Hausawa kan ce Salla mai yawan baya!
Ga dukkan alamu, wannan zance ya fi zama gaskiya, ga shugaban da ya yi Idinsa na ƙarshe a kan karagar mulkin Najeriya.
Bikin Ƙaramar Salla da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a Abuja, zai kasance ɗaya daga cikin muhimman lokuta a tarihin rayuwarsa.
Ya zo ne a lokacin da shugaban na Najeriya ke tattara nasa-i-nasa daga fadar mulki ta Dutsen Aso, kafin ya miƙa harkokin shugabanci ga magajinsa nan da mako biyar.
Yana dai fatan komawa can nesa da Abuja, mai cike da ƙalubale da matsalolin mulkin ‘yan Najeriya kimanin miliyan 200 zuwa cikin iyali a gidansa na Daura, wani wuri da shi ma yake da tarihi, idan ana maganar bukukuwan sallar idi guda 17 da Buhari ya gani a zamanin mulkinsa na tsawon shekara takwas.
Jawabin bikin sallar idin Buhari na ƙarshe dai, ya saɓa da na sallar idinsa na farko.
A idin farko, jawabin cike yake da alƙawurran shugabancin da zai gyara kura-kuran masu mulki na baya. Neman ci gaba da goyon baya da nuna fahimta da kuma haƙuri daga 'yan ƙasa.
Akwai ƙudurin fifita aiki mai nagarta kuma cikin tsanaki, maimakon tafiyar sauri da wasu suka fara ƙosawa suka ga an yi. Sai kuma alƙawarin karya lagon taɓarɓarewar tsaro da cin hanci da kuma ƙarancin ayyukan raya ƙasa.
Sallar Idin Buhari ta watan Yulin 2015, ta zo ne mako biyu bayan wani mummunan harin ƙunar bakin wake da Boko Haram ta kai Zabarmari, da ke kusa da Maiduguri.
Inda aka kashe mutane da yawa ciki har da soja ɗaya a harin, wanda mayakan Boko Haram suka riƙa buɗe wuta, wasu ‘yan mata guda shida kuma suka tayar da bama-baman da suka yi jigida da su.
A cikinsu wata ta yi yunƙurin kutsawa wani masallaci, ana sallar tarawi.
Lamarin ya zo ne kwana biyu, bayan wasu hare-haren Boko Haram a kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Kukawa da suka yi sanadin kashe masallata kusan 100.
A Idinsa na ƙarshe a kan mulki kuwa, jawabin Buhari da ya fi jan hankali shi ne wanda ya yi wa rukunin wasu shugabannin al'ummomin Abuja, lokacin da suka kai masa ziyarar barka da salla.
Jawabi ne da cike da tsokacin rayuwarsa kafin da kuma bayan mulki.
Ya dai nanata bayanin da ya sha yi cewa zai tafi nesa da Abuja, kuma ya nemi afuwa daga waɗanda ya ɓatawa a tsawon shekara takwas.
Duk da yake, a wannan bikin idin Ƙaramar Sallah na 2023, kamar na 2015, Najeriya tana fama da matsalolin tsaro, amma muhimmin bambanci shi ne ana ƙara mantawa da ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-baya da ta yi ƙaurin suna a duniya, wato Boko Haram.
A wannan karo dai ko ba komai, dogayen layukan masu ibada da suka riƙa fuskantar binciken jami’an tsaro kafin shiga masallatan Juma'a da na idi, sun daɗe da ɓacewa.
Sallar Idin ta watan Yulin 2015, ta zo ne mako biyu bayan wani mummunan harin ƙunar bakin wake da Boko Haram ta kai Zabarmari, da ke kusa da Maiduguri.
Inda aka kashe mutane da yawa ciki har da soja ɗaya a harin, wanda mayakan Boko Haram suka riƙa buɗe wuta, wasu ‘yan mata guda shida kuma suka tayar da bama-baman da suka yi jigida da su.
A cikinsu wata ta yi yunƙurin kutsawa wani masallaci, ana sallar tarawi.
Lamarin ya zo ne kwana biyu, bayan wasu hare-haren Boko Haram a kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Kukawa da suka yi sanadin kashe masallata kusan 100.
A Idinsa na ƙarshe a kan mulki kuwa, jawabin Buhari da ya fi jan hankali shi ne wanda ya yi wa rukunin wasu shugabannin al'ummomin Abuja, lokacin da suka kai masa ziyarar barka da salla.
Jawabi ne da cike da tsokacin rayuwarsa kafin da kuma bayan mulki.
Ya dai nanata bayanin da ya sha yi cewa zai tafi nesa da Abuja.
Kuma ya nemi afuwa daga waɗanda ya ɓatawa a tsawon shekara takwas.
Duk da yake, a wannan bikin idin Ƙaramar Sallah na 2023, kamar na 2015, Najeriya tana fama da matsalolin tsaro, amma muhimmin bambanci shi ne ana ƙara mantawa da ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-baya da ta yi ƙaurin suna a duniya, wato Boko Haram.
A wannan karo dai ko ba komai, dogayen layukan masu ibada da suka riƙa fuskantar binciken jami’an tsaro kafin shiga masallatan Juma'a da na idi, sun daɗe da ɓacewa.
Juma'a ga alama, muhimmiyar rana ce a tarihin mulkin shugaban mai barin gado.
Muhammadu Buhari ya fara Sallar Idinsa ta farko a kan mulki, ranar Juma’a 17 ga watan Yulin 2015 a filin Idi na Abuja, ƙasa da wata biyu bayan rantsar da shi.
Kuma ya kammala Sallar Idinsa ta 17 karon ƙarshe a kan mulki a Barikin Mambila cikin Abuja ranar Juma’a 21 ga watan Afrilun 2023.
Bikin Sallar Idi, kamar wannan na Ƙaramar Sallah da muke ciki, ga ma’aikata da manyan jami’an gwamnati, lokaci ne na samun sararawa daga ayyukan ofis.
Shugaba Muhammadu Buhari ya riƙa amfani da lokacin wajen sada zumunci tsakanin iyalai da dangi.
Ya ƙara buɗe ƙofar karɓar masu ziyara da ke zuwa gaisuwa da fatan alheri da kuma taya shi murnar an yi salla lafiya.
A duk lokutan bukukuwan Sallar Idi, akan ga manyan jami’an gwamnati ciki har da mataimakinsa Yemi Osinbajo da ministoci da gwamnoni da 'yan majalisa da ƙusoshin jam’iyya mai mulki da sarakuna da shugabannin al’umma da na addinai suna tururuwar zuwa gaisuwa a fadar Aso ko kuma a Masarautar Daura.
A irin wannan lokaci akan ga hotunan shugaban cikin 'ya'ya da jikoki da sauran makusanta da kan je gaisuwar salla.
An lura cewa akasari Shugaba Buhari ya fi yin shagulgulan Ƙaramar Salla a Abuja, a lokacin bikin Babbar Salla kuma yakan je mahaifarsa ne wato Daura.
Yakan halarci masallaci, sannan bayan an sauko daga idi ya saba yin tattaki a tsakiyar al'ummar da kan yi dandazo suna kai gaisuwa da kuma kai caffa.
Sai dai a shekara ta 2020, Buhari yanka ragon sallarsa ne a Abuja, saboda bai je Daura ba, dalilin cutar korona.
Alba
ƙar Buhari da Sarakuna>Sallar Idi dai, bikin shekara-shekara ne da kan zo da batun komawa ga al'ada da kuma gargajiyar al'ummar Hausawa.
Ba abin mamaki ba ne ganin babbar alaƙar da shugaban ya gina tsakaninsa da sarakuna a faɗin Najeriya, kasancewarsa mutumin Daura. Mashahuriyar Masarauta mai daɗaɗɗen tarihi a cikin Hausa bakwai.
Muhammadu Buhari ya sha nanata muhimmiyar gudunmawar da sarakuna ke iya bai wa shugabannin ƙasa kamar sa wajen inganta ayyukan tattara bayanan sirri a yankuna da masarautunsu don magance babbar matsalar da ta addabi Najeriya a zamanin mulkinsa, wato ƙalubalen tsaro.
Kyautar sarauta da aka gani an bai wa Shugaba Buhari ta ƙarshe a bainar jama'a, ita ce wadda Sarki Aminu Ado Bayero ya miƙa masa a watan Janairun 2023, wani zungureren ƙaho.
Rahotanni dai sun ce ƙahon wani maƙunshin kyauta ne na karramawa kuma yana ƙunshe ne da wata babbar rigar sarakuna.
Sarakuna sun sha karɓar sa a ziyarar da yake kai wa fadarsu zamanin mulkinsa, ga alama shi ma ya buɗe ƙofar fadarsa ga masu sarautar da suka sha zuwa ziyara daga faɗin Najeriya.
Mai yiwuwa wannan ba abin mamaki ba ne, ga mutumin da ke riƙe da sarautar 'Bayajiddan Daura'.
A bikin Babbar Salla cikin 2021, Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk ya sake gwangwaje Buharin da iyalinsa, da wata sabuwar sarauta, ta hanyar naɗa babban ɗansa namiji, Yusuf Buhari, matsayin Talban Daura, kuma Hakimin Ƙwasarawa.
Ban da aminta, Shugaba Buhari ya haɗa surukunta da sarakuna kamar na Kano.
A cikin watan Agustan 2021 ne, aka yi ƙasaitaccen bikin da a nan kusa ba a ga irinsa ba a sabuwar Masarautar Bichi, kai har ma da mahaifiyarta Masarautar Kano.
Lokacin da aka ɗaura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero, ɗiyar Sarkin Bichi, Mai martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Yayin bikin, garin Bichi da ke wajen birnin Kano, ya shaida manyan baƙi da suka hadar da jami'an gwamnati da sarakuna da ɗumbin mutane masu fatan alheri.
Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ya ga saukar jiragen sama masu tarin yawa.
Babu daɗewa kuma a cikin wannan shekara, Sarkin Daura ya ɗaga darajar ƙauyen Dumurkol, mahaifar Buhari zuwa garin Hakimi.
Shekara ɗaya kafin nan cikin watan Disamban 2020 a lokacin wata ziyarar hutu ta tsawon mako ɗaya a Masarautar Daura, Buhari ya samu ƙasaitacciyar tarba da wata kyautar sarakuna ta kilin doki, taka-haye da takobin yaƙi.
An shiga yanayin damuwa
Cikin ƙalubalen da alaƙar Shugaba Buhari da sarakuna ta fuskanta har da ka-ce-na-cen da aka fuskanta a lokacin da gwamnatin jihar ta tuɓe sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sanusi na II.
Sai da ta kai ga fadar Shugaba Buhari fitar da sanarwa tana musanta duk wani hannu a dambarwar tuɓe Muhammadu Sanusi daga sarautar Kano.
A tsawon mulkinsa na shekara takwas, Shugaba Buhari ya sha ganawa da shugabancin Majalisar Sarakuna ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da Ooni na Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Majalisar dai ta shafe tsawon lokaci tana gwagwarmayar ganin tsarin mulkin Najeriya ya martaba sarakuna tare da ba su ikon da ya kamaci matsayinsu a ƙasar.
Sai dai, fafutukar Majalisar Sarakunan ta ganin an mayar wa masu sarauta ikonsu cikin tsarin mulkin Najeriya, a tsawon shekara takwas na mulkin Buhari, a iya cewa, haƙa ba ta cimma wani ruwa ba.