BBC Hausa of Wednesday, 26 October 2022

Source: BBC

Ronaldo zai koma buga gasar Amurka, Messi zai kara kaka daya a PSG 

Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na son tsawaita kwantiragin Lionel Messi zuwa kaka daya. Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 35 za ta kare a karshen Yunin 2023. (Le Parisien - in French, subscription required)  Bayern Munich na tsara yadda za ta dauki dan wasan Manchester City, mai shekara 32,  Ilkay Gundogan a kakar badi. (90min)  Barcelona na tattaunawa kan yadda za ta sayi dan wasan Portugal, Ruben Neves, mai shekara 25 daga Wolves, wadda ke fatan kammala cinikin a Janairun 2023.  Kociyan Sporting Lisbon, Ruben Amorim ya ce mafarkin kowa a kungiyar shi ne Cristiano Ronaldo ya sake koma mata taka leda, to sai dai ya ce ba su da kudin da za su iya biyan albashin dan kwallon. (Football.London)  Ronaldo yana da zabin barin United ya koma taka leda a gasar kwallon kafa ta Amurka ta Major League Soccer, watakila a Inter Miami ko LA Galaxy ko kuma LAFC. (Los Angeles Times)  Arsenal za ta iya musaya da Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, domin a sayar mata da mai taka leda a Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27. (Calciomercato - in Italian)   A shirye Chelsea take ta fara batun tsawaita zaman Mateo Kovacic, mai shekara 28, bayan gasar kofin duniya. Yarjejeniyarsa za ta kare kasa da kaka biyu a kungiyar Stamford Bridge.  Watakila dan wasan Ingila, Jude Bellingham, mai shekara 19, ya yanke shawarar ci gaba da taka keda a Borussia Dortmund a badi, duk da cewar Liverpool da Real Madrid na son daukar dan kwallon. (Sky Sports, via Express)  Dan wasan Lille, mai shekara 22, Jonathan David, 22, ya ce dama na nan tafe nan gaba da zai buga tamaula a babbar kungiya. Ana ta alakanta dan kwallon Canada da cewar watakila zai koma Chelsea ko Arsenal ko kuma Manchester United. (Mirror)  Manchester United na jinjina da yadda daraktan wasanninta ke gudanar da aikinsa, wato John Murtough, bayan da ake jita-jitar za a maye gurbinsa a Old Trafford da tsohon daraktan wasannin Liverpool, Michael Edwards. (Express)  Leicester City da kuma Southampton na sha’awar daukar dan kwallon tawagar Morocco, Zakaria Aboukhlal daga Toulouse. (Football Insider)  Ana sa ran Newcastle United za ta sayi dan kwallon Leicester, James Maddison da na Bayer Leverkusen, Moussa Diaby da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai a watan Janairu. (Chronicle Live)  Sabon kociyan Middlesbrough, Michael Carrick ya ce zai yi anfani da alakarsa da tsohuwar kungiyarsa Manchester United, domin yake daukar aron ‘yan wasa. (TalkSPORT)