BBC Hausa of Saturday, 29 July 2023

Source: BBC

Sadio Mane zai koma Saudi Arabia

Sadio Mane Sadio Mane

Bayern Munich ta sanar cewar Sadio Mane na tattaunawa da wata kungiyar, domin komawa buga gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Dan kwallon tawagar Senegal, mai shekara 31, ya samu tayi daga Al-Nassr, mai buga babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Mane ya bi Bayern Munich wasannin atisayen tunkarar kakar bana, amma kungiyar ba ta saka shi a wasan sada zumunta da Kawasaki Frontale da ta yi a Tokyo ba.

Mane ya koma Bayern a bara kan yarjejeniyar kaka uku daga Liverpool kan fam miyan 35.

Ya ci kwallo 12 a karawa 38 da ya buga wa Bayern Munich, wadda ta lashe kofin Bundesliga na 11 a jere a kakar da ta wuce.

Sai dai ya rasa gurbinsa, bayan rahoton da ya ce ya naushi Leroy Sane, bayan tashi daga Champions League da Manchester City ta yi nasara.

Lamarin ya faru a cikin watan Afirilu, inda aka ci tarar Mane, sannan aka daina saka shi a wasanni.

A cikin watan Disamba, Al-Nassr ta dauki Cristiano Ronaldo daga baya ta sayo Marcelo Brozovic da Alex Telles da kuma Seko Fofana.