Erik ten Hag ya ce Cristiano Ronaldo zai girbi abin da ya shuka, bayan da ya tabbar dan kwallon bai yadda ya shiga ya yi canji ba a wasa da Tottenham. Manchester United ta doke Tottenham 2-0 a gasar Premier League karawar mako na 12 ranar Laraba. Ronaldo, mai shekara 37 ya bar Old Trafford tun kan tashi daga karawar, wanda ya tashi daga bencin da yake zaune a minti na 89 ya fice daga filin. An cire sunansa daga 'yan wasan United da za su kara da Chelsea a Stamford Bridge ranar Asabar a babbar gasar tamaula ta Ingila, kuma shi kadai yake yin atisaye. An tambayi Ten Hag ko Ronaldo ya ki yadda ya canji dan wasa - sai Ten Hag ya ce ''gaskiya ne.''