Sabuwar shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan na kokarin neman goyon baya - na dinke barakar da ke tsakaninsu da makwabciyarta kasar Kenya, wacce ta yi tsami a lokacin mulkin shugaban kasar da ya gabace ta.
John Magufuli, wanda ya mutu a watan Maris, sananne ne wajen yin wasu-wasi game da cutar korona, kuma matsayin marigayi shugaban kasar mai cike da ce-ce-ku-ce ya sa kasar Kenya ta dauki matakin rufe kan wuraren ketarawa da ke kan hanyar iyakarsu mai nisan kilomita 750.
Amma kuma, a yayin wata ziyararta ta kwanaki biyu a Kenya, Shugaba Samia ta kauce wa al'adarta a kasar Tanzania inda ta saka takunkumin fuska a duk tsawon lokacin da ta kwashe a kasar.
A lokacin jawabanta, wasu a cikin harshen Swahili da duka kasashen biyu ke amfani da shi, ta burge manyan 'yan kasuwa da 'yan majalisar dokoki da wasu labarai da kalamai na barkwanci.
Ga biyar daga cikin fitattun kalaman nata:
Awaki da takunkuman fuska
Shugabar kasar mai shekar 61, ta yi amanna cewa ziyarar tana zuwa ne a '' wani lokaci mai tsanani...da muke fuskantar annobar korona a fadin duniya'':
"Ga mu a nan kowa sanye da takunkumi a fuskokinmu - a duk lokacin da na ga mutane sanye da takunkumin a fuskokinsu, yana tuna min da cewa a kauyenmu idan muka tafi kiwon dabbobi da awaki, muna rufe musu bakunansu da takunkumi don kada su ci amfanin gona a kan hanyar su... don haka muna rufe musu baki kamar yadda muke yi a yanzu .... dole mu yi hakan."
Dabbobin "wildebeest" sun hada kawunanmu
Cike da zumudin jaddada muhimmancin huddar cinikayya tsakanin kasashen Gabashin Afirka makwabta, da ke samar da fiye da dala miliyan 450 ( $450m), ta yi misali da dabbobin ' wildebeest' (dangin bauna) da ke ketarawa daga gandun dajin Mara na kabilar Maasai a kasar Kenya zuwa gandun dajin Serengeti a Tanzania wajen fitar da ma'anarta.
"Allah ya albarkaci wadannan kasashe biyu da suka zama makwabta. Muna da kan iyakokin kasa da na ruwa. Kuma yanayinmu daya ne. Ko dabbobinmu ma makwata da dangin juna ne.
"Akwai wadannan nau'in dabbobi na wildebeests, da ku zuwa sau dauki ciki a kasar Kenya kana su je su haihu a Tanzania… Yanzu, idan wadannan dabbobi suna da shaidar zama dan kasa, a wace kasa za su kasance?"
Kenya na fama da harshen Swahili
'Yan kasar Tanzania, musamman wadanda suka fito daga kasar Zanzibar kamar Shugaba Samia, kan yi magana kan abin da aka dauka a matsayin ''tsaftataccen harshen'' Swahili. Ta wani gefen kuma, harshen Swahili na kasar Kenya a gurbace yake - da wasu ke tunanin na rashin wayewa ne, kuma ya kan zama abin zolaya a tsakanin makwabtan:
"Muna farin ciki da shawarar da kuka yanke na fara amfani da harshen Swahili a zauren majalisar dokoki. Abin da ya sa nake sauraron abinda ke faruwa a zauren majalisar dokokin kasar kenan - Ina kaunar naku harshen Swahilin. Na ku Swahilin da da abubuwan barkwanci sosai. Wadannan kadai sun isa su nishadantar da mutum.
"Ina cikin saurare yayin da kakakin majalisar dokokin kokarin fadin sunan lambobin shekaru a cikin harshen Swahili."
Arashin hade sunayen shugabannin kasa
Ta yi barkwanci da sunanta da na takwaranta na kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, wajen yin kira da su bunkasa huddar cinikayya:
"Kun yi sa'a cewa tsakanin kasashenmu biyu, daya gefen kuna da 'Uhuru' ('Yancin Swahili) wajen yin kasuwanci, ta daya gefen kuma akwai 'Suluhu' (warware matsalar Swahili) don cire takunkumin kasuwanci. Aiki ya rage a gare ku.''
Wuraren shakatawa a birnin Nairobi
Shugaba Samia ta yi misali da shakatawar dare da sauran al'amuran nisahantarwa da aka saba morewa a babban birnin kasar ta Kenya - amma kuma komai ya tsaya saboda dokar hana fitar dare sakamakon annobar cutar korona.:
"Na yi amanna cewa wani babban bangare na tawagar da na zo da ita sun san lunguna-lungunan birnin Nairobi. Sun san inda za su samu wurin da ake gasa balangu 'nyama choma' irin na kasar Kenya.
"Amma saboda korona, ba su samu damar more rayuwarsu ba. Na damu saboda me yiwuwa wasu daga cikin su an bar su a baya