa Al-Ahli ta Saudiyya bayan barin Liverpool.

Ɗan wasan Brazil ɗin mai shekara 31, kwantaraginsa ta ƙare da Liverpool a ƙarshen kakar da ta gabata.

Ya kuma sanya hannu kan kwantaragin shekara uku da Al- Ahli.

Firmino ya ci kwallo 111 a wasa 362 da ya bugawa Liverpool tun bayan komawarsa ƙungiyar a 2015 daga Hoffenheim.

Yana ɗaya daga cikin manyan 'yan wasa da ƙungiyoyin Saudiyya suka ɗauka a bana, tare da mai tsaron ragar Chelsea ɗan Senegal Edourd Mendy da ya koma Al-Ahli a makon jiya.

N'Golo Kante da Kalidou Koulibaly sun bar Chelsea suka koma Saudiyya, Karim Benzema da Ruben Neves da kuma Marcelo Brozovic.

Shi ma tsohon ɗan wasan Liverpool Steven Gerrad ya koma Al-Ittifaq a matsayin mai horaswa.

Firmino da Naby Keita da Alex Oxlade-Chamberlain da James Milner duk sun bar Liverpool a wannan shekarar bayan ƙarewar kwantaraginsu.

Zaman Firmino da Mohamed Salah da Sadio Mane a matsayin 'yan gaba uku, ya taimaka wa Liverpool ta lashe Champions a 2019, da Premeir a 2020 sai FA a 2022.