Shin ya za ki ji idan masu haɗa bidiyon ƙarya suka sanya fuskarki a bidiyon batsa sannan suka yaɗa shi a shafukan sada zumunta ba da sanin ki ba? Wata mata ta bayyana tashin hankalin da ta shiga bayan da irin haka ta faru da ita. Tana cikin duba shafinta na Tuwita wata rana da yamma, Kate Isaacs ta ci karo da wani bidiyo mai tayar da hankali. "Gaba ɗaya hankalina ya tashi," in ji Kate, lokacin da ta yi bayani a karon farko game da abin da ya faru. "Wani ya ɗauki fuskata ya shigar da ita cikin bidiyon batsa, sai ya zama kamar da gaske ni ce a ciki." An yi amfani da fuskarta ne a bidiyon bogi wanda yake kama da na gaske. Inda wani ya maye gurbin fuskar wata ƴar fim ɗin batsa da ke cikin bidiyon, da fuskar Kate. Kate wata mai fafutika ce da ke hanƙoron ganin an daina saduwa da mutum ba tare da izinin sa ba. An ɗauko fuskar ta ne daga bidiyon tattaunawar da ta yi da ƴan jarida a game da hanƙoron da take yi. Inda a cikin bidiyon aka nuno ta tana jima'i. "Na shiga ruɗani. Na rasa me zan yi," in ji Kate. "Na yi tunanin cewa bidiyon zai karaɗe duniya - wannan babban tashin hankali ne." A lokutan baya, an fi yin amfani da fuskokin manyan taurarin fina-finai da na ƴan siyasa wurin yin bidiyon bogi - ba domin bidiyon batsa kawai ba, wasu akan yi na ban-dariya. To amma kamfanin lura da tsaron shafukan intanet na Deeptrace ya ce an samu sauyi a baya-bayan nan, inda yanzu aka samu kashi 96% na irin waɗannan bidiyoyi ana yin su ne kan batsa. Kamar yadda yake faruwa a zahiri, ana bayyana irin wannan lamari da ɓata sunan mutane ta hanyar lalata/cin zarafi, wanda yake nufin haɗawa da yaɗa hotunan baɗala na mutane ba da sanin su ba. A ƙasar Scotland, laifi ne yaɗa bidiyon tsiraicin mutane ba tare da izininsu ba. Amma a sauran yankunan Birtaniya hakan zai zama laifi ne kawai idan aka iya tabbatar da cewa wanda ya yaɗa bidiyon ya yi ne da niyyar cutar da wani - wani abu da ya sanya ake gaza hukunta da dama daga cikin masu haɗa irin wadannan hotuna. Kate, mai shekara 30 ita ce ta samar da ƙungiyar masu fafutika da aka yi wa laƙabi da #NotYourPorn a shekarar 2019. Shekara ɗaya bayan ƙaddamar da fafutikar aka tilasta wa shahararren shafin batsa na Pornhub ya cire duk wasu bidiyoyin batsa da aka ɗora a shafin daga mutanen da ba a tantance su ba. Wanda hakan ya shafi mafi yawa daga cikin bidiyoyin shafin. Saboda haka Kate na da yaƙinin cewa wanda ya sanya fuskarta a wannan bidiyon na batsa da aka haɗa yana daga cikin waɗanda fafutikar da take yi ta shafa. Domin "ita ce ta sauke masu bidiyonsu." To amma ko kaɗan ba ta da masaniyar ko wane ne ya haɗa bidiyon ba, ko kuma iyakar waɗanda suka kalli bidiyon ba. Yayin da ita ta tabbatar da cewa fuskarta ce aka ɗora a kan wata ƴar fim din batsa, to amma bidiyon ya yi tamkar na gaskiya, ta yadda ba kowa ne zai iya gane cewa haɗa shi aka yi ba. "Wannan laifi ne - an yi amfani da fuskata ba tare da sanina ba." A ƙarƙashin bidiyon sai mutane suka rinƙa yin tsokaci na ɓatanci , suna cewa za su bi Kate har gida su yi mata fyaɗe, su naɗa a bidiyo sannan su yaɗa a shafukan intanet. "A wannan lokacin dole ka fara tunanin iyalanka," ta faɗa cikin hawaye. "Ya za su ji idan suka ga bidiyon." "Na fara munanan tunani - su wane ne suka san gidana? Shin ko wanda na sani ne ya yi min haka?" "Na yi ta tunanin cewa ina cikin babbar matsala. Wannan ba kawai wasu mutane ne suke soki-burutsu ba, wannan babbar barazana ce." Kasancewar ta da dade a cikin harkar saboda ta sha taimaka wa wadanda suka shiga cikin irin wannan hali, za a iya cewa ta san abin da ya kamata ta yi - to amma a wannan lokaci ta rasa me za ta yi. Ta ce "Na kasa amfani da duk shawarwarin da nake ba wasu ba. Kate wadda ke da karfin hali, sai ga shi na shiga cikin razani." Wani abokin aikina ne ya kai wa Tuwita kara game da bidiyon, daga nan tuwita ta cire shi. To amma da zarar aka ce an wallafa wani abu a shafin intanet, yana da matukar wahala a iya cire shi gaba daya. Kate ta ce "babban burina a lokacin shi ne a cire bidiyon daga intanet baki daya, to amma babu abin da zan iya yi a kan hakan." Abin da za ku yi idan aka yi amfani da fuskarku a bidiyon bogi -A samu shaida - Duk da cewa abu ne mai wahala, saboda za ka so a ce an goge komai, to amma yana da kyau ka mallaki bidiyon ko kuma ka ɗauki hotunan, da lokutan da aka sanya su, da waɗanda suka sanya, da adirenshisu na intanet, ka ajiye su a wani wurin da ba za su ɓace ba. -A kai rahoton waɗanda suka wallafa - Da zarar ka sauke shaidar da ka samu sai ka kai rahoton duk wanda ya wallafa abin zuwa ga shafukan da suka ɗora. -A tuntuɓi ƴan sanda - Yana da kyau ka je ka yi bayanin abin da ya faru ga hukuma, kuma a nuna masu shaidun da ake da su. A kira lambar agajin gaggawa ta 101. -A nemi shawarwari - Za a iya samun shawarwari kan bidiyoyin batsa a kan waɗannan lambobi 1000 - 1600 cikin ranakun mako ko kuma 0345 6000 459 a ƙarshen mako. (A Birtaniya) Majiya: #NotYourPorn Campaign Kafin wannan lokaci ba kowa ne yake iya samun manhajojin haɗa bidiyoyin bogi masu kama da na asali ba, sannan ba kowa ne zai iya amfani da su ba, koda ya samu. To amma yanzu bisa ka'ida ta doka duk wani mutum da ya kai shekara 12 zai iya sauke manhajojin ya kuma haɗa bidiyoyin bogi cikin sauƙi. Kate ta ce wannan abu ne mai ban tsoro. Ta ce "abu ne da yake a fili, bai da wahalar samu." Ta ce a yanzu dokokin da aka ƙirƙiro a baya kan irin waɗannan bidiyoyi sun tsufa. Sanya fuskar Kate a bidiyon bogi ya yi illa ga lafiyarta da kuma yadda take amincewa da mutane. Ta yi amannar cewa waɗanda suka haɗa bidiyon ba sun yi ne kawai domin su tsorata ta ba, sun yi ne domin ganin sun rufe mata baki. Da farko ta ja baya wurin aikin nata na fafutika, tana ganin cewa kamar ba ta cancanci ta ci gaba ba. To amma yanzu ta dawo da ƙarfinta. Ta ce "ba zan bari su yi nasara ba." Ta ce za a iya amfani da bidiyon bogi wajen sarrafa mata, saboda haka ya kamata a ƙarfafa wa kamfanonin fasahar zamani - ciki har da waɗanda ke haɗa manhajojin da ake amfani da su wurin sauya fuska, su samar da samar da tsari mai kyau. "Ya kamata a ce kowace manhaja za ta iya gane bidiyon batsa." "Idan kamfanoni suka ƙi zuba kuɗi, da basirarsu wajen ganin ba a yi amfani da manhajarsu wajen ƙirƙirar bidiyon batsa ba, to suna bayar da gudumawa ke nan, kuma su ma suna da laifi."